Rayuwar Sarki Sunusi ta bayyana misalai cikin tsarin zamantakewa , kuma daga baya wannan tsarin ne dai ya dore a salon shugabanci na masarautu daban-daban. Sarki Sunusi ya kyautata kuma ya inganta tsarin jagorancin al’umma. Mutum ne mai kima da martaba da tsoron Allah da Kankan da kai ana matuqar girmama shit un tasowarsa har zuwa rasuwarsa har kawo yau har abada a matsayin jagora.
TARIHINSA
Alhaji Sir Muhammadu Sunusi sarkin Kano na goma sha daya a jerin sarakunan Fulani kuma na hamsin da hudu a sarakunan Habe Wato dan sarkin Kano Abdullahi Bayero jikan sarkin Kano Muhammadu Abbas dan sarkin Kano Abdullahi maje- karofi dan sarkin Kano Dabo. An haife shi a cikin birnin Kano a wata unguwa da ake cewa Tudun wuzirci a shekarar 1905. Duk da a lokacin ba takamaimai shaidar ranar haihuwar amma an kamanta lokain haihuwarsa da bayan faduwar Kano a hannun ‘yan mulkin mallaka da shekara biyu. Don haka in aka waiwayi tarihi za a ga an haifi sarki Sunusi ne a lokacin mulkin kakansa sarkin Kano Muhammadu Abbas kuma lokacin ya yi dai-dai da shekarar 1905. Mahaifiyarsa ita ce mai babban daki Hajiya Hadiza ‘yar jakadan Garko Salisu Mainasara. Sir Sunusi shi ne da na farko kuma na qarshe a wajen mahaifiyarsa amma a gefen mahaifinsa akwai dan da ya fara haifa sannan Ado kuma Allah bai yi masa sahon rai ba don an ce bai kai shekara goma ba Allah ya karbi ransa. Don haka Sir Sunusi ya zama babban da namiji wajen sarkin Kano Abdullahi Bayero.
NEMAN ILIMINSA
Ya fara da makarantar allo tun da ya fara magana, tun yana tafiya qarqashin kulawar wadanda suka girme masa har ta kai yana tafiya shi kadai . Malamin da ya fara karantar da shi shi ne malam Abbas dan Badamagare wato mutumin Damagaran ne ta jamhuriyar Nijar. Sarkin Kano Muhammadu Abbas ne ya kawo shi Kano. Inda har Sir Sunusi ya sauke alqur’ani mai girma a hannunsa. An ce har sarkin Kano Sunusi ya girma bayan an nada shi sarautar Chiroman Kano idan suka fito kilisa shi da Baffaninsa sukan biya ta makarantar malam Abbas su yi masa jinjina daga kan doki shi ma kuma sai ya mike ya yi musu jinjina yana nuna musu bulalar dorina a hannunsa dukkansu sai su yi dariyar farin ciki. Bayan ya yi sauka ta farko ya ci gaba da karance-karancen a sauran fannoni na ilimin addini da bunqasa karatunsa na fannoni da ci gaba da qu’anin har Damagaran ya je don jaddada saukarsa da bunqasa fannonin ilimi. Daga cikin malamansa akwai malam Ahamadu Abbasi (wanda daga baya saboda kyawawan xabi’un sarki Muhammadu Sunusi har ya aurar masa da ‘yarsa mai suna Aishatu wacce aka fi sani da yayar Goshi kuma Allah ya albarkaci wannan aure da zuri’a. Ita ce ta haifar masa dansa na biyu wato Wamban Kano Abubakar) sannan akwai alqalin Bichi Malam Mustapha da Danmakwayon Kano malam Yusufu da sauransu.
Sarki Sunusi ta fannin boko ko da yake bai halarci makaranta ta musaman ba to amma kuma bai yarda ya tsaya a baya ba wajen tafiya da zamani ba, ya rungume shi hannu bibbiyu. Ya fara da koyon rubutu da karatun Hausa , sannu a hankula har yake hada wa da Turanci a haka har ya kai yana jin Turanci. Saboda sha’awarsa har ta kai sai da aka daukio masa gogaggun ‘yan kwalejin Katsina (waxanda suka kware) suka koya masa Turanci. Wadanda suka hada da malam Barau Danbatta da malam Sule Oktoba da chiroman HADEJA Sambo. Daga baya kuma ya yi bita tare da malam Maikano Dutse da Inuwa Wada. Sannan ya qara inganta turancinsa ta tattaunawa da su malam Bello Kano da malam Bello Dandago da Abubakar Dokaji.
DABI’UN SARKI SUNUSI
Mutum ne haziqi mai kulawa da ibada ainun. Karimi ne matuqa. Sannan mutum ne mai taimakon jama’a gaya.Mai biyayya ne matuqa da juriya da amana wannan ta sa mahaifinsa a lokacin yana hakimcin Bichi Chiroman Kano ya nada Sarki Sunusi a matsayin magatakardarsa wato malamin hakimi. Wanda wannan muqami ba a ba wa mutum shi sai an tabbatar da amanarsa. An shaide shi da biyayya kwarai inda kusan ko da yaushe yana gefen mahaifinsa yana yi masa hidima.
Mutum ne mai zumunci don kuwa an shaida yadda ya riqe ‘yan’uwan mahaifinsa matuqar kulawa.
SARAUTAR DA YA RIKE
An yi wa sarki Sunusi sarautar Chiroman Kano bayan mahaifinsa Abdullahi Bayero ya zama sarkin Kano sai ya maye gurbin da ya bari. A lokacin da aka yi masa sarautar Chiroma bai fi dan shekara ishirin da daya ba. Sannan aka nada shi hakimcin Bichi. An kais hi Bichi a shekarar 1926 ba a dawo da shi Kano ba har sai a shekarar 1947 lokacin da aka dawo da shi cikin birni don kulawa da sha’anin hakimai da gundumomi.
A shekarar 1947 jikin madakin Kano Mamuda ya yi tsanani sai aka sauko shi daga Bichi aka Dora masa nauyin kulawa da aikin gudanarwa na gundumomi masarautar Kano.
Sarkin Kano Abdullahi Bayero ya rasu a 1953 kashegari ranar Juma’a Razdan din Kano ya Mika wa masu zabe sarki sharuddan da za a yi la’akari da su wajen zabe sarki. Bayan duba cancanta masu zaven sarki suka miqawa Razdan sunan sarki Sunusi shi kuma ya miqawa gwamnan arewa na wancan lokaci , Sir Buyn Sharwood Smith don amincewa. Bayan amincewar Razdan din Kano Mr A.T. Weatherhead ya gudanar da Nadin ranar 1 ga watan Janairu na shekarar 1954 da qarfe tara na safe. An yi bikin rantsar da shi a matsayin sarki ranar asabar 19 ga watan Yuni 1954 a matsayin sarki Kano na goma sha daya a jerin sarakunan Fulani. Gwamnan arewa ne ya gudanar da bikin a filin wasa na hauren qofar mata a cikin birnin Kano
AYYUKAN DA YA YI NA HIDIMAR AL’UMMA
Yana Ciroma hakimin Bichi ya assasa tafsiri da ake yi da azimi a gidansa kuma har bayan ya dawo birni ba a daina ba. Sai kuma aka ci gaba da gabatar da shi a gidansa na Ciranci.
Tun yana hakimci a Bichi yake lallasa Barayi da bata gari. Idan aka kawo masa labarin ‘yan caca da kansa yake fita shi da yaransa don kame.
A lokacin da Sarki Sunusi yake ciroma ya shiga sojan sa kai bisa umarnin mahaifinsa don kyautata tsaro
A lokacin da guguwar siyasa ta tashi aka fara shirye-shiryen zabe a shekarar 1947 ciroma na daya daga cikin mutanen da aka zaba don wakiltar Kano a majalisar wakilai ta arewa. A shekarar 1952 sai aka ba shi muqamin minister mai bayar da shawara akan sha’anin addini musamman a aikin hajji shi ne mutum na farko a arewa wanda ya riqe irin wannan muqami duk kuwa da cewa shi ba dan boko ba ne. Kamar yadda Parden ya fada a littafinsa mai suna Ahadu Bello ya ce lokacin da ake kakkafa jam’iyyun siyasa Sir Sunusi yana da qarfi kwarai ya taka rawarr gani wajen janyo matasa ‘yan boko cikin siyasa ire-irensu sun hada da Inuwa Wada da Maitama Sule da Sule Gaya da sauransu.
Shi ya qarfafa dangantaka tsakanin masarautar Kano da ‘yan Kasuwar Kano.
Shi ne qashin bayan shigar ‘yan kasuwar Kano cikin siyasar arewa. Kuma akasarinsu suka zama magoya bayan sardauna. Daga cikinsu Akwai irinsu Haruna Kasim da Isyaka Rabi’u da Ahamadu Dantata da Alhaji Nabegu.
Sir Muhammadu Sunusi mashahuri ne ta fannin addini. A ko da yaushe aka ambaci zamanin mulkinsa abin da za a fara tunani shi ne ibada da kuma tsayar da shari’a. Ya yi matuqar qoqari wajen ganin cewa ya zama shugaba abin koyi wajen gudanar da ibada da kuma ganin an bi qa’idojin shari’a yadda ya kamata.
AYYUKANSA BAYAN YA ZAMA SARKIN KANO
Abin da ya shafi Addini
Tunda Sir Sunusi ya zama sarkin Kano har zuwa lokacin da wa’adinsa ya cika na sauka shi ne yake limancin juma’a. Wannan ba qaramin kwarin gwiwa ya qara wa jama’arsa ba. An ce har yakan yi kuka yayin karanta huduba . An ce wata rana shugaban makarantar koyon shari’a ta Kano Sheikh Awad ya ce “in har saboda tsoron Allah sarki yake yin kukan da ya yake yi a huxubarsa , to kuwa yana da wuya ya mutu a kan gadon sarauta”Allahu Akbar hasashen Sheikh Awad ya tabbata. Shi yake yin sallar idi musamman qaramar sallah saboda yawanci babbar sallah yana zuwa aikin hajji. Kuma yakan yi huduba mai jan hankali da fadakarwa ga al’umma.
Bayan ya zama sarkin Kano ya ci gaba da gudanar da tafsirin al-qur’ani a fadar Kano duk azimi tafsirin da har yau ana gabatar da shi wanda shi ne ya assasa shi. A lokacin da ya zama sarki sai ya sa malam Nasiru Kabara yake yin tafsirin.
Shi ne sarkin da ya riqe muqaddashin gwamnan arewa kafin wannan lokacin riqon kwarya ba a tava jin kiran sallah a gidan gwamnati ba. Amma daga hawa kan wannan muqami sai ya yi umarni da a riqa yin sallah a gidan gwamna.
A lokacin da ya yi sarauta kusan sarakai suna cikin al’amuran siyasa. To a lokacin shi ne ministan kula da al’amuran alhazai. A wannan matsayi nasa ya taimaka matuqa wajen taimakon alhazai tun daga tashinsu daga Najeriyar har ya zuwa dawowarsu daga qasa mai tsarki. A lokacin ne Kano ta zama cibiyar zirga-zirga da jigilar alhazai. Kusan duk alhazan yankin arewa Kano ce matattararsu. Wannan ya dada Habaka tattalin arziqin qasar Kano saboda shigowar baqi.
Sir Sunusi mutum ne mai tausayi a lokacin sarautarsa yana sa a Dinka kayan sawa da yawa duk sati bayan an idar da sallar juma’a sai ya sa fadawansa su dudduba wasu daga cikin wadanda suka zo masallaci marassa suturar qwarai sai a dauko kayan nan da aka dinka a rarraba musu sadaka.
Tsaro
A batun tsaro kuwa sarki Sunusi ya yi matuqar qoqari na yaqar munanan laifuka kamar caca da shan giya da sace-sace da sauran laifuka wadanda suka janyo aikata manyan laifukan da kan haddasa rashin tsaro. A lokacinsa an ce barayi ba su da sakat sai da ta kai saboda tsaurarawa da yake yi wa Barayi da yake yi sai da ta kai kusan duk barayin Kano sun tsere zuwa Makwabta . Idan aka kama barawo za a kai shi gidan yari kafin ya gama wa’adin da aka zebar masa za a tarar ya yi karatun ta nutsu da ya fito shikenan ya yi bankwana da sata. Duk inda aka ji labarin gawurtaccen varawo a qasar Kano sai ya sa sa an je an kamo shi don raba jama’a da alaqaqai.
Kasuwanci
Sarki ne da ya yi matuqar qoqari kan Habaka kasuwanci a qasar Kano misali akwai wata unguwa Malafa a cikin birnin Kano ita wannan unguwa duk kududdufi ce mutane ba sa iya zama a wajen amma da ya zama sarki sai ya saka aka cike ta ya mayar da ita fegi kuma ya rarrabawa talakawa.
Haka kuma a kasuwar Kurmi akwai gefen ‘Yan tabarma anan aka yi wa mahauta gini na zamani su kuma mazauna nan aka mayar da su ‘Yan awaki aka ba su wani matsugunni aka biya su diyya kuma aka gina musu makarantar firamare ta ‘Yan awaki.
Sir Sunusi bayan ya hau karagar mulki sai da ya je kasuwar sabon gari ya yi waxanda galibinsu ciniki ne ya kawo su Kano mutanen kudanci da yammacin qasar nan ne) ya kai musu ziyara ta musamman ne don neman goyon bayansu game da taimakawa ga sha’anin tattalin arziqin Kano game da saye da siyarwa. Inda y aba su goyo su kuma su tabbatar sun yi komai da amana.
A zamaninsa adada titina musaman na Mandawari zuwa titin masallacin juma’a da Goron Dutse ya bi ta gadon gaya Goron Dutse ya zarce har Gwammaja ya bullo qofar ruwa ta Katsina Road ya bi murtala Muhammad Way. A zamaninsa ne saboda a rage cunkoso a cikin gari aka raba fegin Mainagge sarkin shanu Sani. Mahaifin madaki Abdullahi ne ya raba filin.
Ta fannin masana’antu da ciniki a lokacinsa unguwar masana’antu ta cika ta batse ta Bompai. Har ya yi tunanin a fadada ta a wannan lokacin ne aka yi tunanin kafa unguwar Sharada Industrial area.
Shi ne ya qirqiro bikin cikar Kano shekara dubu festival of Kano. Ya shirya qayataccen biki aka gayyaci duk gwamnaoni na yankunan Kudu da na yamma da firimiyoyi da sarakunan gargajiya ba a taba yin qayataccen biki irinsa ba.
Walwala da Motsa jiki
A zamaninsa ya bawa matasa dama. A da ba’a cika bawa matasa dama a wajen mulkin jama’a sai dai tsofaffi. Amma da ya zama sarki duk inda yaji labarin matashi mai hazaka zai yi kokari ya ga an janyoshi an yi tafiya da shi. Don haka, lokacin siyasar NPC ya ja matasa da dama daga Bagar Ori daban -daban ya shigar da su cikin lamuran jama’a. Misali, akwai ‘yan boko ‘yan kasuwa, malamai da sauransu. Daga cikin irinsu akwai irin su Maitama Sule da Magajin gari Inuwa Wada da sauransu. Irin su Bello Kano, Bello Dandago duk shi ne ya sa su a siyasa. kwalliya kuwa ta biya kuxin sabulu domin a lokacin ba inda aka kai Kano gogaggun ‘yan siyasa.
Hatta a wasannin motsa jiki ba a bar Kano a baya ba lokacin sarkin Kano Sunusi. Duk abin da ya zo Kano ba ya bari Kano ta zama a baya ba kuma komai sai ya haxa da roqan Allah. Don haka hatta a kwallon kafa sai hada da roqon Allah don a yi nasara.
Adalci
Sarki Sir Muhammadu Sunusi ya yi qoqarin ganin ya yi adalci a shari’un da yake gudanarwa . Kafin zamansa sarki ba a ba wa mata gadon gida ko gona. Amma da ya zamo sarki saboda tabbabatr da adalci idan mace ta cancanci gida ko gona sai a ba ta kayanta duka. Wannan doka ita ce ake gudanarwa a rabon gado har zuwa yau.
Saboda adalcinsa idan aka kawo shari’a gun sa nan take yake yanke hukunci a ya bari a jinkirta sai dai in shari’ar mai buqatar dogon lokaci ce.
Ilimi
Ilimi fitilar rayuwa. Sarki Sunusi ya tsaya tsayin daka kan qarfafa al’umma kan batun ilimi. A zamaninsa ya gina makarantar firamare a gurare daban-daban misali a shekarar 1960 aka bude makarantar boko matakin firamare har uku a cikin birnin Kano kuma a rana daya.
Noma da Raya Karkara
A vangaren noma da raya karkarasa sarki Muhammadu Sunusi ya yi qoqari kwarai wajen bunqasa su a lokacinsa an ba wa manoma ingantaccen irin shinkafa da auduga da rogo da gyaxa don bunqasa tattalin arziqin qasa. Saboda son sa da fadada noma da kuma yi wa al’umma nuni da su riqi noma a kullum ya tashi daga zaman fada bayan la’asar yakan tafi gandu. Yana da manyan ganndaye a Joda da Durumin shura. Shi ya fara kawo irin tuffa Kano inda aka gwada a gonarsa duk da ba a dace ta yi ba.
Kiwon Lafiya
A qoqarinsa na inganta kiwon lafiya a lokacinsa aka bude makarantar koyon aikin tsafta a shekarar 1956 School of hygiene. A shekarar 1959 da qoqarinsa da kuma na majalisarsa gwamnatin jahar Arewa ta bude asibitin qashi na Dala . Sannan aka bude qananan dakiunan shan magani na qauyukan Rimin gado da Shanono da Ungoggo da Ajingi duk a shekarar 1960
Alaqar Sir Muhammadu Sunusi da Sir Ahmadu Bello (Sardaunan Sakkwato)
Alaqar Sir Sunusi da sardaunan Sakkwato ta samo ne tun daga kakanninsu. Kamar yadda aka gani suna da alaqa da auratayya a tsakaninsu Sarkin Kano Alu ta gefen mahaifiyarsa jika ne ga sarkin Musulmi Aliyu Babba. Lokacin da Sir Sunusi yana Ciroma shi kuma Sir Ahmadu Bello yana Sardauna sun taba samun sabani da sarkin musulmi har rigima ta tsananta har sai da ta kai an tsare sardauna. Sai Ciroma shi da iyan Zazzau Aminu kafin ya zama sarkin Zazzau suka dau lauya suka daukaka Kara . Allah ya kuma ba su nasara. To tun daga wannan lokacin dangantaka tsakaninsu ta dinga qara qarfi. Lokacin da aka kafa jam’iyyar N.P.C kuma a lokacin Turawa na shirin hada komatsansu su ba da mulkin kai tare suka dinga fadi tashi. Sun yi aure-aure a tsakaninsu da tsakanin ‘ya’yansu kuma da zuriya da dama a tsakani. Alaqarsu ta yi nisa kwarai har ta kai ko sutura daya ya yi sai ya yi ma daya . Haka tafiye-tafiye tare suke yin su sannan daya ba ya gabatar da wani abu ba tare da ya nemi shawarar xaya ba.
Duk wannan kyakkyawar alaqar bai hana mahassada su shiga tsakani ba inda abu ya qi dadi har ta kai gwamnatin Arewa ta yanke shawarar kafa hukumar bincike game da N.A ta Kano. Wanda wanan bincike ne ya janyo sanadin barin sarautar Sir Muhammadu Sunusi. Lokacin da gwamnatin jahar Arewa ta qudurci niyyar sauke sarki Sunusi sai ta kafa hukumar bincike qarqashin Mr David Muffet wani Baturen qasar Ingila babban ma’aikaci a ofishin firimiyar jahar Arewa . A ranar 18 ga watan Satumba shekarar 1962 gwamnatin jahar Arewa ta kafa hukumar binciken N.A a Kano. Wannan hukuma ta zauna kimanin kwana dari da arba’in da hudu tana gudanar da bincike kan sarki da wasu ma’aikatan N.A ta Kano. An ta kai tsegume-tsegume tsakanin Razdan da Sardauna wanda hakan ya susuta alaqar. Sannan wani dalilin da kuma ya janyo wannan sabanin an ce Sarkin Kano Sunusi ya cika tsauri wajen gudanar da shari’a. Irin Shari’ar nan da yake gudanarwa ta yin haddi ga mai shan giya wai ta yi tsauri.
Sarki Kano Sunusi sarki na goma sha xaya a daular Fulani Alhaji Sir Sunusi ya yi murabus ranar 28 ga watan maris 1963 bayan sun yi wata ‘yar ganawa da Sir Kashim Ibrahim a Kaduna. Kasshim ya yi wa sarki Sunusi bayanin irin qudirin da manufofin arewa na kawo sauye-sauye a N.A Kano, kuma ya nuna buqatar da suke yi ta ya sauka daga sarauta. Amma sai ya nemi ra’ayinsa da cewa ko ya yarda. Nan take ya sa alqalami ya rubuta daga ranar ya bar sarautar Kano. An ce shi kansa sir Kasshim din ya yi mamaki irin jarumtarsa. Da hannunsa ya bar sarautar Kano don haka har sai da suka yi barkwanci na tsakanin Fulani da Barebari. Shi da bakinsa Sir Sunusi a wata hirar da ya yi da wakilin mujallar new era a watan Mayu na shekarar 1971 inda yake cewa “komai nawa yana hannun Allah saboda shi yake zaba mani abin da ya fi mani alheri a idonsa shi yake zaba min mafi kyau a ko da yaushe. Shi yasa ba ni da
Zabi na kaina.
Bayan labari ya iso Kano, jama’ar Kano sun Kadu sosai bisa jin labarin murabus din sarki wannan lamari ya sa jam’iyyar N.P.C ta shiga wani hali na ha’ula’I qusoshinta na can tarayya waxanda ke zaune a Ikko irinsu Tavawa Balewa da Ribadu da Inuwa Wada da Yusuf Maitama Sule na ganin wannan lamari bai dace ba su kuma qusoshin da ke zaune a Kaduna irin su Gashash da Sardauna da Sule Gaya su kuma suna ganin abin da aka yi ya dace.
Bayan Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi ya yi murabus sai ya koma azare da zama. Idan wani sarki ya yi murabus ba ya zama masarautarsa gudun husuma sai dai ya koma wata masarautar. Wannan ya sa lokacin a sarki Alhaji Muhammadu Sunusi ya yi murabus shi ma an yi ta kai kawo kafin a yi matsayar inda zai koma. Inda Lokacin da ya yi murabus ya so ya koma Madina ne da zama amma sai gwamnatin jahar Arewa ta qi yarda. A lokacin da sarakunan da aka nemi a kai musu shi sai su e a’a sai sarkin Katagun na wannan lokain ne ya ce ya amince a kai masa shi don bayan dangantakar sarauta akwai dangantakar auratayya. Duk wannan abun da ake yi shi Sir Sunusi yana Kaduna, iyalinsa kuma na Kano. Azare kuma ana can ana gyara masa inda zai zauna. Gwamnati ta bayar xan qaramin jirgi aka xauko shi da shi da xan’uwansa Turaki Salihi da dansa Xan’iya Ado da babbanDanmorinsa Saje Alhaji Agaisa aka kai su Azare a shekarar 1963. Wannan shi ne ya kuma bude masa wani sabon shafi na rayuwarsa.
HALIFANCIN SIR MUHAMMADU SUNUSI NA 1
Sarkin Kano Murabus Sir Muhammadu Sunusi ya zamo halifan Shehi Ibrahim Nyass ne lokacin da ya koma azare. Malam Dahiru Usman Bauchi ya je hajji sai suka Hadu da Shehu Ibrahim Nyass suka yi maganar sarki Sunusi sannan sai Shehi Ibrahim da Shehi Dahiru Bauchi in ya dawo gida ya je ya samu Sarki Sunusi ya fada masa ya nada shi halifansa. Tun daga wannan lokacin sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya ci gaba da sha’anin tarbiyyar jama’a bisa darikar Tijjaniya gadan-gadan ba dare ba rana. Tun daga wannan lokaci mutane daga kowacce nahiya ta qasar nan har da ma makwabtanta kullum sai tururuwa suke yi suna zuwa su ziyarce shi a Azare.Idan suka zo ziyara suna gudanar da zikirorinsu da sauran ibadu. Adamawa har da mutayensu suke zuwa inda matayensu suke shiga cikin gida wajen iyalan Halifan suma suna gudanar da nasu zikirin. Haka ma makwabtan Najeriya kamar Nijar da Chadi da Ghana da Mali da Burkina da sauransu duk suna kan hanya kowanne lokaci don sa ziyartar Halifa. Haka ya ci gaba da gudanar da rayuwarsa wajen ibada iya tsahon zamansa a Azare.
Alaqar Sarkin Kano Muhammadu Sunusi da Shehu Ibrahim Nyass
Alaqar Sarkin Kano Sunusi da Shehu Ibrahim Nyass ta kullu ne tun zamanin mulkin sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero a cikin shekarar 1937. Lokacin da shehu Ibrahim din ya ziyarci Kano bayan ya dawo daga aikin Hajji . Sannan Shehu Ibrahim ya kuma zuwa Kano ya kawo ziyara a shekarar 1944 da shekara ma ta kewayo ya kuma zuwa. Duk wannan ziyarar da Shehu yake zuwa Ciroma ne babban jakada tsakaninsu da sarkin Kano. Daga saukar Shehu da tashin duk hidimarsa Ciroma ne yake kula da ita. Wannan ya janyo shaquwarsa kuma ya qarfafawa Ciroma aqidarsa ta xariqar Tijjaniya. Bayan Ciroma ya zama sarkin Kano sai dangantakarsu ta qara qarfafa tsakaninsu da shehu Ibrahim sai da ta kai duk shekara idan Shehu zai tafi aikin Hajji tare suke tafiya da sarki Sunusi kusan tun daga shekarar 1952 har zuwa shekarar 1962. Akwai zuwan da ya yi Kano lokacin Halifa na sarautar Kano wani azimi har ya xan yi tafsiri kafin ya koma gida.
Dawowa Wudil
Gidan da Halifa ya zauna a Wudil ainahinsa sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero ne ya gina shi tun a cikin 1929 ya zabi wajen da za a gina wannan fada. Amma ba a fara aikin ba sai a cikin shekarar 1938 an kammala ginin gidan a shekarar 1939. Bayan da Alhaji Muhammadu Sunusi ya ci sarautar Kano a 1953 sai ya sake yi wa gidan kwaskwarima tare da karin gidajen dogarai da na ‘yan’sanda saboda tsaro.
A shekarar 1978-1979 daya daga cikin alqawuran da Alhaji Abubakar Rimi ya yi lokacin yaqin neman zabensa na siyasa shi ne idan ya hau mulki shi ne dawo da sarkin Kano Sunusi Kano. Shi ya zabi komawa Wudil saboda ba ta da nisa da Kano kuma ya saba da ita tun yana sarautar Kano yana zuwa har yakan yi wata guda a can da iyalansa da barorinsa da fadawa. Ya sami gagarumar tarba a lokain da ya koma Wudil tun daga Kan Gwamna na lokacin Alhaji Abubakar Rimi da shugaban Jam’iyyar PRP malam Aminu Kano da da malamai musamman na darikar Tijjaniyya da sauransu.
Ko a Wudil dorawa ya yi kan hidima da ya saba ta addinin muslunci da ibada da karbar baki da bayar da karatu. Duk ranar litinin da Juma’a ana yin dafifi cikin qauna da soyayyar juna.
GUDUMMAWAR HALIFA SUNUSI 1 GA DARIKAR TIJJANIYYA
Gudummawar da Halifa Sunusi ya bayar a xariqar Tijjaniya ba za ta misaltu ba ya hada zumunta da qauna ya bayar da ilimi da soyayya don Allah. Ya haifar da auratayya kwarai da gaske musaman tsakanin mutanen Azare da Kano.
Rasuwarsa
A ranar juma’a 21 ga watan Ramadan ta shekarar hijra 1411 wanda ya yi dai-dai da 5 ga watan Afrilu 1991 Allah ya amshi rayuwar Halifa Sunusi. Bayan an yi masa sutura sai aka dauke shi daga Wudil aka tafi da shi Kofar Kudu. Daga nan aka kai shi gidan Nassarawa aka binne shi. Tun kafin ya rasu yana lafiya ya nuna sha’awarsa kan in Allah ya yi masa cikawa a yi masa kabari a bayan mahaifinsa sarki Kano Abdullahi Bayero. Allah ya yi masa gafara ya sanyaya makwancinsa Amin.
An ciro wannan bayani ne littafi mai suna Sir Muhammadu Sunusi wanda Ruqayya B. Makama ta wallafa.


