Adabi Mudubin Rayuwa
Tarihi da Gudummawar Malam Bala Anas Babinlata a duniyar Adabi
Daga
Sarra Tasi’u Ya’u
In ha rana batun kirkira na kageggen labari cikin kwarewa da hikima da basira to tabbas tarihin adabin Hausa ba zai taba kammala ba in har ba a sako Malam Bala Anas a ciki ba.Jarumta da kwarewarsa da bayar da gudummawa ba ta tsaya iya rubutun zube na littafi ba hatta a masana’antar Kanywood Malam Bala Anas ya zama wani jigo da ake jingina da shi a bangarori da dama kama daga labarin fim din zuwa shiryawa. A yau in dai ana batun siddabaru a fina-finai da an ce Babinlata to addu’a ake a shafa iyaka Kenan
Za mu so mu ji takaitaccen tarihinka
An haife ni a shekarar 1964 a watan nuwamba a cikin birnin Kano. Na fara da karatnn muhammadiyya kamar yadda yake a addininmu da al’adarmu sannan aka sa ni a makarantar firamare ta K/Nassarawa a 1072-1977 na qarasa a Dakata Firamare. Na Yi sakandire a Kawaji sannan na shiga makarantar School of Management na karanta Secretarial studies.Na fara aikin gwamnati wanda na bari tun wajen shekara ishirin da suka wuce don kashin kai.
Fara Karatuna
Na fara rubutu tun a lokacin ina Sakandire amma littafin farko da na fara rubutawa na turanci ne. Na fara karatun littafin Hausa tun ina aji biyu na Firamare, ban kai aji huxu ba na qure NNPC da Alhuda-huda duk wani littafin Hausa a lokacin na karance shi ya zamana ni nake jira. Kasancewar karatun ya shige ni sai kuma na kasa jiran sai na fara tsallakawa ina neman littatafan Turanci na fara da qananan littattafai irin su Hackles da series sermon nan ma sai na ga labarurrukan ba sa gamsar da ni sai na tsallaka nan na yi ganganci na fara karanta na Turawa maimakon na ‘yan Afrika tun ina kokawa da ganewa sai na nemi Dictionary har ya zamanto har na murmure. Wannan ya sa sai na ji kawai ni littafin Turanci zan rubuta kuma har sai da ta kai na kusa kammalawa sannan na ajiye shi na fara rubuta na Hausa. Amma littafina na farko na yi shi ne a shekarar 1980 . har yanzu bai kai ga bugawa ba saboda littafin tunanina irin na wannan lokacin ne sunan littafin “Son maso wani”. A lokacin ko dai ka kai Alhuda-huda su buga maka ko kuma NNPC har ya zama sun ma daina publishing sai dai mu rubuta mu ajiye. Amma littafina na farko da na buga shi ne Kulu na buga shi a 1991
Dalilin Fara Rubutuna
Yawan karatu da kallo shi ya ja hankalina har na fara karatu saboda a lokacin hatta wasu rubuce-rubuce da aka yi da ajami sai da na karanta. Ta Ya ya ka Koma Sana’ar Fim
Tun farko da ma ni ina cikin harkar wasan kwaikwayo wai ba daga baya na koma ba saboda tun fil azal da ni da Abokina Khalid Musa muna da qungiyar wasan kwaikwayonmu da muka kira Jigon Hausa. Ita wannan qungiyar ta jigon Hausa muna rubuta labarurruka da ake yin su a dabe da wanda ake sa musu kyamara labarurruka da fina-finan da muka yi sun girmi fara rubutuna na littafi. Abinda ya karkato ni ma har na dawo harkar rubutun littafin ganin yadda Gidan dabino da Xan’azimi Baba da Balaraba Ramat suka buga littafinsu da kansu don haka ni ma sai na kai nawa aka yi type setting na buga abina. To da ma ni a wajena na mai kirkira burina ta ya ya zan isar da sakona ga al’umma da na ga a wannan kafar na sami karbuwa sakona ya isa sai na mayar da hankali anan fiye da wasan kwaikwayo. Har sai da aka kawo gabar da muka haifar da kasuwar bidiyo kafin ta zama Kanywood . Don a lokacin, kawai muna yin kwali inda za a dau hoton a lika a jiki. Ni ne na fara cewa bangane wancan ba don a lokacin za a ba da abin da bai taka kara ya karya ba ni na ce sai dai su biya kudin hoton kuma su biya kudin kwalin muka sa abin ya mike. Ganin ya mike din muka ga ya zama kasuwanci sai muka dawo kansa saboda shi duk da kudin da ake kashewa ya ninnika na littafi to amma idan aka kawo shi kasuwa ya fi littafi kawo kudi, don shi za a ba ka kudinka a dunkule ga riba kuma a lokacin ana nunawa a silima lokaci daya za ka karbi kudinka. A lokacinma mashin da ake amfani da shi na ma’aikatar Information ne da CTV da muke yin lenier editiin. Da suka sami matsala sai muke amfani da bidiyo da bidiyo har zuwa yau da ake yin digital editing ana amfani da kwamfuta. Amma a lokacin masu buga kwali daban masu aikin fosta daban masu yawo a mota suna zagayawa suna sanarwa in za a nuna fim a sinima daban har ta kai ga an yi mujallar fim ta farko mai suna tauraruwa daga ita ne ma mai mujallar malam Sunusi Shehu Daneji ya radawa masana’antar suna da Kanywood.
A Harkar Rubutun Littafi da Fim wa ne Jagoranka?
Zai yi wuya a sami jagora musamman a harkar da kai ka kawo kanka da kanka sannan musamman ina cikin sahun farko da muka kafa wannan masana’antar hakan sai yasa kusan duk waxanda muka kafa harkar abokai ne. Amma akwai waxanda nake xaukarsu iyayen gidana akwai Mai unguwar Daneji Alh Abba Lawan Daneji kusan aminina ne amma ina kallonsa a ubangida. Sai kuma Farfesa Abdallah Uba Adamu shi ma ubangida ne wajena don duk abinda zan nema zan samu wani lokacin ma shi zai ce me nake so saboda yana harkar internet duk abinda nake nema shi zai tattaro ya ce na zo na karba wani abin sayowa zai yi wani kuma downloading zai yi gaskiya farfesa Abdallah ya daure min gindi kwarai. Duk abinda na ji sabo zan kira in ma babu zai sa a kawo a duk inda yake a duniya.
Ka Kware a Directing Bidiyo Effect da Animation da Editing, Suna da Alaqa da Rubutu ne?
Duk kowanne yana cin gashin kansa ne, wanda yake da alaqa ma da rubutu shi ne aditin in an ce wanda ya yi rubutu marubuci na daya to adita shi ne marubuci na biyu don adita yana iya canza alqiblar labari ya kara sa wa ya yi nauyi. Amma shi darakta ana so ne ya zama ya hada ilimin kowa ko da kuwa ba ka kware ba ya zama ka san wani abu a ciki. Duk fim ana kallonsa ne ta fuskar darakta.
Kukan da al’umma ke yi kan ingancin labari laifi waye?
To wannan korafi yana fitowa daga kowanne bangarori akwai kalubalen. Abu na farko dai su marubutan suna yin rubutu ne dai-dai saninsu don haka za ga rubutun da aka yi da karancin shekaru da bambanci da wanda aka yi bayan marubucin ya mallaki hankalinsa ya yi iyalai. Sannan a bangaren al’umma su ma sun zamewa rubutu cikas. Ina ji Bahaushe ne kadai ke da dabi’ar suka babu yabo. Shi zai soke ka bai ma san mai ka yi ba. Mutane wasu ma ba sa dubawa in sun ga kuskure su gyara masa in kuma ya yi kokari a yaba masa. Kullum ana yi mana kudin goro ne marubutan soyayya ne har ta kai ma muna rubuta abu muhimmi da bai shafi soyayyar ba amma sunanmu bai sauya ba saboda mutanen ba karantawa suke ba. Mu marubutan yanzu ba mu samu wannan gatan da za a tallafe mu ba kamar yadda a ka yi wa na baya irin su malam Abubakar Imam inda suka sami kulawar Norla da hukumar fassara zuwa NNPC. Su an bar su sun girma da rubutunsu . Wannan ya hana rubutu girma da ka fara ba za a bar ka ka girma da rubutunka ba sai a datse ka sai wani shi ma yaro sharaf ya fara tunda ba za ka yi tsalle ya shige tsayinka ba kai ma xin iya saninka za ka rubuta. Don haka har yanzu rubututtukanmu yana nan a yarintarsa.
Amma a vangaren fim su ma suna da waccar matsalar amma kuma kafin waccar xin su masu shirya fina-finan ne suka kasa girma ba marubutansu ba. Su masu fim su za su zaunar da marubuci su ce ga yadda suke son labarin in ma marubuci ya kawo ba yadda suke so ba, za su ce a’a don haka sai ya zama gabaxaya an kasa morar marubutan duk abinda za ka gani ba nasu ba ne su kuma ‘yan gari in sun ga shiririta ba tare da sun sani ba sais u zargi marubuci. Wanda a qa’ida marubucin ya kamata ya jajirce bai kamata ya zama haka ba.
WANNE QALUBALE KA SAMU A RUBUTU
Ai qalubalen da na fuskanta ba za su lissafu ba akwai qalubale na rubutu ya fara lokacin da muka qetaro daga yin wasan kwaikwayo na dave muka ce za mu yi home vedio sai ya zama littattafanmu ba mu da jarin da za mu yi su a fim don haka da muka zo mayar da shi fim sai ya zama da wuya saboda ba mu qayyade iya gidaje da ma budged ba. Bayan an gama xaukar fim xin har sai da na kwanta jinya don sai da muka yi kwana goma a jere kowacce rana da matsalarta waxannan matsaloli kala-kala ban san su a littafi ba.
Sannan ita kanta masana’antar tana da ta ta matsalar wanda babban qalubale ne da cikas. Masana’antar akwai qarancin ilimi amma abin takaici domin mutane su haqura su nemi ilimin sai kuma suke tunqaho da jahilci har tunqaho suke ka je da iliminka mu haxe a kasuwa. To yanzu ga kasuwa ta zama fagen ilimi don haka sai aka diririce. Har sai ya zama gara ma yadda muka fara don mu sai mun nuna a sinima mun harhaxa kuxaxenmu sannan mu kai kasuwa in za a sata a sata . Amma su sai ya zamanto da an agama fim xin za a dire shi ne a gaban varayi ‘yan piracy kuma ana ji ana gani ba yadda za a iya.
Su kansu masu shirya fina-finan ba sa kallon fim xinsu in har ka ga mutum ya kalli fim to nasa ne ko kuma na abokinsa. In har kai da kake cikin masana’antar ba za ka kalla ba to ta ya ya ka ke tunanin wani zai kalla? Duk lokacin da za ka tsaya ka ce kai za ka birge kanka dakanka to akwai matsala. Labari ka faxa a soke shi ne za ka gyara kuma shi ne za ka yi abu mai kyau.
NASARA FA?
Nasarori akwai su da yawa. Nasarar farko da na fara samu shi ne muryata a ji ta kusan duk abin da ke damuna na xau alqalami na rubuta kuma na kai shi kasuwa a sa kuxi a saya. Misali littafina Zinaru ban san abin da na rubuta ba sai da na kai kasuwa. Ni kawai bincike na yi kan ‘yan Kano –Jidda na tsara labarina. Amma da littafin ya fita taratsin da littafin ya samar ni kaina sai da na sake karanta littafin. Hatta wanda ya katanta littafin zinaru a gidan radiyo sau biyu ana kiransa shaida don karanta littafin da ya yi a kotu. Wata Hajiya har kuxi ta bayar dubu arba’in irin ta wancan lokacin tare da magiyar a daina karanta littafin.Rubutu kaxai zai iya ba ka wannan nasarar.
Shi kuwa Fim nasarorinsa ba ma za su iya lissafuwa ba kama daga karramawa da aka samu sannan duk inda ka shiga ake yaba ayyukanka. A kwai wani babban festival da ake yi Can Film festival film award ne da ake yin sa Europe a France babban award ne kowanne xan Flm yana alfahari in an nuna shi anan. Sannan na sami kambun girmamawa a Zuma Film festival da national film festival
City Bussness centre an kafa ta ne saboda yin editin da typing da grapics da foster amma ni na tsa aka samo wani kati wanda na takurawa Alh Abba Daneji ya sayo vc10 ya buxe kwamfutarsa da ake yin waxancan ayyukan aka saka. Ni na zo da wannan sabuwar fasahar don haka dole sai mun jira an tashi sha xayan dare a wannan wajen sannan ni da shi za mu zauna mu kwana muna kallon yama abin yake mu duba manual don ma ba mu san yanda abin yake ba har zuwa daga baya mutane suka raja’a a kansa. A yau a fagen aditin da typing da harkar fim daga ‘ya’ya sai jikoki na wannan City Bussness center xin.
Ni ne mutum na farko a home vidiyo da na fita na kama hotel suit don xaukar shirin fim wannan ma babbar nasara ce.
KIRA GA MARUBUTA A YAU

Kirana ga matasa ne da suka shigo rubutu amma mu waxanda muka fara rubutu tare har yanzu ba wanda ya bar rubutu. Kirana gare su shi ne su yi a hankali da alqalami su kiyaye abin da zai je ya dawo su tabbatar mai amfani ne kada su yi rubutun da zai je ya dawo ya yaqe su.
Yaya Bala Anas Babinlata muna godiya Allah ya qara girma da xaukaka ya ja kwana amin.

