Home Labarai Gaskiya da Sadaukarwa da jajircewa da albarkar Iyaye shi ne matakin Nasarata

Gaskiya da Sadaukarwa da jajircewa da albarkar Iyaye shi ne matakin Nasarata

by masta

KALLABI TSAKANIN RAWWUNA
Tare da
Batool Yusuf Ali

Hajiya Tasidi Muhammad Yakasai tsohuwar ma’akaciyar jinya ce ta ta fara aiki tun daga matakin farko har ta kai wan babban matsayi a cikin aikin jinya kuma uwa jajrtacciya a harkar da ta shafi zamantakewar iyali inda ake zuwa wajenta don neman shawara da warware wasu matsaloli da suka shafi zamantakewar aure a yau.

TARIHINKI

An haife ni a Birnin Kudu amma aiki ya kai maigidanmu can.Ina ‘yar shekara uku da haihuwa ya koma Gezawa da aiki yana alkali a lokacin. A 1956 aka saka ni a Firamare ta Gezawa a lokacin ina shekara 6 amma sanadiyyar an kai wana nima na kafe sai na bi shi. Mun yi firamare a nan shekara hudu sannan na wuce post primary school Provision Girls School inda shekara take a yanzu.Mun yi shekara uku daga 1956-1960 don lokacin da Najeriya ta sami mulkin kai muna makaranta mu muka fita muka yi faretin Karbar Goggon sarauniya a dai-dai inda asibitin Nuhu Bamalli yake a yau. Da wajen zama ne na hutawa wajen shuke-shuke ne anan muka tarye ta da la’asar ana I gobe za a bayar da mulkin kai. Washe gari kuma aka fita da mu faretin karbar mulkin. Mun dau jarrabawar shiga sakandire kuma a wannan shekarar aka gama gina GGC Dala ta ‘yanmata an kai mu mun ga gininta ya ba mu sha’awa. Amma da muka yi jarrabawar sai aka dauki Kadan a cikinmu aka ce mu tafi Queen Elezabeth College Ilorin a 1963 a lokacin da aka nada sarki Marigayi Alh Ado Bayero . Amma sai aka hana mu zuwa a gida aka ce dan musulmi bai kamata ya tafi nesa ba ya balaga yana karatu don haka aka tsare mu a gida. Sai aka yi min aurena na fari a shekarar 1964 inda aka bayar da ni gidan Alhaji Muhammadu Dangote wanda shi ne mmahaifin Alh Aliko Dangote. Zaman bai yi wu ba. Bayan na dawo gida ba ma jimawa Allah ya yi masa rasuwa. Ina gida na ga zaman ba zai yi wu ba ana haka sai na ga kamfanin Nigerian Airways suna neman air Hosters kuma ‘yan kasa sai na cika kuma na yi nasara na ci muka yi interview a Lagos. Amma kuma sai nayi bincike kancewa aikin wannan in ka yi aure zai zama ba ka da lokacn mjinka da ‘ya’yanka kuma iyayena nasan ba za su yarda ba don haka na ce na fasa. Amma sai ya zamana su kuma kamfanin Nigerian Airways din sun ce ba za su sake ni ba don haka suka kai ni Kano printing press in koyi telephone operator. A da telephone din katon akwati ne in an yo waya za a tambayi wa ka ke nema an san layin da ka ke nema za a hada ka da layin. Na iya wannan sosai. Sai kuma rannan na shiga asibiti sai na ga nurses suka ba ni sha’awa don haka na gudu a Nigerian Airways na nemi school of Nurses nan muka yi traininn na wata shida sai ka zabi me ka ke so ka yi. Ni sai na zabi aikin unguwarzoma inda wata sha takwas ake yi. A lokacin da aikin Unguwarzoma na fara.Galadima na yanzu Allah ya Kara masa lafiya shi ya dauke ni aiki ba wani offer sai dai a rubuta maka a ce ka je wajen wane an dauke ka aiki. Wakilin magani ya tura ni shikenan. Na fara aikin a 1969. Ina da yara shida da Maigidana a halin yanzu.

Ya Gwagawarmayar Aiki?

I to! da yake ni a karamarhukuma ne ina aiki ne a kananan asibitoci kamar Nuhu Bamalli asibiti ne da ake kula da mata da qananan yara. Na yi aiki a asibtin Marmara akwai Dala da Sabon gari france road an kaini Kumbotso na zauna a asibitin Bebeji na zauna a munincipal na zauna a Nasarawa akwai a gidan Mai martaba Sarkin Kano. Alhamdlillah Tun muna kananan ma’aikata har Allah ya sa muka zama manya muka zama incharge. Da aka raba Kano da Jigawa sai aka ba ni shugabar Ma’aikatar lafya ta hukummar Birni da kewaye. Tafiya dai tana qara nisa har abin ya zo na ga abubuwa sun fara lalacewa aikin ba wani girma ba secuitity sai na ga ya kamata kawai na bar shi. Tunda ni da ma tun farko aikin nan sha’awa ce akwai abubuwa da yawa da suka taso Wadanda ba zan iya jurewa ba don haka na ajiye aikin a shekarar 1998. Bayan na yi ritaya ne ina zaune sai kuma sabani ya shiga a Kungiyar Fansho da ‘yankananan hukumomi inda suke karar a cikin qungiyar fansho ba ‘yan kananan hukumomi har suka kai ga kotu.Daga baya sai aka ce a sasanta aka zabe ni na zama women coodinator ta Nigerian Union of Pensioners. Ina nan ina ciki duk zabe na kan shiga takara kuma in na shiga takara in dai nace ni zan tsaya suna yi min wannan karar ba me tsaya a wanann matsayi.A qarshe sai qungiyar ta kasa ta dauke ni a cikin National Trustee na koma Abuja yanzu watan Afrllu na gama tenure din mu ta biyu a 2021.

Me ne Aikin Kungiyar ‘yan Fansho

Tana ayyuka da daman gaske dukkan jihohin nan 36 da Abuja muna da reshe a kowacce jiiha. akwai chairman da sakatare da sauran muqamai na qungiya. Haka kowacce qaramar hukuma ita ma da nata ana bibiyar yadda ‘yan fansho suke, yawansu a kowacce qaramar hukuma da kuma wanne hali suke ciki. Idan abu ya taso ya fi karfin jiha sai a tafi tarayya. Mu ke shirya zabe da bin duk wani hakki sannan a duk inda hukuma za ta tantance wani dan fansho komai nisa komai hatsari sai mun je an yi a gaban idonmu don mu tabbatar ‘yan Fanshon ake yi wa. Wani ma ya mutu ‘ya’yansa za a ba wa hatta a yanzu da ake maganar mafi kankantar albashi dubu talatin muna nan su ma ‘yan fanshon muna kokawar suma nasun ya zama mafi qarancin ya zama talatin ne.

Ya Kike Ganin Ftowar Mata a Wancan Lokacin a aikin jinya?

Ai ba yawa a wancan lokacn duk northern state a Kano suke yin training na Nursing. Mata a wancan lokacin ba yawa ko ma babu za a ce

To Ya Aka Yi Ke Ki Ka Samu Wannan Damar

A da idan ana neman aiki ko neman karatu sai an shiga gidan manya. Abin nufi su manyan kasa suka bayar ballantana kai na qasa? Allah ya sa ni na girma a gidan alqali don haka za a dauki yara ne daga gidan hakimi da dagaci da alkali da mai’unguwa da sauran masu madafun iko.

Mai Ki ke Ganin Ya Fara Lalata Aikin Jinya a yau?

Siyasa ita ce ta shigo harkar lafiya sai abubuwa suka lalace. Mu lokacin da muka yi aiki mun yi shi ne saboda Allah sai kuma sha’awa. Ni yanzu abin da ke ban mamaki mutane sun raina wannan takardar da ake cewa acceptance letter gani suke an ba ka aiki ka rubuto ka yarda da duk qa’dojin aikin ka sa hannu an sa a file an rufe ka dauka Magana ta mutu to wallahi Magana ba ta mutu ba wanda ya halicce ka shi yana ganinka. Ga rashin shugabanci misali ko a kaina da tafiya tai tafiya ne ya zama in ka gyara wa mutum kan ya bi dai-dai sai a ce kai ba ka isa ba su ne suke da dama in sun dauki wani abu da ba hakkinsu ba in ka ce don me sai cibi ya zama Kari, Alhalin ni na yi shugabar lafiya amma daidai da Panadol ban taba daukarsa daga store na kawo shi gidana ba kuma a lokacin ba zan bari a dauka ba. Ai daga baya bayan na ajiye aiki na gwada aikin immunization a lokacin Turawan sun Dora mana amana saboda mune manya don haka suka sakar mana aikin to ko a lokacin in ka ga wani abu da ba dai-dai ba in ka ce a gyara sai cibi ya zama qari na fara baqin jini sai na koma gefe. Don ni babu wanda zai danqa min amana kuma ana wasa da ita. Ka ga rashin amana nan ma ya taimaka wajen lalata harkar jinya.

Ya Ki Ke Ganin Za a Gyara Harkar a Yau

To ai harkar aiki ta riga ta tafi kin ga dai lokacin da muka yi aki asibitoci ko’ina akwai kayan aiki yanzu kuwa babu. kin kuwa san harkar aikin asibiti ba zai yiwu ba kayan aiki ba to ya za a yi aikin ya gyaru? Duba a bangaren likitocin nan kowa yana da asibitinsa, da ka je da wani abu hoto ko aiki sai ya tura ka asibitinsa. Su ma maikatan ba bin doka da ka”Ida . A da in ka Kara minti biyar a lokacin aikinka ba ka zo ba sai an yi maka displine manyan meturorin suna bakin gate amma yanzu ba metron din da ta isa ta tsawatarwa da wata nurse. Dole a cire siyasa in ana son aiki ya gyaru. A da dan siyasa daban ma’aikacin jinya daban ba su da wata alaqa kai ko ada kana da ra’ayin siyasa ba ka isa ka goyi bayan wani ba saboda ya karya dokar aiki yanzu kuwa aikin ya cuxanya da ma siyasar watakla ma yanzu ba scheme of service din ma’aikata sun zama ‘yan siyasa

Bayan Aikin Jinya Kin Tava Wasu Sana’oin?

Ai ni tun da na tashi ma ban san me ne zaman banza ba . Na yi sana’oi da dama a ciki na sayar da uniform na nurses na yi ma chemist har uku amma ni da mutane muka karar da wajen ko a hanya na ganka da kati sai na ce zo mu je chemist na b aka magani kyauta.

Me Ki ke Alfahari da Shi?

Alhamdlillahi an yi abubuwa da yawa amma kuma ina alfahari da zamana a qaramar Hukumar Kumbotso don kuwa duk wani asibiti a hukumar Kumbotso ni na assassashi aikin da na yi a can sai dai a Dora a kan nawa in ma za a Dora din. Kusan duk asibitocin da ke Kumbotso mu muka yi hatta babban asibtin da ke Kumbotso wanda yanzu ya zama Department na asibitn malam Aminu Kano Teaching Hospital da kudina na sai plan din a ministry of health don kawai a yi asibitin Kuma muka sayi kayan asibtin muka bude asibitin Fanshekara daga cikin kayan wannan wajen muka bude asibitin Sheka muka yi upgrading dinsa. Ni na zuba kayan da suke cikin asibitin sheka amma yanzu da za ka koma za ka tarar da abin da aka saka ba. Ina alfahari da zamana da mutane lafiya wasu na taimaka musu wasu sun taimaka min kuma ba mutumin da ya taba kawo min taro da sunan cin hanci ni abin da na dauka in ka zo neman abu in zai yi wu zan fada maka in kuma za a dau file Dinka ne kuma zai zagaya wurare to zan fada maka in ka ga shuru to ba daga guna ba ne. Ba na mantawa a Kumbotso a rana daya sai da muka bude health post goma sha biyu wannan ina alfahari da shi. Ni na kafa qungiyar Head of departments forum ta Kano ba mu fi mu bakwai ba muka yi shawarar kafata har na bar aiki ni nake shugabantar Kungiyar. Mun yi fafutika ta gyara aiki a lokacin musamman imunazation muna tsaye a kai za mu hadu 44 local govnrment kowa zai fadi team nawa ne da shi muna tsaye daga jajircewata a lokacin na zama zakaran gwajin dafi don in har na fadi a Immunazation coverage din ya zama low to kuwa ba wanda zai kai ni. A da tafiya ake wani bai san wani ba amma sai da muka hada Kungiyar nan muka tafi tare . Kuma ni kadai ce mace a tafiyar nan

Ya Ki ke Hada Aikin Jinya da Renon Yara da Kuma Kula da Gida?

Lokacin da primary health care ta shigo sai mu kai biyun dare muna aiki za ka dawo gida ka tarar yara tuni su yi bacci za ka tura su makaranta ka koma aiki. Da goyon ciki da goyo haka aka yi duk akin dole ne ka nemi mai rike maka. A haka don galibi ni ‘ya’yana ‘yan’uwana nake bar wa su. Mu kuma aiki na asibiti a da ba ma shiga da danmu hatta kayan jikinmu na aiki yana da ma’ajiya a asibiti saboda kada ka dauko wani abu na cuta ka kawo cikin gari. Yana daga cikin abin da ya sa wasu cutocin suka yi yawa. Ya kamata asibtocinmu su gina wajen renon yara a daina shiga ko’na da yara a asibiti a yi wurin reno don hadari ne. In kin ga na shiga da Dana asibiti to ba shi da lafya.

A Baya Kin Ba mu Labarin Kun Taryi Sarauniya Lokacin Karvar Mulkai A Kano Ne Aka Bayar da Mulkin?

A’a A Lagas ne amma Kano lardi ne ita Goggon Sarauniya da ta zo sai da ta zo Kano da gayar da sarki saboda sarakunanmu suna da kima a idonsu.A lokacin muka yi faretin aka ba mu tuta da kofi a yayin faretin ana farar sunayen makarantunmu. Da ma shekara ta zagayo sai da aka kuma yin biki muka yi fareti aka ba mu tuta.

Hajiya Kin ga Jiya Kin ga Yau Musamman a Zamantakewar Aure ya Kike Ganin Tsarin a yanzu?

Ai a zamantakeawr aure an bar kari tun ran tubani ne. Mu al’adunmu na arewa kana shekara goma sha hudu za a yi maka aure. Amma yanzu da ka ce wa ‘yarka ga miji sai abin ya zama tashin hankali da ka ce ga wadda za ta aura sai ta ce za a yi mata auren dole ta kai ka kotu ko ta kai ka hisba amma a da ba ka da ta cewa duk abin da iyaye suka zartar.

Hajiya ko da ba Ka So?

Wanne kuma so? A ina aka san so din ? A al’da ta Bahaushe ta Soyayya mu ba mu san wata soyayya ba mu abin da muka sani shi ne mutuncin inda za a kai ka da wanda za a bawa da alaqa da ke tsakanin iyayenku da kuma kyawun mu’amalarka a zamantakewa in an yaba hankalin zaman gidan. Yanzu ne ake maganar wata soyayya. Magana ce ka isa munzalin za a yi maka aure za a ce to ga dan gidan wane yana da kirki yana da zuciya yana yin noma ba kamar yanzu da za a ke la’akari da wane gidan mai kudi ko arziki ko ya zo da mota da sauransu. Amma a baya kawai mutunci ake kallo da aminci da amana. Wani ma fa sai uban ‘yar ya Daura auren ya bayar da sadaki za a ji.

Ya Kike Ganin Tasirin Irin Wannan Auren?

To ai ga tasirin nan za mu ga auratayya mai albarka ga tasirin albarka ‘ya’ya da jikoki ai mutuncin gidan da za a kai ka ko sabani ya tashi ba kai da aka auro ake kallo ba a’a gidanku ne a ke gani haka shi ma mijin ba zai taba musguna musu ba haka iyayen miji su ma suna ganin surukansu a matsayin ‘ya’yansu.

Savani da Ake Samu Tsakanin Surukai a Baya Kenan Duk Babu Wannan?

To ai ke matar da da aka kawo ki kina kallon surukarki tamkar mahaifyarki ne ita kuma uwar miji ba ki da bambanci da ‘yarta ta cikinta to ta ina za a sami matsala? Ai Dora aure da ake yi ne a son rai duk yake kawo ire-iren waxannan matsaloli. Saboda aure ne ake yi ba harsashi. Hatta Daura wa saurayi nauyi da ‘yanmata da ma iyaye ke dorawa saurayin ‘yayansu kamarsu anko shi ma yana kawo mace-macen aure. Kai hatta tarbiyyar ita ma duk ta kawo naqasu a aure a yau. Sannan mu iyaye ba ma zaunar da ‘ya’yanmu mu fada musu mai ake nufi da auren me ake zaton in an yi auren za a samu sannan me ne makomar auren. Amma aure a yau ana yinsa ne kara-zube kawai akan abin duniya ake Dora shi. A da kuwa rufin asiri ake nema cin abinci sau uku a rana sannan in sallah ta zo ya yi mata sutura. Iyaye ba su taba sa ran aka wo musu komai daga gidan ‘yarsu ba maimakon haka ma kullum sune suke qoqarin su kai mata.

Me ki ke Gani shi ne Matakin Nasararki a Yau

Ito na farko dai komai daga Allah yake shi ya nufe mu da komai sannan na biyu ni a rayuwa a mike nake ni ba na yin kwana-kwana sannan a lokacin an yi aiki fisabilillah . sannan akwai jajircewa Ban taba zama daga safe har yamma ina ofis a zaune ba kullum kafin na shiga ofis sai na bibbiya asibtocin da ke qarqashina na ga wanne hali suke ciki in kuma har na shiga ofis latti to kuwa bayan na gama harkar ofis din zan fita na zagaya. Don dai na ganewa idona. Bana shayin na fadawa kowa gaskiya yayin da ka yi kuskure wannan ta sa muka yi farin jini muka yi baqin jini. Ni na yarda da godiyar Allah don haka ina godewa abin da duk nake da shi. Ina da imanin na fi wani kuma wani ya fi ni.

A yanzu Haka Kina Iya Gwada Aikin Jinya a Cikin Gida?

Kwarai kuwa ina iya yin komai har gobe. Ai ni da na koyi aiki koyansa na yi don ina da sha’awa. Don haka ko yanzu in aiki ya same ni ina yi.

Wanne Abu ne na rashin Hankali da ba za ki manta da shi ba ?
Rashin maigidan mu wato Alh muhammad Yakasai maaikacin Radio sanannan dan jarida .Allah yayi masa rahama Ameeen. Wannan rashin ya girgiza ni.

Abin Farinciki kuma fa?

A 2021 April Kungiyar yan fansho ta qasa ta sake zaben sabbin shugabanni wanda ya kawo qarshen zangon mu na biyu 8yrs a National.

kafin nan kungiyar yanfansho ta jihar kano ta karrama ni da lambar MERIT AWARD! kuma bayan mun gama gwagwarmayar mu a kingiya ta qasa na dawo gida Kano sai kungiyar yan fansho ta jiha ta sske bani mukami na patron Uwar kungiya kenan wa da Wanda har yanxu ina kai.

Toh Allah cikin ikon sa kuma bara kenan sai kuma Jamiyyar matan Arewa ta qasa karkashin shugabar ta qasa wsto president HAJ RABI MUSA SAULAWA ta ai ko mana da takardar nadin zama kwamiti na ruko na wannan jamiyya a jihar kano wadda niche shugabar wannan kwamiti,
kwatsam sai wadda ta sauka ita ma ta bada nata kwamitin kuma ta garzaya kotu ta Kai mu Kara tun daga Saman kungiyar har kan mu .
wannan shugabancin ya sake dawowa hannun mu bayan da maisharia ya yanke cewa mune halattattun shugabanni. Alhamdulillah.
Sun ce kuma nice Mataimakiyar shugaba ta qasa ta wata kungiya da aka kafa ta tsakanin kanawa da bayin mu zage zagi wadda muka hassasa ta kuma munyi mata register da CAC, a matsayin cikakkiyar kungiya. bisa doron shugabanchi yadda hukuma ta tanada.
wannan kungiya ta kanawa zage zagi cultural Association ta samu karbuwa daga sarakunan mu manyan malamwi na addini da na Boko .

Ya Gwagwarmayar Siyasa kuma?

Duk da ba mu shiga Siyasa Kai tsaye ba to amma mun wayar da kan mata kan Siyasa kwarai da gaske tun daga kan muhimmancin yin katin zabe har zuwa kan fita zaben da kira kan mata mu zabi cancanta kada mu zabi Wadanda ba su dace ba.
ina shugabantar kungiyar Tufun maliki women innitiative wadda wannan ita ma nice na kirkir ta kuma muna yin Tarurruka lokaci lokaci sannan mukan kai ziyarar jaje murna, ko dubiya ko gaisuwa ga duk inda muka ji akwsi bukatar yin hakan

Idon Gari na godiya
Nima na gode.
Mun gode

Related Posts

Leave a Comment