Home APC A Yau Gwamnan dai-dai da zamani: Alhaji Ahmad Aliyu Gwamnan jihar Sakkwato

Gwamnan dai-dai da zamani: Alhaji Ahmad Aliyu Gwamnan jihar Sakkwato

by Bilkisu Yusuf Ali

Alhaji Ahmad Aliyu Gwamnan Jihar Sakkwato: Irin dan Siyasar da  kasar Nijeriya ke Fata

A kullum aka tashi batun siyasa ba abin da ke fitowa a bakin al’umma sai a ba wa matasa dama su ne za su iya,  kuma su ne ke da dabaru da wayewa da kwari da lafiya da ma juriyar daukar duk wani tudu da gangare da kura da zafi na shugabanci. Sannan uwa uba su ne suka san matsalar da al’umma ke ciki musamman ma matasa. Su ne ruhin kasa duk wani fandisho su za a yi wa. Ba a ce a kauce a ba wa matasa waje ba sai dai a ba su ragama sannan a koma gefe dattijan kirki suna kallonsu suna  kara sa su a hanya. Sokoto tana cikin jahohin da Allah ya tarfawa garinsu nono suka rabauta da samun haziki kuma jajirtaccen matashi  AlhajiAhmad Aliyu A Matsayin zababben Gwamnan JiharSakkwato Cikin jam’iyyar APC bisa daga hannu da addu’ar jagorancin uba kuma jigo a jam’yyar APC wato Sen Aliyu Magatakardar Wammako.

Tarihinsa

An haifi Alhaji Ahmad Aliyu a ranar 1 ga watan janairu a shekarar 1970 a unguwar Tudun wada da ke cikin garin Sokoto. Tun tasowarsa da karatun allo ya budi ido har sai da ya kai shekara bakwai da haihuwa sannan aka  saka shi a makarantar firamare. Ya fara  ashekarar 1977-1983 a Magajin rafi model primary School. Wanda a wannan shekarar shi ne dalibi ma fi kwazo  da tarbiyya da kuma tsafta inda ya samu kyaututtuka akan hakan. Ya yi makarantar Sakandire daga 1983-1989 a sakandare ta garin Yabo. Bayan ya kammala ya je ya yi wani tirenin a bangaren  Akanta(Clerical Officer Account and Audit) a 1991  a makarantar polytechnic ta jihar Sokoto. Ya kuma yin wani kwas din dai a wannan fagen na Akanta (Public Account) 1991-1992. Ya koma ya yi (Professional   diploma in Public Account and Audit DPAA) 1992-1994 A  makarantar polytechnic ta Abdu Gusau  da ke Talatar Mafara a shekarar 1995-1997 . Ya gabatar da babbar Diflomarsa a bangaren nazarin  kanananhukumomi (HNDLGS) Daga shekarar 2000-2002 sannan ya yi masters a bangaren kasuwanci daga 2002-2003. Alh Ahmad Aliyu tun tasowarsa ya san muhimmancin ilimi da nemansa don haka bai taba gajiya ko gazawa wajen nemansa ba. Wannan ta sa a shekarar 2004-2007 ya kuma yin wani masters din a a bangaren Business Administraation. Bai numfasa da neman ilimin ba daga nan ya kuma komawa aji inda ya yi  wani dai digirin na masters a makarantar NDA da ke Kaduna ya karanci huldar jakadanci tsakanin kasa da kasa (Internatonal relationship) a shekarar 2009-2010. A shekarar 2010-2011 ya halarci makarantar Akanta ta kasa don samun horo na musamman inda  akarshe ya sami shaida ta zama cikakken akanta na kasa.

Gwagwarmayar Rayuwa

Alhaji Ahmad Aliyu ya fara fadi-tashin aiki tun daga shekarar 1989 a karamar hukumar Jega. Tun daga nanbai huta ba sai ma kara daukar nauyi da ya yi ta yi na hidimtawa al’ummar Sokoto har ta kai da ya zama mataimakin gwamnan jihar Sokoto. Ahmad Ali  ya zama kwamishina a ma’aikatar social  welfare  and Culture  inda ya yi shekara hudu sannan bayan nasara a karo na biyu da Gwamna Alu Magatakardar Sakkwato ya yi sai Alh Ahmad Aliyu ya zama kwamishinan lafiya. Inda anan ya zauna shekara hudu. A shekarar 2014  jam’iyyar APC ta zabi Ahmad Aliyu ya zama mataimakin dan takarar gwamna na jihar Sakkwato.Bahaushe ya ce “Dan halas ke mayar da biki da mai zuciya” ko bayan da gwamnan jahar Sokoto santsi ya ja shi zuwa PDP  ya yi wa jagoransa butulci Alhaji Ahmad Aliyu bai matsa ko’ina ba yana nan yana ci gaba da biyayya da duban al’ummar jihar Sotoko ba bukatar kansa ta kawo shi wannan matsayin ba don haka ya zauna daram a APC abin sa. Wannan ta ba shi damar tsayawa a matsayin takarar gwamna karkashin gwamnatin APC bayan tankade da rairaya da jam’iyyar ta yi ta tabbatar in dai Sokoto a ke kishi da al’ummarta to Alhaji Ahmad Aliyu ne ya fi dacewa da zama Halifan Magatakarda a Sokoto don tabbatar da duk manufofi da akidunsa. Bayan kai ruwa rana da tafiya inconclusive a wannan karon jam’iyyar APC ba ta saminasara ba. Amma ranar 18/may/2020 Alh Ahmad  Aliyu Sakkwato ya zama Sakataren hukumar ‘Yan sanda ta kasa wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi. Ya rike wannan mukami har zuwa lokacin da ya kudiri niyyar fara takarar gwamnan jihar Sakkwato. A ranar 

Wasu Daga Ayyukansa a matsayin kwamishinan lafiya 

• Ya fadada asibitin kasha  na Wammako

• Ya fadada makarantar Ungozoma a Tambuwal

• Ya gyara makarantar Jinya ta Sakkwato

• Ya gyara makarantar kimiyya da lafiya ta Gwadabawa

• Ya  karasa asibitin Murtala Muhammad da ke Sakkwato sannnan ya bude shi.

• Ya gyara makarantar MaryamAbacha Women And Children Hosp Noma Hospital and WCWC 

• A lokacinsa dukkan asibitocin jihar Sakkwato manya Gen Hosp an fadada su an gyara su sun zama dai-dai da dukkan manyan asibitoci da ke kasar nan ta fuskar kayan aiki da ma’aikata. 

• An gyara dukkan kanann asibitoci da ake kira primary health care an wadata su da kayan aiki da kyakkyawan muhallin da ake bukatar asibiti ya kasance. Sannan an fadada su sun zama dai-dai da zamani.

• An raba kayan aiki da motocin daukar marassa lafiya dukkan gunduma da ke Sakkwato don ceto rayuwar al’umma da ingamta lafiya.

Gogewarsa a Siyasa

Bahaushe kan ce “barewa ba ta gudu danta ya yi rarrafe” Kowa ya kalli siyasa ta Sen Aliyu Magatakarda Wammako ya kalli Alhaji Ahmad Aliyuyasan ya sami tsatso na madarar siyasa gangariya ta tamakon talaka da kishinsa wannan ya sa tun daga lokacin da aka ambata Alhaji Ahmad Aliyu a matsayin dan takarar gwamna karo na biyu a kakar zabe ta 2023 Sakkwatawa da masu kishin Sakkwato ba abin da suke furtawa sai an ajiye kwarya a gurbinta Adduar Sakkwatawa ta yi tasiri sun san sun sami jagora adali , matashi, marar girman kai , mai tausayi mai son ci gaban matasa wanda neman ilmi ke gabansa wanda zai kare musu mutuncinsu da al’adunsu  da sarakunansu. Sun sami gwamna da zai ji matsalar al’ummarsa na shi ne. Dansu ne da ya tashi cikinsu bai taba guduwa ya bar su ba. A ranar 30 ga watan Maris 2023 hukumar zabe ta kasa ta dankawa Alhaji Ahmad Aliyu takardar shaidar zama wanda ya lashe zaben 2023 amatsayin  gwamnan Sakkwato.

Lokacin Cika Alkawari ya yi.

Mai kamar zuwa ake aike. Mutanen Sokoto bukatarku  ta biya. Daga cikin alkawuran da gwamnan Sakkwato ya dauki alkawari akansa sun hada da:

• Tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankali za su tabbata in sha Allahu don duk hanyar da za ta kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a Sokoto ya gama shirya ta aiwatarwa kawai ake jira.

• Samun kayan noma da ma dabarun noman zamani kamar yadda yake a kasashen da suka ci gaba.

• Batun koyarwa da dabarun koyarwa da kayan koyarwar da diban malamai aiki don koyarwa da samar da yanayin koyarwa wato kyakkyawan muhalli makarantu da gine-gine na zamani da yardar Allah za su tabbata a jihar Sakkwato.

• Samar da walwalar ma’aikata a duk fadin jahar Sokoto zai tabbata da yardar Allah.

• Lafiya uwar jiki. Alhaji Ahmad Aliyu ya yi alkawarin bunkasa kiwon lafiya da samar da duk abin da ake buqata a kananan hukumomi 23 da jihar ke da su.

• Ruwa abokin aiki. Batun matsalar ruwa a jihar Sokoto ta zama tarihi da yardar Allah don duk hanyoyin da za a bi da kuma yadda za a yi tuni An kammala tanadinsu a cikin birane da karkara.

• Batun ilimi na ckin muhimmin  abin da ya ke ci wa Alhaji Ahmad Aliyu tuwo a kwarya musamman na matasa ‘ya’yan talakawa da suke da cancanta su fita kasashen waje don samun damar karo ilimi. Gwamna mai jiran gado ya yi alqawarin kai matasa ‘yan asalin jihar Sokoto kasahen waje don karo karatu a bangarori da daman gaske. Burisa a fannin ilimi nan da 2023 da yardar Allah sai jahar Sokoto ta zama ta farko wajen samar da matasa da za a yi alfahari da su a Najeriya.

• Zai zo da dabaru da hanyoyi na kasuwancin zamani da inganta tsofaffin hanyoyin da suke da su na kasuwancin da bunkasa tattalin arzikin Sokoto.

• Duk kasar da ta zama abar alfahari har ake marmarin zuwa ko dai don ziyara ko wani aiki na musamman ko yawon bude ido to tsari ta samu ingantacce musamman na muhalli.  Wannan ya saAlhaji Ahmad Aliyu ya yi alkawarin mayar da jahar Sokoto sabuwa.

• Rashin ayyukan yi yana cikin abin da ke ci wa Gwamna mai jiran gado tuwo  a kwarya don haka ya tsaya kai da fata sai an samar da ayyukan yi a tsakanin matasa da ma al’ummar jahar Sokoto damarsu da suke da ita ta guraben aiki a gwamnatin tarayya za su dawo da ita.

• Alhaji Ahmad Aliyu ya daura damarar yaki da fatara da ta’addanci da shaye-shaye tsakanin matasa da banga da cin hanci da rashawa da danne hakki da yaudara da ci da gumin talaka da sauran abubuwa da a yau suke bata tarbiyyar zahiri da ta badini.

• Dillalin wada an ce shi ya san kudin jariri. Alhaji Ahmad Aliyu ya tashi gidan ilimi na addini don haka ya yi alkawarin taimakawa makarantun allo da malamansu don su ma su sami ribar siyasa. 

• Mata iyayen giji. Alhaji Ahmad Aliyu yana da kyakyawan shiri da zai yi wa mata don inganta rayuwarsu Za a ba su horo na sana’oi daban-daban sannan kuma za a ba su wadataccen jarin da zai isa a juya su rike iyalansu a ciki

Allah ya taya riko, Allah ya sa al’ummar Sakkwato su ce gara  da  aka yi. Amin.

Related Posts

Leave a Comment