WASAÙ DAGA CIKIN MANÚFÓFIN SABOŃ SHÙGABAN KASA MALAM ASIWAJU BÓLA AHMED TÌNÚBÚ AKAN NÀGERIÁ
DAGA: Bashir Abdullahi El-bash
“Za mu samar da megawat 15,000 na wutar lantarki a faɗin Nageriya, kuma za mu tabbatar da ɗorewarta tsawon awa 24 kowace rana a tsawon kwana bakwai”. Cewar Bola Tinubu.
Alhaji Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayyana manufofinsa akan tarayyar Nageriya wanda su ka sanya yanemi shugabancin ƙasar nan. Tinubu wanda ya ke da ƙwarewa a fannin shugabanci tayadda har ya yi gwamna sau biyu a babbar Jiha irin Legas, ya ba da tabbacin samar da zaman lafiya, inganta fannin lafiya da samarwa matasa ayyukan yi idan aka zaɓe shi.
Sannan kuma, Alhaji Asiwaju Bola Tinubu ya yi alƙawarin zamar da Nageriya ƙasar da kowane ɗan ƙasa zai mori arziƙinta ya kuma yi alfahari da ita tayadda duk Duniya ba za a rena ta ba.
Za mu farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasarmu, inda arziƙi zai yalwata kowa ya amfana batare da bambancin addini, matsayi, ko yare ba. Ƙasar da kowa zai samu tsaro, ya samu abinci da kiwon lafiya da muhallin kwana cikin aminci gami da ingantaccen ilimi a kowane mataki”.
“Za mu ɗaga darajar hanyoyin samun kuɗaɗen shiga tayadda ma’auninmu na lissafin kayayyakin cikin gida (GDP) zai na haɓaka cikin hanzari a kowace shekara gami da samarwa miliyoyin matasanmu ayyukan yi”. Inji Tinubu.
Asiwaju ya kuma ƙara da ba da tabbacin samar da tsarin ma’aikatun tattalin arziƙi na shiya-shiya waɗanda za su taimaka wajen inganta masana’antun shiyoyi da samar da ƙarin guraben ayyukan yi da inganta noma da kuma samar da tsare-tsare kan gine-gine na gidaje, tituna, da titunan jirage sama da ƙasa. ƙarƙashin tsarin “Build A New Nigeria” (BANN).
A ɓangaren wutar lantarki, Tinubu ya yi alƙawarin samar da wutar lantarki gami da raba megawat 15,000 a faɗin ƙasa gami da tabbatar da ɗorewarta tsawon awa 24 a kwana bakwai.
“Za mu kyautata tsarin hada-hadar man fetur, za mu samar da ma’adanar adana shi domin fitowa da ƴan ƙasa shi a duk lokacin da aka samu ƙarancinsa bazato-ba-tsammani”. Ya ce.
Haka zalika, Asiwaju ya yi alƙawarin kawo ƙarshen matsalar yawan yajin aikin malaman makaranta na jami’a, tare da alƙawarin cigaba da ciyar da miliyoyin yara ƴan firamare abinci kyauta, sannan ya kuma yi alƙawarin ƙara kuɗi a fannin lafiya tayadda mafiyawan ƴan ƙasa za su samu inshorar lafiya.


