Home Labarai Kungiyar Matasa Ta yi Tayin Hada Kai Da Gwamnati Don Kawo Karshen Satar Danyen Mai*

Kungiyar Matasa Ta yi Tayin Hada Kai Da Gwamnati Don Kawo Karshen Satar Danyen Mai*

by Muhsin Tasiu Yau

*Kungiyar Matasa Ta yi Tayin Hada Kai Da Gwamnati Don Kawo Karshen Satar Danyen Mai*

A yunkurinta na cika alkawuran da ta yi wa matasa na samar musu da damammaki na aiyukan yi,

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya jaddada kudirin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na tallafa wa matasan Najeriya wajen ganin sun kai kololuwar ci gaba a bangaren ayyuka masu dogaro da fasahar zamani karkashin shirin iDICE da basu guraben gudanarwa a cikin gwamnati.

 

Kashim Shettima ya bayyana hakan ne a yayinda ya karbi bakuncin Mambobin Majalisar Zartarwa ta Matasa ta Kasa (NYCN) a fadar shugaban kasa, inda ya yaba wa majalisar bisa goyon bayan da take bai wa tsare-tsaren ayyukan gwamnati

 

A nata bangaren Kungiyar NYCN ta yi tayin hada kai da gwamnatin tarayya wajen magance matsalar masu fasa bututun mai ba bisa ka’ida ba, sannan ta nemi a gina gidan matasa.

 

Kungiyar NYCN da aka kafa a shekarar 1964, tana bikin cika shekaru 60 da kafuwa a bana, kuma ta gayyaci VP Shettima da ya kaddamar da bikin tunawa da ranar kafuwarta a hukumance, wanda ake sa ran za a samu mahalarta sama da 100,000 daga sassan kasar.

Related Posts

Leave a Comment