
Hukumar hana fasakwauri ta ƙasa, hukumar kula da shige da fice ta ƙasa, rundunar tsaro ta farin kaya, hukumar yaƙi da cin-hanci da rashawa sun bazama kan iyakoki domin hana fita da abinci ƙasashen waje daga Najeriya.
Matakin na gwamnati na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyoyin ƙwadago suka ayyana gudanar da zanga-zangar kwanaki biyu saboda matsalar tsadar rayuwar da ake ciki a Najeriya.
Majiya daga fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya kafa rundunar aikin haɗin gwiwar domin su daƙile duk wata safarar fita da abinci daga Najeriya a duk kan iyakokin ƙasar dake Borno, Niger, Katsina, Sokoto, Kebbi, da Jihar Jigawa.
Wannan cigaba ya samu ne bayan kammala wani taron gaggawa a tsakanin shugaban ƙasa, da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da gwamnonin Jihohi a Abuja fadar shugaban ƙasa, a ranar Alhamis.
A taron, shugaban ƙasa Tinubu ya umarci babban mai ba shi shawara kan tsaro, shugaban ƴan sanda, shugaban rundunar tsaro ta farin kaya, DSS, da su tabbatar da cewa sun bankaɗo tare da rufe dukkan wani wuri da aka ɓoye abinci su yi duk abin da ya dace a kai tayadda za a magance matsalar tsadar abinci da ƙarancinsa a Najeriya.
Daga Shafin Sabuwar Nigeria

