Daga
Nafi’u Mustapha Kaduna
Wasu iyayen yara a sun nuna fargabar komawar yaransu makarantar Firamari, bayan da wasu ‘yan bindiga suka ƙona wasu ajujuwa na makarantar.

Al’amarin ya faru ne a garin Kamfanin Doka da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna a ranar Lahadi, a yayin da majiyar IDON GARI ke zantawa da wasu daga cikin mazauna wannan gari da suka nemi a sakaya sunansu, sun bayyana cewa, “Da misalin ƙarfe huɗu na yammacin ranar Lahadi ne suna zaune sai suka ga wasu mutum biyu ɗauke da bindigogi a kan babur sun tunkari makarantar, jimawa kaɗan sai wasu babura uku (kowanne babur da goyon mutum biyu da makamai) sun ƙara nufar cikin makarantar, bayan waɗancan baburan guda biyu na farko.
Zuwansu ke da wuya (in ji mazauna garin) sai suka ga hayaƙi yana tashi. Jim kaɗan sai suka ga wuta ta kama rufin kwanon ajin makarantar tana ci banga-banga. Hakan yasa su leƙawa don ganin abinda ke faruwa, inda suka yi arba da ‘yan bindigar riƙe da makamansu, da wasu itatuwa riƙe a hannu sun kunna wuta. Wannan ne ya tabbatar musu da su ne suka kunna wutar.

Garin Kamfanin Doka na da nisan kilo mita goma sha biyar tsakaninsa da ƙaramar hukumar Birnin Gwari, kuma gari ne da ya ƙunshi yaruka kala-kala, Gwarawa, Inyamurai, Fulani da Hausawa. Gari ne da suke noma da kiwo sosai, sannan akwai babban daji da tsaunika da ƙoramu da suke kewaye da shi.
A shekarun baya dai, wannan gari na ɗaya daga cikin garuruwan da ‘yan bindiga suka addaba da yawan kai hare-hare a cikinsa. Baya ga ɗaukar mutanen gari tare da neman kuɗin fansa. Haka zalika sun sha tare mutane a lokacin da suke kan hanyar zuwa kasuwa ko gona su ɗauke su, inda wasu kan rasa rayukansu a hannun ‘yan bindigar.
Al’amarin yayi tsamari, har ta kai mazauna wannan gari na Kamfanin Doka sun shiga aikin sintiri da ake kira da (‘Yan sa kai) domin su tsare garinsu. Da rana su gudanar da harkokinsu, da dare kuma su ɗebi makamansu na gargajiya su hana idonsu barci har sai gari ya waye. Duk da haka mutanen wannan gari basu sami natsuwa ba, domin ta kai har wasu na yin hijira suna barin yankin zuwa Kaduna, Niger da dauran garuruwa.
Haka suka ci gaba da rayuwa har zuwa lokacin da suka yi yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninsu da ‘yan bindigar, a bisa sharaɗin za su biya wasu miliyoyin kuɗi. Bayan yi wannan sulhu ne mazauna wannan gari suka sami damar zuwa gonakinsu da Damina, da zuwa kasuwanni. To sai dai a yanzu haka garin ya kasance wurin dab-dalar waɗannan ‘yan bindiga, wanda sakamakon hakan wasu al’amura marasa daɗi suke ci gaba da faruwa na ƙwace da kisa da wasu daga cikin ‘yan bindigar suke yiwa mutanen wannan gari, duk kuwa da cewa manyansu suna yi musu kashedin taɓa duk wani ɗan garin da bai yi musu komai ba.
A yayin gudanar da bincike kan musabbabin ƙona waɗancan ajujuwa na makarantar Firamari kuwa, wata ma’ajiya ta bayyana mana cewa ‘yan bindigar sun sami labarin za a kawo jami’an tsaro na soji ne a cikin makarantar, shi yasa suka fara ƙona wani ɓangare na makarantar.

Shin ko iyayen yara zasu bar yaran nasu su koma makaranta idan an koma hutu?
Za mu ci gaba da bibiyar inda aka kwana, don haka sai mun sake haɗuwa a gaba.
Nafiu Salisu,
Daga Kaduna.

