Shugaba Tinubu Ya yi Sabbin Nade-nade A Bangaren Tsaro
A wani mataki na karfafa bangaren tsaron kasa, shugaba Bola Tinubu ya sanya hannun amincewa da nadin sabbin shugabanni a hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta (PSC) da kuma asusun kula da walwalar ‘yan sandan Najeriya (NPTF).
Wadanda shugaban ya nada sun hada da
– DIG Hashimu Argungu mai ritaya a matsayin Shugaban Hukumar ‘Yan Sanda (PSC) sai Chief Onyemuche Nnamani a matsayin Sakatare, PSC
Sai DIG Taiwo Lakanu mai ritaya a matsayin Memba a hukumar PSC.
Haka zalika shugaban ya amince da nadin Malam Mohammed Sheidu a matsayin Babban Sakatare na (NPTF)
Ana sa ran Majalisar kasa za ta amince da nadin nan ba da dadewa ba, kazalika nan ba da jimawa ba za a sanar da nadin karin mambobi a hukumar
Shugaban na fatan mutanen da aka nada zasu nuna kwazo da jajircewa tare da yin aiki da gaskiya, da kishin kasa domin kara habaka ‘yan sandan Najeriya da ci gaban kasa baki daya.
Sanarwar daga kafar yada labarai ta fadar shugaban kasa, Yuni 10, 2024

