Home Labarai DALILAN DA YA SA MUKA KAURACEWA DHIGA MASALLACI

DALILAN DA YA SA MUKA KAURACEWA DHIGA MASALLACI

by Bilkisu Yusuf Ali

Yadda Wasu Masallata a Kano Suka Bayyana Wasu Daga Cikin Dalilan Da Yasa Suke Ƙauracewa Harabar Masallaci Ranar Juma’a.Tsananin zafin ranar da ake yi a wannan lokaci, ya kan haifar da yawan shan kayan sanyi dangin su ruwa da lemuka.

Haka nan zafin yana sa mutane Æ™auracewa cikin rana zuwa inuwa duk Æ™anÆ™antarta.A É“angaren ibadu a masallatai (musamman ranar Juma’a), mutane kan nemi inuwa a cikin masallaci don Æ™auracewa zafin rana. Abin da kan sa wasu da dama Æ™in zuwa masallacin da wuri saboda zafin da ake yi a wannan lokaci.Sai dai duk da hakan, wasu kan yi haÆ™uri su zauna a cikin ranar duk da irin zafin da ranar take dashi.

Amma wasu kan yi amfani da lemar tare ruwa wajen yiwa kansu inuwa, yayinda wasu kan rufa Æ™yalle ko dardumar sallah a kansu duk domin tare zafin rana.Wasu suna ganin kamar ba daidai ba ne Æ™in zama a cikin ranar da wasu masallatan kan yi a yayinda ake jiran sallar Juma’a. Sai dai Malamai sun bayyana cewa yin hakan bai laifi ba ne, musamman ga waÉ—anda zafin ranar zai iya cutar da lafiyarsu.

Wasu mahalarta sallar Juma’a da muka zanta dasu a yau, a É—aya daga masallatan da muka ziyarta, sun bayyana mana dalilansu na Æ™auracewa harabar Masallaci.Sun ce; Suna Æ™aucewa harabar ne saboda zafin ranar da ake yi, kuma yawancin Limaman sukan yi doguwar huÉ—uba ba tare da yin la’akari da zafin ranar da ake Æ™wallawa ba.

Haka nan sun ce, idan mutum ya zauna a cikin rana ya kan jiƙe sharkaf da zufa, sannan idan kana so ka zauna cikin harabar Masallacin ba tare da zafi ya takura ka ba, to sai idan kana da lema, sannan kuma yawancin masallatan basu da bishiyoyi ko rufuna da zasu magance zafin rana.

To sai mu ce Allah Ya sassauta mana wannan zafin rana, ya kuma bamu ruwan sama mai albarka.

Related Posts

Leave a Comment