Home Tarihi Wanene Bola Asiwaju Ahmed Tinubu?

Wanene Bola Asiwaju Ahmed Tinubu?

by masta

Daga Bashir Abdullahi El-bash

Sanatan Yankín Légas ta Yamma a shékarar 1993, Gwamnañ Jìhar Légas a shékarar 1999 zuwa 2007, zababben shugaban ƙasar Nageriya a 2023, basaraken gargajiya mai riƙe da sarautar Asiwaju na Jihar Legas, gami da sarautar Jagaban Borgu na masarautar Niger, Bola Ahmed Adekunle Tinubu, an haife shi a ranar 29 ga watan mayu, 1952 a Jihar Legas.

Alhaji Bola Tinubu ya yi karatun Firamare a makarantar (St. John’s Primary School) da ke Aroloya, a Jihar Legas, da kuma (Children’s Home School) a Jihar Ibadan. Bayan nan ya koma ƙasar Amerika a 1975 inda ya ɗora karatu a makarantar (Richard J. Daley College) da ke yankin Chicago da kuma Jami’ar Jihar Chicago ya karanci harkar alkinta kuɗaɗe, (Accounting) inda ya kammala a 1979.

Tinubu ya yi ayyuka da kamfanoni a ƙasar Amurka kamar kamfanin (Arthur Andersen, Deloitte, Haskins, & Sells, da GTE Services Corporation). Ya dawo Nageriya a 1983 ya shiga aiki da kamfanin mai na (Mobil Oil Nigeria) inda daga baya ya zama shugaban kamfanin gabaɗaya.

Tun a shekarar 1992, ya tsunduma harkokin siyasa a ƙarƙashin jam’iyyar SDP. Bayan gwagwarmaya da faɗi tashi cikin harkokin siyasar, Tinubu ya samu nasarar zama gwamnan Jihar Legas a shekarar 1999 a ƙarƙashin jam’iyyar AD. Inda kuma ya sake lashe zaɓe karo na biyu a shekarar 2003 tare da mataimakinsa, Femi Pedro inda su ka kammala a ranar 29 ga watan Mayu, 2007 inda Babatunde Fashola ya gaji mulkin wanda a lokacin gwamnatin Tinubu shi ne shugaban ma’aikata na fadar gwamnatin Jihar. Yanzu haka Tinubu shi ne zababben shugaban ƙasar Nageriya daga jam’iyyar APC a shekarar 2023.

Related Posts

Leave a Comment