Home Labarai Ni na fara Sakin album din Audio na sayar nawa na kaina amma da sai dai a ce best of sai a fadi sunan Fim.

Ni na fara Sakin album din Audio na sayar nawa na kaina amma da sai dai a ce best of sai a fadi sunan Fim.

by masta

MUDASSIR KASSIM FASIHI GWARZO ABIN KOYI

An ce ba ka iyawa ba ka gamawa kuma ba a yabawa in ka rike wannan to gwiwarka ba za ta yi sanyi ba a kullum ka sa kare addininka da al’adarka a gaba a duk abin da ka sa a gaba to ba za ka tabe ba. Wannan shi nemakami da Malam Mudassir ya rika don haka har yau tauraruwarsa ke haske in har ana maganar Waka.

TARIHINKA

An haife ni a Kano. Na fara neman ilimina daga gida kasancewar gidanmu gidan ilimi ne akwai makaranta don haka na fara karatuna na muhammadiyya a hannun mahaifina daga nan aka sa mu makarantar allo mun yi makarantar islamiyoyi da dama kama daga makarantar rana zuwa ta yamma da ta dare wanda Alhamdulillahi zuwa yanzu mun sami abin da muka samu a Bangaren karatun islama.A kuma boko nan ma na yi makarantar firamare da sakandire a Kano . Na yi qaranar diploma a FCE Kano sannan na yi wata qaramar Diploma xin a jami’ar Bayaro a vangaren jarida na kuma yin babbar diploma a bangaren shari’a a makarantar Legal da ke Kano.

FARA WAKA

Na fara waka tun lokacin ina makarantar firamare lokacin da aji yake ba malami sai akan tashe ni cikin yara sai a sa ni na yi waka. A lokacin, ina wakoli ne irin su mai fitsarin kwance ko dakiki marar kokari yara za su ta kada tebur ni kuma ina wala. Abin haka ya taso har lokacin da aka fara wakoki irin na Madhu na yabon Annabi (SAW) Akwai kungiyoyi irin su Usshaqu da madinatul ahbab da akwai kungiyoyi irin na malam Rabi’u Usman Baba da sauransu mu ma mun kafa namu anan Kurnar asabe Madinatul Ahbab a nan muka fara har ake kira na da dan’autan me wake saboda kankantata a lokacin. Amma sai na ajiye na komakaratu.

Wakar fim kuwa ba na mantawa shagona da nake yin askin baba a lokacin Shehu Hassan Kano da Husaini Sule Koki suna zuwa hira kusa da wajen wurin wani yayana abokinsu. Ni kuma a lokacin ni sha’awata na zama dan wasa ne sai na sami Shehu Hassan Kano nace ina son na zama dan wasa sai ya ce ba kana yin waka ba? sai na ce ey. Sai yace to zai hada ni da kamfanin fim na Sarauniya sai mukaje. Daga nan na fara wakar fim da waqar

Sannu-sannu Halifa jinjina Mukai maka

In da rai da lafiya mulkinga kai za ka riqa

Sai kuma

Ga mu cikin harka noma na shuka dan daminarga da albarka

Daga nan sai muka tafi Iyantama Ali Baba ya yi mana kida rana guda muka fara ni da Misbahu M Ahmad.

Amma waqar da na fara yi ita ce waqar madahu da na yi a lokacin ban fi shekara 12-14 ba

WACCE WAKA CE BAKANDAMIYARKA?

Bakandamiyata a waka it ace

Bayani na taho na ba ki kan soyayyata

Cikin nutsuwa tsaf a waye ba na yin wauta

Mutanen kirki da gaskiya suka shiryata

Tunanuna ai da ni da ke ba savawa

Uhum! Ka ji maigida a bar dai tonawa.

An yi wannan waqar ne a fim din (Nagari)

Amma ni wadda na fi so ita ce wakar Fim din Rana

Rabbi ga zare nan a saka ka ba ni baiwa

Baiwa ta saka arziqi ga kowa

Ey Rana ta haska baiwa…

Abin da ya san a fi son ta shi ne na yi addu’a acikinta.

SU WA YE IYAYEN GIDANKA?

Iyayen gidana sune Malam Shehu Hassan Kano da Auwalu Muhammad Sabo har gobe ina girmama su a matsayin iyayen gidana tunda sune suka yi min silar shigowa . A bangaren kida ina girmama Mukhatari Kwanzuma na zauna a wajensa lokacin ba ni da ofis. Awajensa har na koyi kida ya koya min abubuwa da dama ni da marigayiya Rabi Mustapha.

WANNE TASIRI WAKOKIN FINA-FINAI SUKA YI A YAU

Gaskiya wadannan wakoki sun taka muhimmiyar rawa saboda sau tari ma wakokin ke sayar da fina-finan a baya ma mun ta damuwa a raba fim da waka. mu mawaka a bar mu mu yi ta wakokinmu su ma ‘yan fim su je su yi fim dinsu amma su ‘yan fim din suka ki saboda wakar tana cikin kyalakyalen fim duk da sukan yi fim din ba waqar kuma ya karbu amma su sun fi so dai a yi da waka.

ZA KA IYA WAKAR FIM A YANZU?

Ai ita waka yayi ce, da mu ake yayi yanzu mun girma mun bar wa wasu mun tafi wani layin. Industry din,tunda tana da fadi dole kana girma kana kaucewa inda ka san akwai yarinta a ciki kana komawa inda hankali da dattijantaka take

GWAGWARMAYAR DA KA YI

Gaskiya an sha gwagwarmaya ba akan kaina ba kadai har ma ita wakar kanta, in ki ka duba daga inda aka ratso ake inda ake a yau. Misali a da waka dole sai ka iya sannan a yi recording haka aka taho aka sami wani mashin da in an yi za a iya ware kida. Ana nan aka zo kwamfuta sannan yau abu ya kara girma mawaki yana hulda da internatiol media za a iya daukarsa ya je ya yi performance a ba shi makudan kudi da sauransu. An kai matakin da mawakan na da daraja da kima ba kamar da ba.A da, sanda muka fara waka kusan kyauta muke yi saboda duk a lokacin koya muke kuma harkar babu jari. Yan siyasa suna da mawakansu kamar su Rarara da Ibrahim Ibrahim in kuwa ana maganar makadin mata ga su gwanja da Adam Zango nan haka ma fina-finan. Haka in kika dawo bangaren tallace-tallace a kwarzanta abu a ji ana sha’awar sayensa to ga mu muma. A bangaren yabon Annabi SAW kuwa in ka ji wakokin Hafiz sai ka ji kamar ka mutu yanzu ka hadu da Annabi saboda shauki.

ZA A IYA KIRAN WAQA DA SANA’A?

Ey to, a gargajiyance ba za a kira waka da sana’a don suna ganin waka roko ce kawai ba amma a zamanance waka sana’a ce , amma a yanzu in ka yi waka kai da kanka zaka tafi nema mata kasuwa ko ma ka ga wani a gefe zai ga in ya dauki wakar ya sarrafa kasuwancinta za a sani alheri shi da mawakin.

NASARA

Alhamdulillahi nasara kam an samu na farko dai lokacin da muka fara waka na sha kaiwa gidan radiyo a ce a’a wannan harka ce ta yarinta za ku bata mana yara ku bata mana tarbiyya ga mu da mawakanmu irin su Dankwairo da su Shata. Tun muna yi ba a jin mu ana korarmu har Allah ya kawo Freedom Radio suka ce ina muke ga program sukutum guda an ba mu daga nan sai gidajen radiyo suka ce muna ina.A jamio’I an saka maa cikin hajarsu dumu-dumu suna turo mana dalibai. Ana nazarin wakokinmu. Yanzu rayuwar sai da mu ‘yan siyasa sai da mu za a aurar da yara sai da mu shago ka bude sai da mu wannan ma babbar nasara ce.

Kana hulda da manyan mutane wanda a da ko a tv ka gansu sai ka rusuna amma kai ka zauna da su ka ci abini da su ka yi hira da su da sauransu.

Ni ne wanda na kawo kalangu a tsarma a waka na kira Tambai na ce ya zo mu koya masa. A lokacin da da muka yi wakar Nagari wani malami ya tare ni ya ce Allah yi min albarka yace satinsu biyu ba sa Magana da matarsa amma matarsa na jin waqar nan sai suka shirya yace abinda ya faru a wakar matsala ce tsakaninsu bai ma san ya yi mata laifin ba amma ana gama waqar ta ce laifin da ka yi min kaza da kaza shikenan suka shirya.

A dalilin waqa na je wurare da dama a dalilin waqa na je Ghana da Nigerda Chadi Yawundi da sauransu. A irin wannan ziyarce-ziyarcen mun yada harshen Hausar wadanda kuma ke jin Hausar amma ba ta yi laushi ba a dalilin waka sun gyara wani ma bai iya Hausar ba amma in yana saurara yana bi sai ka dauka ya kware. Hatta kira a zauna lafiya akwai wata waqa da muka yi kuma har yanzu ana amfani da ita.

Ni na fara sakin album din audio na sayar nawa na kaina a cikin mawaka amma da sai dai a ce the best of sai a fadi fim kaza. Amma ni na fara karya wannan sai na ce idan na yi wa mai fim waka sai na ce ni ma ina son zan yi amfani da ita in an kwana biyu.

Ni na fara kada life band a wannan masana’antar me kada jita da kalangun duk ga su a zaune na fi shekara goma ina gwada wannan wakokina yawanci live nake yi ban a son miming duk da yake maming yana da tashi ranar.

QALUBALE

Babban kalubalen shi ne yadda al’mma suke kallonmu a wancan lokacin ana ganin mun kawo wani sabon abu maimakon wanda aka sani tun iyaye da kakanni irinsu Dandawo da Dankwairo da Shata da sauransu. A ka dinga kin mu har aka bari wasu ma suka hauro suka fara gurbata abin sannan aka yarda da mu.

WANNE KIRA ZA KA YI GA MAWAKA

Kira na shi ne mutum ya kare addininsa da al’adarsa saboda duk abinda ka ke yi ka san da akwai ranar da za a tambayeka.

Idon Gari na godiya.

Nima na gode.

Related Posts

Leave a Comment