Home Labarai YADDA KWACEN WAYA A CIKIN AADAIDATA SAHU YA CANZA SALO

YADDA KWACEN WAYA A CIKIN AADAIDATA SAHU YA CANZA SALO

by masta

Yadda Wani Mutum Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Al’amarin sata da ƙwacen waya a cikin garin Kano, al’amari ne da ya daɗe yana ciwa al’umma tuwo a ƙwarya, wanda kuma jami’an tsaro suke yaƙi da masu aikata hakan.

To sai dai duk da ikirarin da jami’an tsaron ke yi na cin galaba a kan masu aikatan ƙwacen wayoyin jama’a, amma al’amarin sai ƙaruwa yake a cikin garin Kano, tare da sauya salon sata da ƙwacen wayardaga hannun jama’a.

A zuwa yanzu dai, wannan lamari yasa wasu daga cikin masu amfani da manyan wayoyi shiga cikin fargaba, ta yadda dole idan suka shiga wasu wuraren sai dai su ɓoye wayoyinsu don gudun kada a ƙwace musu, inda wasu kuma suke barin wayoyin a gida su fito da ƙarama.

Wani mutum da ya haɗu da irin waɗannan masu ƙwacen waya a cikin babur ɗin ADAIDAITA, ya kuma tsallake rijiya da baya, ya yi wa wakilin IDON GARI bayanin yadda al’amarin ya faru a lokacin da suke tattaunawa.

“Bayan na tare Adaidaitan na shiga, muna ɗan matsawa gaba sai wani ya tare su ya hau suka saka ni a tsakiya. Muna cikin tafiya sai ɗaya daga cikin wanda muke tare dasu a baya yace zai sauka, a take sai mai jan babur ɗin ya taka wani irin burki ba tare da ya rage gudu ba. Hakan yasa muka yi jijjiga tare da tsalle daga kan kujerar mukadawo. Dama wayata (Android) tana cikin aljihun rigata ta gaba.

Taka wannan burki da yayi, ashe shi kuma na gefena ɗayan har ya cire wayar ya jefa ta jikin ɗan uwansa. To ni kuma sai Allah bai sa hankalina ya tafi ko’ina sai nayi saurin duba wayata tun kafin ya sauka amma sai naga babu. To a lokacin da ya cire ta a aljihu naji faɗuwarta gefena da shi ɗayan, don haka sai na miƙa masa hannu nace bani wayata. Babu musu ya miƙo min, sai na sauka nace na fasa hawa, da yake basu da gaskiya tuni sukai gaba har shi wanda yace zai sauka ɗin bai sauka ba..”

Da muke zantawa da wasu daga cikin masu sana’ar Adaidaitan, bayan tambayarsu shin ko ana iya taka burki na lokaci ɗaya don ayi wa fasinja satar wayarsa? Sun tabbatar mana da cewa tabbas ana yin haka, suka ƙara da cewa, hakan wani sabon salo ne ta yadda mutum zai tsorata ya gigice, su kuma sai suyi amfani da wannan damar su zare masa waya (musamman idan a aljihun gaban riga take).

Al’amarin ƙwace da satar waya dai yana ƙara ƙamari a ‘yan kwanakin nan, wanda ko a kwanakin baya ma wasu ɓatagarin matasa sun zare wa wata mata makami a Kaduna, a lokacin da take tafiya kan gadar sama da jama’a suke hawa idan zasu tsallaka titin mota da ke Kawo, inda bayan sun ƙwace wayar suka turo ta daga sama gadar ta faɗo kan kwalta, kafin aje ko’ina take a wajen rai yayi halinsa.

A kan wannan al’amari ne Kakakin rundunar ‘Yansanda ta jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa suna nan suna farautar duk wani mai aikata wannan laifi na ƙwacen waya, dama sauran masu aikata miyagun laifuka. SP Kiyawa ya ƙara nanata cewa, Rundunar ‘Yansandan Kano zata saka ƙafar wando da duk wani tsagera da ya ci gaba da aikata laifi, kuma idan har suka kama mutum to ya kuka da kansa.

Related Posts

Leave a Comment