Home Mas'alolin Mata So kadai ba ya rike aure! A duba Maslaha shi ya fi dacewa

So kadai ba ya rike aure! A duba Maslaha shi ya fi dacewa

by masta

Daga Alkalamin Amina Yusuf Ali

Eh , so kadai ba ya iya rike aure
Barkanmu da sake Haduwa a wani makon!

Duk da dai Hausawa sun ce: “so Aljannar Duniya”. Haka kuma sun ce; “so gishirin rayuwa”. Sun ma Kara da so Hana ganin laifi To amma masu dabara, zaman lafiya da maslaha da dacewar halayya suka zaba. Matasa kada ku yaudaru da Wadannan kalamai. Duk kuwa da zaqinsu kamar zuma sabuwa! Ku bude idanu da kunnuwa ku kalli gabanku. Ku guje wa yin aure don so kawai. Idan ka zabi dacewar halayya da tsarin rayuwa sai ka ga bayan an yi aure, soyayyar ta ginu a hankali.
Ba a ce kada a yi auren soyayya ba, kuma ba a ce auren soyayya ba ya qarko ba. Amma a zahirance soyayya kacal ba ta iya riqe aure. Kuskure ne yin aure kawai don kuna son juna kadai. Domin soyayya kadai ba ta riqe aure. Duk da dai ita ce babban sinadarin da yake riqe aure, amma ba ta da danqon da za ta iya rike aure ba tare sauran wasu sinadaran ba.
Sinadarin farko shi ne dacewar halaye. Ya fi soyayyar ma muhimmanci a aure. Na san dai zai wuya a ce mutane biyu wato ma’aurata sun samu dacewa a dukkan halayyarsu a ce iri daya ce. Da ma ‘yanadamtaka ita ce banbanta a halaye. Kuma wani lokacin banbancin halayen ma yana kawo zaman lafiya. Misali idan miji mai haquri ne da mata mara haquri sai ka ga idan ta taso da fada shi zai kau da kai. Haka zai sa ta yi nadama ta gyara kuskurenta. Haka idan daya daga ma’aurata ba shi da ibada, daya yana da ita, sai ka ga dayan ya yi koyi da shi ko ita. Shi ya sa idan za a yi aure ake yi wa ma’aurata addu’ar Allah ya saba halaye.
Amma fa ba a koyaushe Sabawar halaye take zama alkhairi ba a zamantakewa. Wata sabawar halayyar fitina take zama. Misali, mace wacce ta saba da almubazzaranci idan ta hadu da miji mai tattali za ta sha wahala. Kuma ba za su taba zama lafiya ba. Haka kuma idan daya mai surutu ne, daya kuma shiru-shiru shi ma za a yi ta samun sabani . Ko mai zurfin ciki da wanda ba shi da shi. Haka dai. Don haka kada so ya sa a zabi abokin rayuwa ko abokiyar rayuwa wacce sam ba ku da kamanceceniya a halayenku.
Sannan kuma duk son da kake mata ko kike masa, kada ki sake ki aure shi in dai ba ki amince da amanarsa ba. Yarda da aminci na cikin jigon zamantakewa kowacce iri ce. Kuma ko kafin aure za ka iya gane wanda kuke tare da shi yana da amana ko akasin haka. Ko ta wajen qananan abubuwa kamar rashin cika alqawari. Misali yana kiranki lokacin da ya ce zai kira? Da sauransu. Wasu za su ga ai ba wani abu ba ne akwai mantuwa. Amma cika alqawari da riqe amana manyan shaidu ne da suke nuna cewa zai riqe ki amana ko bayan ya aure ki.
Haka kuma akwai tsarin rayuwa. Kowanne dan’adam da tsarin rayuwarsa. Duk son da ake wa juna idan tsarin rayuwa ya sha ban-ban haquri ya kamata a yi. Kada ki auri wanda tsarin rayuwarku bai dace da juna ba. Saboda kawai kina sonsa kuma kina fatan zai canza saboda ke. Ba a ce ba a canzawar ba, amma mawuyacin abu ne. Haka kai ma namiji kada ka auri wacce ba tsarinku xaya ba kuma ka dinga qoqarin sai ta canza qarfi da yaji. Gidan aure fa ba fagen daga ba ne. Wajen zaman lafiya da kwanciyar hankali ne. Tun fil azal, mance da so, samu wacce tsarinku ya zo daya , sai ka koya wa kanka sonta. Sai ka fi samun kwanciyar hankali.
Misali, Idan kai dan boko ne, kana son tafiyar da rayuwarka ta ‘yan boko, sai ka samo wacce za ta dace da wannan rayuwar ba wai wacce kake so kadai ba. Haka mace kina da burin ci gaba da karatu, kuma sai ki auri wanda ba ya da ra’ayin haka. Ko kuma mijin da bai son karatu ko aiki. Sai ya nace sai ya auri wacce yake so ko da ra’ayinsu ya sha ban-ban. Kuma idan ya yi qoqarin tanqwara ta da canza mata ra’ayi, sai hankali ya tashi zamantakewa ta qi dadi.
Haka namiji mai tsananin kishi, duk irin harbin da son ma’aikaciya ko ‘yar jami’a ko ma ‘yar kasuwa yake maka ka haqura. Saboda za ka sha wahala a zuciyarka na kishin matarka. Sannan kuma ga zunubin da za ka yi ta samar wa kanka na zarginta idan ta fita gudanar da harkokinta. Zaman lafiya ma ba a zancensa ya qaura a gidan, tuni.
Kuma sannan ya kamata a yi dogon tunani a kan wanda ko wacce ake so a aura. Shin za ka iya ko za ki iya rayuwa da wannan masoyin naku har muddin rayuwarku. Ku xauki shekaru arba’in gaba har i zuwa sittin. Abinda aka san ba za a iya ba, kada ma a soma.
Sannan kuma akwai kuskuren da ake yi game da sanin asalin wanda za a aura. Da kuma danginsu da sauransu. A lokacin da kake cikin mayen son mace wacce ka kwankwadj giyar qaunarta ka yi tatul, ka dinga tunawa fa ba wai aure ne kawai zai wanzu tsakanin kai da ita ba ne kawai. Zuriyya za a hada tsakanin gidanku da nasu. Sai ku lura ku yi hattara, kada so ya rufe ido a hada jini da baragurbin gida. Wannan ma haka yake ga mace. Kada idonki ya rufe ki afka soyayya da wanda iyayenki za su ce tir!
Bayan haka kuma, abin lurar shi ne, zuriyyar da za a samo a kowanne aure suna dibar wasu xabi’u na ko dai gidan uwarsu ko na ubansu. A wata majiya ma da ban tabbatar da sahihancinta ba ma na ji an ce, duk matar da ka aura, sai ta haifar maka irin mahaifinta sak! Wato a halayya da komai. Don haka sai a yi hattara matasa.
Har yanzu dai muna kan zancen dangi da asali. Kamar yadda na fada a sama, shi aure ba tsakaninka da ita kurum kuka qulla ba, har ma da danginku. Kada ku auro matar da za ta sha ban-ban ta kasa mu’amala da danginka. Ke ma kada ki auro wanda zai zama saniyar ware ga danginku. Ki auri mai mutunci wanda za a samu fahimtar juna da shi da danginku.
Sannan kuma a guji son uwar Inna. Wato a so iya macen ko mijin ba za a so mutanen da suke zagaye da rayuwarsu ba. Misali akwai matan da sun afka kogin son mai mata ko mai ‘ya’ya amma sun yarda za su so mijin amma ba za su tava yarda su so matansu ko ‘ya’yansu ba. Kun ga wannan shi ne aikin kawai xin kenan. Domin shi yana qaunar kayansa. Idan ya aure ki kika shiga muzguna musu fa ba za ku yi zaman lafiya da shi ba. Haka qimarki har abada raguwa take a zuciyarsa. Da haka, gara ki ajiye soyayyar a gefe, ki nemi mara mata ko yara shi ya fi dacewa da rayuwarki.
Haka idan namiji yana son mace kada idonsa ya rufe a kan ragowar al’amura da mutanen da suke kewaye da ita. Ya yi abinda zai iya zamar masa maslaha da kwanciyar hankali kawai.
Misali akwai namijin da zai so bazawara, kuma ya auro ta. Kafin ya aure ta, ya san ta taba aure, ya san wataqila ma tana da wasu yaran a wani gidan. To amma daga ya aure ta, sai hankalinsa ya dinga tashi da waxancan yaran da ta haifa a gidan wani. Ko idan tana kulawa da yaran ya dinga ganin ma kamar begen tsohon mijinta take yi ko kuma so take yi ta koma gidan tsohon mijin nata.
Yallabai, idan kai ka san haka kake, kuma ba za ka jure ba, tun asali ka nemi wadda za ka iya. Duk son da kake mata ko take maka ba zai sa ta rabu da yaranta saboda kai ba. Hasali ma ba za ta iya yi maka ko da rabin son da take yi wa yaranta ba. Wani lokacin ma sai ka ga miji ya fusata idan matarsa ta je ganin yaranta na wani gidan, ko kuma ya yi fushi idan sun ziyarce ta. Ita kuma ba za ta amince ka raba ta da yaranta ba. Daga nan sai a yi ta rigima zamantakewa ta qi dadi.
To da tun farko an bi maslaha ba so kadai ba, hakan ba za ta faru da su ba. Don haka maslaha da dacen hali ya kamata a duba. Domin so kadai ba ya kawo maslaha a zamantakewa. Shi ya sa matasa suka fi manya nadama a aure. Inda za ka ga su sun Fi ruduwa da yaudaruwa da maganar so, a kan manya. Manya sun fi duba maslaha sama da so. Hasali ma duba maslahar zamantakewa alama ce ta hankali ya fara ratsa saurayi ko budurwa masu shirin aure. Kuma ya kamata aure don kwanciyar hankali ake yi ba don a sha wahala ba. In dai ba za a samu kwanciyar hankali ba, to bari shi ya fi.

Mu hadu a mako na gaba

Related Posts

Leave a Comment