Home Labarai BABU BATUN ZUWA KASAR WAJE ASIBITI DON GANIN LIKITA NAN GABA IN JI ME DAKIN SHUGABAN KASA BUHARI

BABU BATUN ZUWA KASAR WAJE ASIBITI DON GANIN LIKITA NAN GABA IN JI ME DAKIN SHUGABAN KASA BUHARI

by masta

Maiɗakin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari. Ta ce “Yanzu babu sauran zuwa ƙasar waje duba lafiyar wani shugaban Nijeriya…”

Haj. Aishatu Buhari ta bayyana haka ne cike da karsashi, a lokacin da ake duba asibitin fadar shugaban ƙasa dake Villa, wanda ta ce ya laƙumi maƙudan kuɗi masu yawa da ake daf da kammala shi.

Sai dai a lokacin da maiɗakin shugabam ƙasar take wannan bayani, ana cikin kwana na biyu da fara yajin Likitoci a ƙasar nan.

Asibitin fadar gwamnatin Nijeriyar da a yanzu a ke daf da kammala shi, ana ganin idan har aka kammala shi, to zai kawo ƙarshen tafiya ƙasar waje ga duk wani shugaban ƙasa, ko muƙarrabansa don a duba lafiyar su.

Abin jira a gani dai a yanzu shi ne, shin samar da asibitin zai kawo ƙarshen fitar shuwagabannin ƙasar nan zuwa asibitocin ƙasar wajen don a duba lafiyarsu?

Daga: Nafiu Salisu

Related Posts

Leave a Comment