YAKI YA KARA TSAMARI A SUDAN
Rikicikin kasar Sudan da a yanzu aka kwashe tsawon makwanni hudu ana gwabzawa ya sake daukar sabon salo. An dai fara wannan fada ne a ranar 15 ga watan Afrilu, a garuruwa da dama da ke kewayen Sudan, kasa ta uku mafi girma a Afrika ciki har da Khartoum babban birnin kasar.
A yanzu haka dai ana ci gaba da fafata fada mai tsanani da manyan makamai gami da jiragen saman yaki a birnin Khartoum fadar Gwamnatin kasar ta Sudan, a tsakanin Sojojin Sudan (SAF) da dakarun sa kai na Rapid Support Forces (RSF), kamar yadda mazauna birnin suka tabbatar.
Daga lokacin da aka fara wannan rikici zuwa yau, an hallaka mutane 700 yayin da wasu fiye da 5,500 suka jikkata bayan yin asarar dukiya mai tarin yawa, wanda hakan ya jawo karuwar ‘yan gudun hijira da suke ficewa daga yankin zuwa wasu sassa daban don tsira da rayukansu.
Rikicin Sudan da ke kara daukar zafi a yanzu, ya jawo tabarbarewar harkokin jinkai a cikin Khartoum babban birnin kasar ta Sudan.
Kasashen Turai da wasu na Africa ciki har da Nijeriya, suna ci gaba da kwaso ‘yan kasarsu don tabbatar da rikicin Sudan din bai ritsa da su ba.






