MALAMAI MAGADA ANNABAWA TARE DA
BILKISU YUSUF ALI
Marigayi Sheikh Isa Waziri (Wazirin Kano)
Malam Isa Waziri dattijo ne mai halin dattaku, Mutum ne wanda ya sadaukar da dukkan rayuwarsa wajen koyarwa da ilimantar da al’umma. Malam Isa Waziri mutum neda ba ya son raini da rashin tarbiyya bai yarda da sauyin zamani da yakerudar matasa ba don haka kullum aka ji yo shi yana tsawatarwada nasiha da fada yayin da duk ya ga wani abu na rashintarbiyya ko sabawa al’ada.
Tarihinsa
Sunan Mahaifin sheik Isa Waziri Muhammadu Gidadomahaifiyarsa kuwa Malama Aisha wadda aka fi sani da Mumina.An haifi sheikh Waziri a shekarar 1925 unguwar Tudun wazirci da ke cikin garin Kano. Ya fara karatun kur’ani a hannunmahaifinsa in da daga baya a ka kai shi makarantar allomakarantar malam Muhammadu Bamallo wanda yake zaune a bayan gidan wazirci. Wazirin Kano Muhammadu, mutum ne maison karatu don haka da zarar an yi sallar isha anci abinci to faba abin da iyalansa ke yi sai karatu har zuga lokacinbacci.Bayan rasuwar mahaifinsa a shekarar 1933 ya yi karatugun yayansa waziri Gidado haka kuma ya yi karatu a wajenlimamin Gwarzo malam Sa’idu lokacin yana can. Daga cikinabokan da suka yi zaman kuruciya akwai Alkali Badayi da Alhaji Nayaya da Abubakar Jakada. Tun tasowar SheikIsa Waziri an shaide shi mutum ne mai son mutane da ladabi da biyayya ba ya son wasan banza. Sa’oinshi, makusantansa da yan’uwansa sun tabbatar ba shi da abokin sa-in-sa ko kumafada ko tashin hankali.
Malam Isa Waziri ya yi aurensa na fari a shekarar 1948. Yana da yara 22.
Karatunsa da ayyukan da ya yi
Malam Isa Waziri ya fara da makarantar judicial da ke Shahuci a shekarar 1933-1940 inda take a matsayin firamare sannan ya je makarantar S.AS a matsayin sakandare. Ya yi digirinsa a vangaren shari’a a kasar Masar.
Malam Isa Waziri ya fara kasuwanci zamansa da wani mutuminqasar Labanon mai suna Sa’id Shon yana koyawa yaransakaratu sannan sannan ya kular masa da kasuwancinsa na gyaxa . Daga baya aka buxe masa kanti inda aka rika kawo masa gishiribeza da kuma sauran kaya. Bayan maigidansa ya komaqasar su, sai ya fara koyarwa a horon malamai ta Bichi yanakoyar da addini da Larabci. Daga canaka mayar da shi S.A.S inda ya zauna tun 1964-1971. Ya koma makarantar koyonLarabci ta Gwale (G.A.T.C) inda ya riqe muqamin mataimakinshugaban makaranta. Daga nan ya juya ya bar harkar malanta yakoma vangaren shari’a inda ya zama alqali mai yin shari’a indaaka kai shi kotun Munjibir. Ya zauna a wannan kotun na tsahonshekara tara. Daga kotun Munjibir aka kai shi Zakirai nan ma yazauna shekara shida. Daga nan aka mayar da shi kotun yara ta Shahuci.Malam Isa Waziri ya fara tafsin qur’ani tun a lokacin da yake shari’a a Zakirai da ya koma da aiki Birnin Kudu nan ma ya ci gaba da yin tafsiri a can, da ya koma Gezawa bai yi tafsiri ba a can, a Gezawa wa’azi ya yi. A shekarar 1981 ne aka nadashi masallacin Murtala . Dakta Hassan Gwarzo shi ya ba wa malam shawara akan ya fara tafsiri a masallacin murtala. Tun da Sheikh Isa Waziri ya fara tafsiri bai yi fashi ba saigaf da rasuwarsa. Mai ja masa baki Malam Ya’u Isma’il shi ne dai bai taba sauya shi ba a matsayin ma ja baki tunda ya farawannan tafsirin.
Halayensa
Halayen Sheikh Waziri da shaide shi da su akwai:
Zumunci da tsoron Allah da gudun duniya da juriya da son karatun addini da taimako.
Abubuwan da ya fi so a rayuwarsa
Yana son nazarin littafi da tafiyetafiye da sa farare kaya da tuwo miyar kuka da launin dorawa.
Garuruwan da ya ziyarta
SheikhIsa Waziri ya je kasar Saudiyya da Ingila da Farida da Denmark da Masar.
Zamansa Wazirin Kano
Annada Malam Isa Waziri a matsayin wazirin Kano ranar13/10/2000 . Asalin Sarautar Wazirci sarkin Kano Alu shi ne yafara nada sarautar Wazirci wanda aka nada waziri na farko wan Malam Isa Waziri waziri Amadu a shekarar 1879.
Rasuwarsa
Allah ya yi wa marigayi Sheikh Isa Waziri rasuwa ranar juma’a2 ga watan Agusta 2013 Allah ya jiqansa da gafara amin.


