Home Labarai HABBATUS-SAUDA GA LAFIYAR IYALI

HABBATUS-SAUDA GA LAFIYAR IYALI

by masta

Lafiyar Iyali

Tare da

Bilkisu Yusuf Ali

Amfanin Habbatus- sauda ga lafiyar Iyali

Ana kiran habbatus-sauda da sunaye daban-dabansaboda muhimmancinta da shahararta. Bayan sunantahabbatus sauda ana kiranta Habbatul Baraka. Da Turanci kuma ana kiran ta da blessed seed, Black cumin, Nigella sativa , black caraway da sauransu.

Daga cikin fa’idojin habbatus sauda akwai:

• Magance larurar rashin ruwan nono ga maishayarwa. Ga macen da ta haihu amma ba ta da ruwan nono idan aka samu garin habbatus-sauda a zuba a madara mai dimi ta sha yana sa gudanarruwan nono. Ko kuma a yi salalan garin hulba in an sauke a zuba zuma da garin habbatus sauda shima za a dace da yardar Allah. Wannan hadi yanada muhimmancin gaske ga mata don ingantajikinsu da saukar da ni’ima musamman ga matarda ta haihu.
• Ga wanda garkuwar jikinsa ta yi rauni shan man habbatus sauda ko garinta a abinci ko abin sha ko a sha haka yana da matukar muhimmanci yana dawoda garkuwar jiki ta samu inganci.
• Habbatus sauda yana da matukar amfani a rauni kokuraje musamman budaddu. Bayan an tsaftacewajen. Ana shafawa a saman ciwon.
• Ga wanda yake da karancin maniyyi ana samungarin habbatus sauda cokali daya babba a samukwai guda biyu da farar albasa da tafarnuwa a yayyanka ta a saka a ciki a soya kwan sama-samawato ruwa-ruwa a cinye zama daya.
• Ga wanda yake da matsalar da ta shafi fata kowacce iri ce ana amfani da man habbatus saudada man zaitun da ma’uwardi a hade su wuri gudaake shafawa sau biyu a rana. In sha Allah za a samu sauqi.
• Ga mai fama da larurar tsakuwar koda a sami zumamai kyau a sami garin habbatus sauda a cude su a ke shan babban cokali sau biyu a rana.
• Wanda yake ciwon kai sai a sami habbatus sauda tagari a cude ta da ma’u khal tuffa a ke shafa wa a goshi sau uku sannan ana digawa a hanci.
• Man habbatus sauda yana magance larurar ciwonkunne ana hada shi da man zaitun ake diga wa a kunne.
• Ga mai larurar shafar shaidanu ana amfani da man Habbatus sauda a rinka sha ana shafe jiki da shi.
• Yin turare da kwayoyin habbatus sauda yana korarshaidanu a wuri.
• A samu garin habbatus sauda a hada da garintafarnuwa da citta kadan da zuma mai kyau a cudesu ake shan babban cokali daya kullum wannanyana magance larurar sanyi ko mura wadda ta dadea jiki.
• Ga wanda cikinsa yake yawan kumbura musammanyara yana da kyau ake ba su man habbatus saudakadan suna sha.

Fa’idojin Habbatus sauda manta da garinta ba za a iyafadarsu ba duka sai dai a tsakuro wanda za a iya. Abinnufi dai ya kamata a ce kowanne gida akwai habbatussauda don tana da muhimmanci kwarai a zamantakewar iyali.

Related Posts

Leave a Comment