Malam Fatihu Mustapha
Wani rubutu jiya na ga Auwal G Danbarno ya yi, inda yake kokawa akan yadda Ali Nuhu ya kai yayan sa makaranta suka yi karatu har suka kai matakin jami’a. Danbarno ya nuna hakan kamar wani wayo ne Ali Nuhu ya yi wa yayan mutane, musamman mata yan film da yake fitowa tare da su a film amma kuma ga yar sa ita bata film din tana jamia tana karatu. Daga karshe Auwal ya nuna cewa, yadda ya tiki rawa da yayan wasu a film, haka shi ma za a tiki rawa da nasa koda kuwa ba a film ba (bana son baiw maganar wata fassara).
Magana ta gaskiya, wannan batu na Danbarno da ya daura shi akan shahararren baudadden tunanin nan na bahaushe da yake cewa “in kayiwa dan wani kai ma sai an yiwa naka” ba daidai bane, ko dai a addinan ce ko a al’adance.
Domin kuwa, kowa dai ya san a addinance, Allah baya kama laifin wani da wani. Allah ba zai kama yaya da laifin uban su ba. Gara ma uba akan kama shi da laifin yayan sa, in har ta tabbata akwai sakacin sa wurin gurbacewar tarbiyar su. Amma Allah bai taba kama wani da laifin wani ba. Don baban mutum yana zina yana lalata yayan wasu, kuma sai Allah yasa shi ma a din ga zina da yayan sa, wannan ya saba da al’ada ta Ubangiji Subhanahu sa Ta’ala. Bai kama Ikramatu da laifin baban sa Abu Jahal ba, bai kama Khalid da laifin babansa Walidu dan Mughira ba (duk kuwa da malamai sun ce shi ne saboda tsanar da Allah ya yi masa, ko sunan sa baya fada a kur’ani, amma sai ga dan sa ya zama gwarzon yada addini. In har yayan Ali Nuhu sun tsare kan su sun bi Allah, to sun rabauta. In kuma sun lalace to dayan biyu, kodai bai musu tarbiya ba, ko kuma mabada hali ya riga mahori, wato ya samu yaya masu kunnen kashi. Amma bisa ga dukkan alamu, yayi iya kokarin sa ya baiwa yayan sa tarbiya daidai gwargwado, har sun kai munzalin da a yau kome suka yi, za a rubuta musu, in sharran in hairan.
Bisa ga al’ada a iya sanina da industri ta Kannywood, rayuwar mata na daya daga cikin kashi uku ne, kodai dama lalata ce ta kawo ta film, ko neman abin yi, ko kuma neman kudi. Da yawa matan da ake ganin sun lalace a Kannywood ni ina ganin dama lalatattu ne. Wasu kuma garin neman shuhra ko abin duniya ake lalata su. Iya kokarin mu na mu kare musu hakkin su, ya ci tura. Musamman saboda rashin hadin kan da muka nema daga wurin su a lokacin muna bibiyar harkar. Hakan ya sanya muka ce, kowa rai yayiwa dadi ba ya mai shi ba. An taba kafa wani kwamiti karkashin Farfesa Abdalla Uba Adamu, Malam Ibrahim Sheme Nasiru Wada Khalil da wasu da dama, wanda ni ne Sakatare na kwamitin, domin kawo gyara kuma an samar da wani kundi da zai kawo gyaran, wanda zai kare ba ma hakkin mata kawai ba, har ma da mazan. Amma abin bai nasara ba.
Mu koma batun Ali Nuhu, bana jin akwai yarinyar da ta zo industri ta ce Ali Nuhu ne ya ce ta zo ta fara film, kamar kowanne dan film, shi ma kiran sa ake a saka shi a film, in har ba shi ne ya kirkiri film din ba. Ba Ali Nuhu ke cewa a kawo masa yarinya ya yi rawa da ita a film ba, Darekta, da Furodusa da Scriptwriter su suke tsara abin, shi aikin sa kawai ya bi umarnin darakta a biya shi in ya gama. Ita kuma da ta amince ayi rawar da ita, ai da hankalin ta da wayon ta da ilmin ta daidai gwargwado, tana da zabin ko ta yadda tayi rawar ko ta ki, in ya so a nemo wata ta yi. A nan meye laifin Ali Nuhu? Sanaar sa yake, bai kuma taba tilastawa yar wani sai tayi rawa ba, in kin yi a biya ki kudin rawar, in kin ki a nemo wata tayi a biya ta. Kuma sai a ce laifi Ali Nuhu ne?
Mu dauka laifin sa ne, to kuma kawai don Ali Nuhu ya aikata laifi, sai a hukunta yayansa da basu ji ba, basu gani ba. Abin tambayar ma anan, shin a wurin Danbarno wanne ne mafi a’ala, yayan Ali Nuhu su zama mutane nagari, ko kuma su lalace kamar yadda kake kallon sa lalatacce. Ina zaton in yayan Ali Nuhu suka zama mutane nagari ai amfanin al’ummar mu ne.
Yayan makada da mawaka da dama a yau sun zama wasu hamshakai a kasar nan, dauki Murtala Dankwairo, kowa yasan arzikin sa yana amfanar da mutane kamar yadda aka hakaito a wata jarida. Yar zabiya Uwani Zakirai a yau lauya ce, dan Garba Liyo yau Injiniya ne, Jamila Shata Lauya ce dake aiki a EFCC. Shin wannan ba alheri ne ga al’ummar mu ba? Sai a ce ana fatan yayan wani su lalace saboda kawai ana zargin uban su lalatacce ne. Allah fa yana son bayin sa, kuma ya karrama su.
Ina fatan zaka janye wannan mummunan fata da kayi ga yayan wannan bawan Allah, ka kuma taimaka musu da adduar Allah ya zamar mu su jagora.
Ina maka fatan alheri, kai da iyalin ka.

