Me Yake Janyo Rashin Sha’awa ga Ma’aurata.
Rayuwar Iyali
Daga
Bilkisu Yusuf Ali
Wannan matsale ce da abu biyu yake kawota. Na farko dai akwai yanayin zamantakewa inda kuma na biyun zai iya kasancewa rashin lafiya ce ke haifarwa. Katsewar sha’awar miji ga matarsa ko mace da mijinta yana hana zama lafiya a zamantakewar aure sannan ya hana al’amuran rayuwa na yau da gobe gudana , saboda al’amuran aure kaso ma fi rinjaye ya ta’allaka ne akan sha’awa tsakanin iyali. Amma kafin mu fara fadin dalilan da ke kawo rashin sha’awa ta bangaren lafiyar jiki bari mu dau kason farko na yanayin zamantakewa. Wanda wannan yanayi yanayi ne ko aiki ne na kwakwalwa.
• Rashin kwanciyar hankali
Duk lokacin da ya kasance babu kwanciyar hankali tsakanin ma’aurata ba yadda za a yi sha’awa ta gitta. Rashin kwanciyar hankalin nan, ko dai ta ita matar da mijin ko mijin da iyayenta ko da yanayin gari ko matsugunni da dai duk wani nau’in rashin kwanciyar hankalin da zai janyo rashin nutsuwa da fargaba ko zulumi. Hatta a wurin aiki in har namiji yana fama da fargaba da rashin nutsuwa to tabbas zai iya neman sha’awa ya rasa. Sannan ga macen da take da yawan ko tafi da daddare sawa’un matsalarta ko ta kishiya ko ta ‘ya’yan miji a lokacin da namiji ya zo da bukatarta ita ma kan haifar masa rashin kwanciyar hankali wanda duk wannan yana iya janyo rashin sha’awar Maigida ga iyalinsa.
• Talauci
Talauci ko rashin abin hannu shi ma babban makami ne da ke yanke sha’awa. Duk lokacin da samun mutum ya yi kasa kuma BUK atunsa suka ninka har ya shiga sake -saken mafita to fa zai yi wuya duk maganin da zai sha ya yi masa tasiri kan wannan matsalar , dole makarin matsalar shi ne a samu abin da ake bukata amma talauci barazana ne ga sha’awa tsakanin iyali.
• Roko
Akan samu mata masu roke-roke ga maigida kuma sukan rike makamin rokonsu shi ne lokacin da maigida yake da bukatar kasancewa da su. Daga lokacin da wannan ya zame wa mace al’ada kuma miji ya tsani hakan to yana iya zama wani sanadari na kashe masa sha’awar maii dakinsa.
• Kazanta
Duk lokacin da Maigida zai kalli abin da ba ya son idonsa ya kalla, ko ya shaki abin da ba ya son hancinsa ya shaka, ko ya ta~a abin da ba ya son ya ta~a, to tabbas a sannu Uwargida za ta gusar masa da dukkan sha’awarsa. Don haka tsafta tana da matukar tasiri wajen karfafa sha’awar Maigida. Haka kamshi na cikin sinadaran da ke karfafa sha’awa.
• Biyayya
Duk lokacin da mace ta zama ba ta biyayya ga mijinta , kullum tana cikin bata masa rai nan ma zai yi wuya yake sha’awarta. Ita irn wannan biyayyar ba sai iya kansa ba hatta iyayensa in ya lura ba ta mutuntawa ko darajjantawa to tana iya fita a ransa.
• Rashin ni’ima ga mace
Akan samu mata marassa ni’ima da iya sarrafa maigida yayin mu’amalar aure wannan nau’ikan matsalolin sukan shafi zamantakewa da kuma sha’awa tsakanin iyali. Haka ma idan namiji ya fuskanci cewa matar ba ta sha’awarsa ko ma ba ta son kasancewa tare da shi , irin wannan matsalar kan kawo matsalar.
• Ha’inci da karya da cutar da abokin zama ko ‘ya’yansa
Wadannan dalilan kan sa mace ta fita a zuciyar namiji har ya ji ba ya son ko ganinta bare sha’awarsa ta kai gare ta.
Akwai dalilai da dama wanda na zamantakewa ne ke kawo wannan matsalar ba wai rashin lafiya ba.
Sakewa
Yana da kyau yayin kusantar juna ma’aurata su sake da junansu sakewar gaske. Ya kasance sun mallakawa junansu kawunansu tsakaninsu ba tsoro ko shayi ko kunya ta haka ne za su gane mai suke bukata don tabbatar da wannan sha’awa. Don haka dole a sallamawa abokin zama zuciya da gangar jiki. Sannan a cire duk wani abu da ke cikin zuciya na damuwa ko wata matsala a tabbatar ba komai a zuciya da kwakwalwa sai }aunar juna da wannan bukata da aka saka a gaba.
Muhalli
In har ana son a samu sha’awa sai an gyara muhalli an kawar da duk abin da yake zai kawo cikas. Misali tsafta an gyara ko’ina an sa abu mai kamshi dai-dai gwargwado an kawata wajen , yanayin tsafta da kamshi kan sa a samu shauki da sakin jiki. Wasu za su yi tunanin su ce to ina ga masu fya]e ko masu kusantar mace a bola ko kan hanya ko wani waje marar tsafta? To wannan daban. Wannan yana faruwa haka ne da taimakon shaidan da kuma neman biyan bukata don wani dalili. Tsaftar jiki ga ma’aurata musamman mace yana da muhimmanci saboda mace ita za ta janyo sha’awa kada ki yi la’akari da wai an zama daya ko an jima. In har kina son ki jawo sha’awar Maigida sai kin dage da tsafta da kwalliya da turare da tsaftar baki da jiki inda da ya doso ki ba abin da zai gani ko ya ji wanda za su sosa masa rai.
• Hutu
In har babu kyakkyawan hutu da bacci mai kyau musamman akalla wanda aka saba awa shida zuwa bakwai a kullum da wuya a samu kyakkyawan sakamakon da ake bukata. Don haka ana son a samu hutu jiki ya kasance babu gajiya , don gajiya tana hana samun kyakkyawan sakamako akan sha’awa. Saboda sha’awa da kwakwalwa suna tafiya ne tare da juna. Don haka hutu yana da muhimmanci.
Zabin lokacin Kwanciya
Nutsuwa da samun kyakkyawan muhalli yana taimakawa wajen samun sha’awa mai dorewa. Ma’aurata ya kamata su san wane lokaci ne ya fi dacewa su kasance tare kuma wane lokaci ne suka fi samun nutsuwa musamman in har sun kasance suna da iyali. Maganganu masu taushi
Kissa da kisisina da maganganu masu taushi da dadI na motsa sha’awa suna taimakawa ma’aurata kuma suna kusanto da sha’awa. Kowacce mace ita ta san yadda take tafiyar da mijinta da yadda take juyo da hankalinsa da zuciyarsa. Hatta a gun namiji shi ma ire-iren wannan lallashin da tausasa murya da maganganu mai dadi suna taimaka masa wajen tada sha’awar matarsa har ta kai an samu abin da ake bukata.
Motsa jiki
Motsa jiki yana da matukar muhimmanci. Yawancin mata da maza da suka yi nauyi ko kiba kuma suna zaune ba sa motsa jiki suna fama da matsalolin sha’awa da rashin gamsar da juna. Don haka motsa jini ya zama wajibi a gun ma’aurata.
Motsawa
Kyakkyawan motsi yayin da ake kusantar juna yana da amfani bai kamata ma’aurata musamman mace ta kwanta kamar dutse ba. irin wannan ba ya taimaka wa Maigida bare har ya motsa sha’awa.
Tsarin kwanciya
Akwai style kala-kala na kwanciya da ya kamata ma’aurata su san su sannan su gwada. Sau tari ma’aurata suna da zabi wasu sun sani wasu kuma ba su sani ba. gwada ire-iren wannan salo na kwanciya yana da tasiri kuma yana da kyau don akwai gundira a amfani da salo guda.
Gudanar da Wasanni
Hatta a addinin Musulunci ya yi umarni da a tura dan aike kafin a gudanar da mu’amalar aure. Ma’aurata musamman mata suna kuka da yadda mazajensu suke zuwa musu. Wasanni yana motsa sha’awa kuma a wannan wasannin ne miji kan gane ina ne makamar matarsa haka ita ma matar za ta gane ina ne mijinta ya fi so.
Neman Magani
Idan har akwai wata larura da take kawo wannan matsalar ta rashin sha’awa yayin kusantar juna to wajibi ne a kawar da ita kafin a ga biyan bu}ata. Ire-iren wa]annan larurori akwai ciwon sanyi da ciwon suga da hawan jini da nau’ikan basur da dai sauran larurori. Don haka yana da kyau ma’aurata su fara sanin yanayin rashin lafiyarsu kafin su fara yin magani.
Amma babban makama da yake dorar da sha’awa shi ne:
Biyayya
Abu na farko kuma na karshe shi ne biyayya da kaunar juna duk sha’awa ba t a tasiri in har babu kauna da soyayyar juna da mutunta juna. Mace wajibi ta yi biyayya ga mijinta ta tausasa harshe ta lakanci me yake so da bin da ba ya so. Sannan ki lakanci lokacin da yake da sha’awar magana da lokacin da yake kyakkyawan yanayi da lokacin da ba ya son a dame shi. Idan ki ka kiyaye wadannan abubuwa za ki mallaki sha’awar mijinki. Sannan shi ma maigida yana da kyau ka ke mutunta matarka, ka ba ta duk Hakkokinta dai-dai gwargwado ka kyautatawa iyayenta wannan zai sa ta saki jiki, ita ma kuma kullum ta kasance cikin laluben hanyar da za ta faranta maka.

