Home Tarihi Rikicin Sadakar 3, 7 da 40 ga Mamaci Nazarin Tarihi

Rikicin Sadakar 3, 7 da 40 ga Mamaci Nazarin Tarihi

by masta

Daga Malam Fatihu Mustapha

A yan kwanakin nan, Malam Sheikh Farfesa Ibrahim Makari ya dauko wata tsohuwar rigima dadaddiya da aka taba yi a birnin Kano a shekarun 1930s tsakanin Malaman Madabo da daliban Malam Abdullahi Salga. Wannan rikici ya yamutsa hazo, ya kuma janyo cecekuce da dambarwa ta ruwan hujjoji a tsakanin manyan bangarorin ilmin guda biyu a Birnin Kano.

Da farko dai ya kamata a lura da cewa, dukkan su bangarorin biyu Tijjanawa ne, kuma Malaman Salga dalibai ne na Madabo, amma daga baya aka samu sabanin fahimta, hakan ya sanya babba malamin su, Malam Muhammadu Salga ya balle daga makarantar Madabo ya koma Koki ya kafa tasa makarantar, inda wani dalibin sa kuma attajiri ya bashi wuri domin ya cigaba da koyarwa. Rikicin dai ya cigaba da kamari, har ta kai aka zuga mutanen Koki, wasu suka yi wa Malam gorin unguwa, hakan ta sanya ya mayar da makarantar zuwa gidan sa da ke Gadar Salga.

Manyan daliban Malam Muhammadu Salga sun hada da, Malam Tijjani Usman Zangon Barebari, Malam Abdullahi Salga, Malam Sani Kafinga, da Malam Shehi Alkalansuwi. Wadannan sune daga baya ake kira da Arba’una Shuyuk (Shehunnai Hudu). Kuma sune kashin bayan kafuwar darikar Tijjaniya Insyasiya, sun kuma samu ilmin Sufanci ne a wurin Malam Mijinyawa Bakinruwa. Saboda, shi Malam Muhammadu ya shaida musu cewa, bai yi zurfi a ilmin sufanci ba, yafi karfi a ilmin fiqhu, lugga da hadisi. Don haka ya basu izinin su je wurin Malam Mijinyawa Bakinruwa su fara karatun tasawwuf. Da izinin Malam Mijinyawa ne suka sake karbar Darikar Tijjaniya a hannun Shehu Ibrahim Nyas, bayan sun gabatar masa da littafin Shehu Nyas me suna Kashful Ilbas. Sai dai Malam Mijinyawa ya tsufa a wannan lokacin, don haka bai samu ya gamu da Shehu Ibrahim ba. Su ma kuma basu gana da Shehu Ibrahim a farkon zuwan sa ba, sai daga baya, domin a lokacin ba su samu izinin Malamin su ba.

Mu koma kan batun rikicin zaman makoki da kuma sadakar 3, 7 da 40. An jima ana zaman doya da manja a tsakanin makarantun biyu, kowa na wa kowa kallon hadarin kaji, har wata kafa ta samu, da aka yi fito na fiton hujjoji a tsakanin malaman. A yayin da malaman Madabo ke yi wa na Salg kallon jaki, su kuma suna musu kallon dabaibayi. Su dai Malaman Salga sun zargi Malaman Madabo da kawo bidio’i a addini, ciki kuwa har da batun sadakar mamaci, a yayin da su kuma malaman Madabo ke kallon malaman Salga a matsayin jahilai kuma tsageru da ke wa malamam su tawaye.

Da farko dai daya daga cikin manyan daliban Malam Muhammadu Salga, wato Shehu Atiku ne ya fara fitar burtu da wata wakar sa ta larabci, ya bayyana cewa mafiya akasarin abinda malaman Madabo suka tafi akai ya saba da sunnah, ya kuma yi kira a gare su da su tuba su bar wannan hanya. Inda shi ma wani bajimin malamin na Madabo wato Malam Bako Sufi bai kasa a guiwa wurin mayar masa da martani ba, inda ya bi daya bayan daya na dukkan abinda Malam Atiku Sanka ya zarge su da su ya bashi amsa, a wani littafin sa da ya kira Hujja al Madabiwin. Anan ne ya bayyana dalilan sa na amincewa da yin sadakar mamaci da zaman makoki. Tun daga nan aka shata daga.

Wannan ya sanya su ma malaman Salga sun fike alkalumansu sun mayar da martani akan wannan matsaya ta su, dalilin da ya sanya yar sai da Malam Chindo ya sanya bakia cikin rigimar. Sai dai martanin da Shehu Atiku ya mayar masa bai dadi ba. Domin baya ga rusa dukkan hujjojin sa, ya ma zargi Shehin Malamin da rashin sanin dokokin luggar larabci.

Wannan hujjaceceniya dai ta shafe kusan sama da shekara ana bugawa, kuma dai daga karshe dai, haka kowa ya gama zube ban kwarya ta na hujjoji aka hakura aka bar kowa a matsayar sa. Wasu suka cigaba da sadakar mamaci musamman tsagin Madabo da kuma Qadirawa, wasu kuma suka bi bangaren Salgawa suka daina.

To amma meye alakar Malam Makari da wannan rigima? Kowa yasan dai Malam Makari dalibin Shehu Ibrahim Salih ne, shi kuma Shehu Ibrahim Salih dalibin Salgawa ne, ya yi karatu a wurin su. Wannan ya sanya ya tuna kowanne tsuntsu kukan gidan su yake. Shi kan sa malamin nasa, akan wannan fatawar yake har gobe. Dan haka ba abin mamaki bane, in Malam Ibrahim Makari shi ma ya zauna akan wannan fatawa.

Na yi wannan dan sharhi ne, saboda na lura wasu na zaton sabuwar magana ce, sam! Ko kadan ba haka bane, tsohuwar magana ce da aka fafata akan ta. Masana kuma sun jima suna sharhi akan ta.

Allah ya sa mu dace!

Related Posts

Leave a Comment