Home Daga Masarautunmu Tarihin Kofar Kwaya Katsina

Tarihin Kofar Kwaya Katsina

by masta

Tarihinmu Abin ALFAHARINMU

Daga

Bilkisu Yusuf Ali

Kofar Kwaya A Birnin Katsina

Kofa kwaya tarihi ya nuna cewa ta samo asali ne daga wani Basarake Bahaushe mai suna Sarkin kwaya, wanda ke mulki a wani gari da ake kira kwaya, da ke kudu da birnin jihar Katsina.

Aikin da yake yi wannan Basarake shi ne, sama wa Sarki hatsi, kamar irinsu su dawa da gero da sauransu, domin amfanin gidan Sarkin a wannan Zamani.

An ce, ta ita wannan kofar kwaya ce Wali Jodoma, wanda Sarkin Katsina na lokacin ya kora, ya bi ya fita ya bar Birnin katsina.

Tarihi ya nuna cewa, da shi wannan Waliyyin zai fita, sai ya juya da baya ya tsinewa kofar ya ce, “ba za a yi wani abin kirki a kofar ba, sai bayan karni guda.

Ga yadda Katsinawa ke cewa, kusan kowace kofa ta sami ci gaba Amma banda kofar kwaya.

To A Wannan Zamanin Da ta ke samun Ci Gaba Karnin Ne Ya Cika.

Ita wannan kofar, Ana Kautata zaton A karni na 15 ne aka gina ta.

Ita ce yanzun Zaka iya bi kaje Dutsinma, Runka, Kankara, Funtua Zariya, Kaduna, Abuja da Sauransu.

Saliadeen Sicey

Related Posts

Leave a Comment