Home APC A Yau MULKIN BUHARI YA MAIDA NIJERIYA BAYA

MULKIN BUHARI YA MAIDA NIJERIYA BAYA

by masta

An Soki Shugaba Buhari A Kan Shirin Ciwo Bashi

A lokacin da ya rage kwanaki ƙasa da ashirin shugaba Buhari ya sauka daga kujerar shugabancin ƙasar nan, amma shugaban yana neman ‘yan majalisa su amince masa da ya ciwo bashin dala miliyan ɗari takwas $800.

To sai dai wannan ƙudiri na shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na shan kakkausar suka daga wasu ‘yan ƙasar, inda suke ganin rashin dacewar hakan, musamman duba da cewa kwanaki kaɗan suka rage masa ya sauka daga mulkin ƙasar.

Shugaba Buhari dai ya bayyana dalilin ciwo bashin da cewa zai yi hakan ne don ragewa marasa galihu raɗaɗin rayuwar da suke ciki. Abinda ya jawo tofa albarkacin bakunan ‘yan ƙasa, inda suke ganin wannan ƙudiri na shugaba Buhari ba komai ba ne face ƙara jefa ƙasar nan cikin mawuyacin hali.

Shekaru takwas na mulkin shugaba Buhari, an ga yadda ‘yan Nijeriya suka shiga mawuyacin hali na ƙuncin rayuwa, wanda hakan ya haifar da komawa rayuwa mai tsada sakamakon ta sauƙi da ake yi kafin zuwansa.

A yayin da wakilin IDON GARI Nafiu Salisu yake zantawa da wasu daga cikin mutanen da suka faɗi ra’ayinsu a kan wannan ƙudiri na shugaba Buhari, wani wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyanawa wakilin namu cewa, “Mulkin Buhari dawo da Nijeriya baya yayi ba ciyar da ita gaba ba, domin kafin zuwansa talakan Nijeriya yana sayen babban buhun shinkafa ta ƙasar Thailand a kan kuɗi Naira 7,500 a yayin da katan ɗin taliya ake sayensa Naira 2,100 amma yanzu buhun shinkafa 36,000 katan ɗin tali ɗaya 7,400 ….”

Itama wata mata mai sana’ar kunu a kasuwa, ta bayyana cewa “Tunda take bata taɓa tunanin shiga ƙuncin rayuwa ba, amma a sanadin mulkin Buhari yau gashi ta tsinci kanta a titi tana talla, domin talauci ne ya jefata da yaranta ƙuncin rayuwa har ta kai ga sun fito kasuwa suna sana’ar kunu ita da yaranta mata..” Ta ƙara da cewa, “A da suna rayuwa cikin sauƙi lokacin kayan masarufi basu yi tsada ba, kuma suna biyan kuɗin hayar gida cikin sauƙi. Gashi maigidanta ya rasu ya barta da yara mata, hatta makaranta sai da ta gagare su zuwa domin abinda zasu ci ma da ƙyar suke samu..”

Jama’a da dama dai suna bayyana ra’ayoyinsu dangane da batun ciwo bashin dala milyan $800 da gwamnatin Buhari mai barin gado take neman ‘yan majalisa su sahale, al’amarin da al’umma kewa kallon ɓarna da rashin dacewarsa.

Suma wasu masana tattalin arzikin ƙasa sun soki wannan ƙudiri na shugaba Buhari, inda suka kira shirin da ƙara jefa wannan ƙasa cikin mawuyacin hali, duba da karyewar tattalin arzikin da ƙasar ke ciki.

Abin jira a gani dai shi ne, shin ko wannan shiri zai sami goyon bayan majalisa ko kuwa za suyi fatali dashi kamar yadda ‘yan ƙasa suke kiraye-kirayen a soke shirin?

Related Posts

Leave a Comment