Zababben shugaban kasa Alhaji Bola Ahmad Tinubu ya bayyana damuwa da jimami ga babban rashin gogaggen dan Siyasa kuma Jigo tsohon dan Siyasa abokin siyasarsa kuma jagora Alhaji Musa Gwadabe, Wanda ya rasu a yau laraba 26/4/2023 a jihar Kano. Alhaji Musa Gwadabe ya rasu yana da shekara 87.
Kafin rasuwarsa Alh Musa Gwadabe ya taba zama ministam kwadago da ayyukan yi sannan kuma ya taba zama sakataren gwamnati na jihar Kano. Kamar yadda sanarwar ta fita daga ofishin mataimaki ma musamman na Zababben shugaban kasa Abdul’aziz Abdul’aziz Alh Bola Ahmad Tinubu ya nuna cewa “ rasuwar Alh Musa Gwadabe ba karamin rashi ba ne, irin rashin nan ne da ba a iya misalta shi.
Mutum ne jajirtacce, nitsattse Wanda ya hidimtawa jam’iyyar APC jini da tsoka. Tinubu ya ci gaba da cewa Gwadabe mutum ne da ya yarda da siyasa ya san dukkan ka’idojinta Wanda muka jima muna gwagwarmaya tare, amintacce ne kwarai kuma tsayayye bango kuma matallafi, gaskiya na yi rashi kwarai da gaske.
A karshe Shugaban kasar ya yi addu’a ta neman gafara da ruhin mamacin sannan yana Mika ta’aziyya ga iyalan mamacin da ‘Yan’awa da abokan arziki da daukacin al’ummar jihar Kano bisa wannan babban rashin, Amin.”
Ofishin Zababben Shugaban kasa
Abdul’aziz Abdul’aziz
26 /4/2023


