Malam Fatihu Mustapha
“Babban burin gwamnati shi ne, habaka masana’antu domin samar da aikin yi da farfado da tattalin arziki, bunkasa harkokin noma domin mu dogara da kan mu wurin samar da abinci, da kuma kyautata rayuwar mazauna karkara”
(Asiwaju Bola Ahmed Tinubu)
Babbar matsalar Arewa ba ta wuce yan siyasa ko kuma in ce jagororinta ba. Mafiya akasari masu wakiltar yankin a gwamnatin tarayya ba su ma san me ke damun arewa ba. Wannan ne ya sanya, sau da yawa haka ake kare gwamnatin yankin bai mori komai ba. Wannan ne ya sanya nayi marhabin da wani yunkuri da wasu dattawa dake jagorancin ACF suka yi a lokacin da aka bude damar kamfen na wannan zabe da ya gabata, irin su Dr Hakeem Baba-Ahmed, Maigirma Madakin Zazzau Alhaji Munir Jaafaru da su Maigirma Wazirin Katsina Alhaji Ibrahim Ida. A wannan tsari sun baiwa kowanne dan takara damar ya zo ya yi wa al’ummar arewa bayani akan me ya tanadarwa arewa. Kuma abin shaawa ba wanda ya yi maganat wane mukami za a baiwa arewa. Abinda ya dame su shi ne, me zaka yi wa Arewa, a fannin tsaro, ilmi, noma da tattalin arziki?
Mafi akasari manyan arewa abinda ya fi damun su in aka kafa gwamnati shi ne, wane mukami za a bani, ko kuma wane mukami aka baiwa arewa! Ba su cika damuwa da wadanne ayyuka aka kawo arewa ba. Wannan ya sanya a yayin da sauran abokan zaman mu ke cigaba, mu namu yankin kullum a ci baya yake. Kalli yadda igbo suka shafe shekaru suna neman wa zai musu 2nd Niger Bridge, har Allah yasa suka dace Shugaba Buhari ya zo ya yi ta. Kalli yadda Yarbawa suka gwangwaje a gwamnatin nan da titin Lagos zuwa Ibadan, da titin dogo na Lagos zuwa Ibadan, da ayyukan more rayuwa, a yayin da taron yan arewa a wannan gwamnati ya zama taron yu yu yu, taron tsintsiya ba shara. Mu ka shafe shekaru 8 muna mulki ba aikin Wutar Mambila, ba Tasha Jirgin Ruwa ta Baro, ba aikin farfado da kamfanin sarrrafa karfe na Ajakuta, ba aikin dogo na Kano zuwa Kaduna ko Kano zuwa Maradi, ba batun kawo karshe taaddancin Fulani a daji, ba, ba, ba…… Mu dai kawai a bamu mukami! Kaico!
To amma me yasa na kawo batun Shagari, Aminu Kano da Rimi a wannan magana? Saboda ina ganin abinda Kwankwaso ya ke kokarin yi, ya yi kama da abinda Malam Aminu Kano ya yi a zamanin Shagari, ya koma saba da yadda alaka ta kasance a tsakanin Gwamnatin Kano karkashin Gwamna Rimi da Gwamnatin Tarayya.
Akan hanyata daga Abuja zuwa Kano da azumin nan, na saurari hirar Malam Aminu da ya yi da wani dan jarida akan dalilan da suka sanya ya ki amincewa da ya hada kai da su Awolawo da Zik a yaki Gwamnatin Shagari. A wannan hira ya yi jawabi akan yadda ya baiwa yan majalisar PRP shawarar da su baiwa gwamnatin tarayya hadin kai, amma su ma su yi amfani da wannan dama, su shigar da bukatun jama’ar da suka turo su su wakilce su. Ta hanyar gabatar da kudurorin da za su amfani jihar su da al’ummar su. Domin kuwa su ma yan NPN za su marawa kudurorin su baya, tunda an samu fahimta mai kyau, sannan kuma shugaban kasa zai sanya hannu akan wadannan kudurori tunda shi ma yana bukatar su taimaka masa a yayin da yan adawa suke neman hana nasa kudurorin wuce wa.
Daga daya bangaren gwamna Rimi ya sha alwashin ganin bai bar NPN ta taka wata rawa a Kano ba. Hakan kuma ya rura wutar gaba a tsakanin gwamnatin ta Kano da ta Tarayya. Dalilin da ya sanya duk da manyan mukaman da aka baiwa yan Kano a gwamnatin Shagari, irin su Ministan Ilmi Bello Maitama, Mai baiwa shugaban kasa shawara a harkokin siyasa Malam Tanko Yakasai, Wakilin Nijeriya a Majalisar Dinkin Duniya Alhaji Maitama Sule, Manajan Darakta na NAFCON Alhaji Magaji Mohammed, Sakataren Kudi na NPN Alhaji Mansur Kankarofi da wasu ma mukaman, Kano bata mori wani abin ku zo ku gani a gwamnatin Shagari ba. In ka cire Kamfanin Fiat, da rukunin gidaje na Shagari Quarters bana jin zaka kara biyu.
Ina ganin Kwankwaso ya yi wa wannan tarihi kyakkyawar fahimta, don haka ya amince da hadin guiwa tsakanin party din sa da gwamnatin APC a matakin tarayya. Bana jin a yadda na san Kwankwaso zai yi wannan abin don neman mukami, ko dan yana son ya samu gurbi a jam’iyyar ta APC. Ina zaton Kwankwaso zai yi kokari ne ya ga Kano ta samu ayyukan cigaba a wannan gwamnati. Musamman ayyuka irin su:
1) Yashe madatsun ruwa na Kano, guda 13 (dam) domin habaka noman rani da samar da ayyuka yi. Wanda na tabbatar su kadai za su taimaka wurin samar da ayyuka ga sama da mutum miliyan 5 a Kano, su kuma samar da abinci ga kasar nan.
2) Aikin bututun gas da ya taso daga Kogi zuwa Kano. Wanda zai samar da wutar lantarki da za ta taimaka wurin farfado da masana’antun Kano da suka durkushe.
3) Karasa aikin dogo na Kano zuwa Ikko, wanda zai saukaka daukar kayan abinci daga Dawanau zuwa Lagos. Ya kuma habaka harkokin kasuwanci da bunkusa tattalin arzikin Kano da ma yankin Arewa baki daya.
4) Mayar da kasuwar Dawanau ta zama cibiyar harkokin kasuwancin amfanin gona ta duniya.
5) Bunkasa hanyoyin sufuri na ruwa, (inland waterways) wanda zai rage dogara da amfani da tituna.
6) Samar da tallafi mai tsoka ga manoman arewa da kuma inganta tsaro a dazukan mu.
7) Yaki da taadancin Fulani da ke addabar yankin Arewa Maso yamma.
8) Aikin Wuta na Mambila
9) Farfado da kamfanin sarrafa karafa na Ajakuta
10) Aikin Tashar jirgin ruwa ta Baro.
In har wadannan sune kudurin tsohon gwamnan, to muna maraba lale da wannan hadaka. Amma in dan rabon mukami ne, to ina ganin karshe dai mu tashi a tutar babu.
Allah ya taimaki wannan zumunta, ya kuma sa ta zama alheri gare mu da yankin mu da kuma kasar mu baki daya.

