JIGA-JIGAN APC SUN MARAWA SULE GARO BAYA A KUJERAR MATAIMAKIN GWAMNAN KANO
8
Tsohon Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi na jihar Kano, Hon. Murtala Sule Garo, nakan gaba cikin masu neman kujerar Mataimakin Gwamnan Jihar Kano.
Majiyoyi sun bayyana cewa Garo ya samu gagarumar goyon baya daga “bangaren” Yan tsohuwar jam’iyyar APC a jihar Kano.
Hakan yabiyo bayan wani taron masu ruwa da tsaki na tsagin tsohuwar APCn manda Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kira a jiya asabar.
Majiyoyi da ke da masaniya kan taron manyan masu ruwa da tsakin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kira sun bayyana cewa Garo ya samu kusan kashi 90 cikin 100 na amincewar shugabannin jam’iyya da manyan jiga-jigan da suka halarci taron. Taron, kamar yadda masana yadda ya gudana suka bayyana, wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kai a jam’iyya da kuma inganta tsarin mulki a jihar.
Wannan ci gaba ya biyo bayan murabus ɗin tsohon Mataimakin Gwamna, Abdussalam Aminu Gwarzo, wanda ya bar kujerar da gwamnati ke ƙoƙarin cike gurbinta ta hanyar shawarwari tsakanin manyan bangarorin jam’iyyar.
A yayin taron, gwamna ya buƙaci tsohon tsagin APC da su gabatar da sunaye uku na mutanen da suka cancanta domin a yi la’akari da su.
Bisa wannan umarni, masu ruwa da tsaki sun gabatar da waɗannan sunaye kamar Haka: Hon. Murtala Sule Garo, Hon. Rabiu Suleiman Bichi, Babban Darakta na Hukumar Raya Kogin Hadejia-Jama’are, da Hon. Kabiru Alhassan Rurum, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Rano/Kibiya/Bunkure.
Majiyoyi sun jaddada cewa gabatar da sunayen uku an yi shi ne bisa buƙatar gwamna kawai, ba yana nufin akwai rabuwar kai a cikin Masu ruwa da tsakin ba.
Duk da tsarin gabatar da sunayen da ya haɗa kowa, tattaunawar da aka yi a taron ta nuna kusan yarjejeniya kan Amin cewa da abawa Hon. Garo, wanda ya samu kusan kashi 90 cikin 100 na goyon baya.
Fitattun jiga-jigan da aka ce sun nuna goyon baya ga takararsa sun haɗa da tsohon Gwamnan Kano kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje; da shugan kwamatin kasafin kudi na majarisar dokokin Najeriya, Abubakar Kabir Bichi; da tsohon Mataimakin Gwamna kuma tsohon Karamin Ministan Gidaje, Abdullahi Tijjani Gwarzo; Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila; Sanata Garba Lado; jigon APC A.A Zaura; tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Hamisu Chidari; da ɗan Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, da sauransu.
Masu ruwa da tsaki sun danganta goyon bayan da aka nuna wa Garo da ƙwarewarsa ta siyasa, kwarewar gudanarwa, da kuma faɗin tasirin sa a matakin ƙasa da ƙauyuka a faɗin Jihar Kano.
A yayin taron, Hon. Doguwa ya bayyana tarihin siyasar Garo, inda ya ce ya taɓa zama Sakataren tsare- tsare na jam’iyyar PDP a 2007, Mai Ba da Shawara na Musamman ga Gwamna a gwamnatin tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso, sannan kuma ya zama zaɓaɓɓen Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo, inda ya kuma kai ga zama Shugaban hadaddiyar ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta jihar Kano wato ALGON.
Bayan kafa APC a 2014, Garo ya zama Sakataren tsare- tsare na farko na jam’iyyar a Kano, inda daga bisani aka bashi mulamin Kwamishinab Kananan Hukumomi da harkokin masarautu a Shekarar 2015 zuwa 2019 bayan nasarar JAM’IYAR APC a Zaben 2019 Ankara baiwa Hon. Muratala Kwaminshinan Kananan Hukumomi a Karo na 2 daga Shekarar 2019 zuwa 2022 inda.ya ajiye domin Tsanyawa takarar mayaimakin Gwamna an JAM’IYAR APC a Zaben Shekarar 2023.
Majiyoyi daga taron sun bayyana cewa shigar Bichi da Rurum cikin jerin sunayen ya kasance bisa umarnin gwamna ne, ba don nuna takara ko gasa a tsakaninsu ba.
Masu ruwa da tsaki sun lura cewa dukkanin su biyun na rike da muhimman mukamai a yanzu kuma suna bayar da gudummawa mai yawa a waɗannan ayyuka. Saboda haka, ganin su ci gaba da ayyukansu an ɗauka zai fi dacewa don kauce wa ƙirƙirar sabbin guraben mukamai a tafiyar gwamnati.
A gefe guda, Garo wanda a yanzu ba ya rike da wani mukami na gwamnati tun bayan zaɓen 2023 an ɗauke shi a matsayin wanda ya fi dacewa ya karɓi wannan matsayi ba tare da kawo cikas ga tsarin gudanarwa ba.
Masu nazarin siyasa na ganin cewa yiwuwar nadin Garo na iya ƙara ƙarfafa haɗin kai a cikin APC a Jihar Kano tare da inganta zaman lafiyar siyasa da gudanar da gwamnati.
Yayin da shawarwari suka kammala, yanzu an mai da hankali kan matakin ƙarshe na gwamna wanda ake sa ran zai ɗauka nan ba da jimawa ba, matakin da zai nuna yadda za a tsara shugabancin jihar anan gaba.


8