Home Labarai Shugaba Tinubu ya biya bashin da malaman jami’a ke bi Wanda gwamnatin baya ta rike musu.

Shugaba Tinubu ya biya bashin da malaman jami’a ke bi Wanda gwamnatin baya ta rike musu.

by masta

A ƙoƙarinsa na tabbatar da daidaito da adalci gami da fatansa na sauƙaƙa wa ƴan ƙasa halin da suke ciki, shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya biya malaman jami’a albashinsu na tsawon watanni huɗu da gwamnatin baya ta riƙe musu.

Idan jama’a ba su manta ba, gwamnatin da ta gabata ta hana malaman Jami’a albashinsu na tsawon watanni huɗu saboda yajin aikin da suka shiga. Sai dai a wannan lokaci shugaban ƙasa Tinubu ya biya su albashin na wata huɗu.

Daɗi da ƙari, wannan na zuwa ne bayan da shugaba Tinubu ya amince da ƙarin albashin malaman da kashi 35.

Biyan Malaman Jami’a albashin watanni huɗu abu ne da zai taimaka ta fuskar tattalin arziƙi a samu walwala da farin ciki a zukatan ɗumbin al’umma.

Related Posts

Leave a Comment