Magana ta gaskia akwai abun fargaba ga hukuncin gobe, wanda idan aka duba a tsanake za’a iya fahimtar mai Supreme Court zata yanke in Allah ya kaimu gobe.
Bayan binciken danayi ina ganin yakamata mu koma baya muduba muga meyafaru a Tribunal da Appeal Court in summary.
1. Tribunal Court:
Ita wannan kotu tace Dr Nasiru Yusuf yayi nasara saboda evidences da APC ta kawo na NNPP sun saka kuri’u na bogi wanda NNPP kuma takasa kare kanta a Tribunal har ita Tribunal din ta ayyana Dr Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin Halastaccen Gwamnan Kano.
Sannan NNPP a gefe kuma tayi nasara akan membership din Alh Abba Kabir Yusuf inda kotu tace tabbas koda Alh Abba Kabir Yusuf ba halastaccen member din NNPP bane ita ba huruminta bane tace shi ba dan NNPP bane.
2. Appeal Court:
Ita wannan kotu bayan tayi reviewing din abubuwan dasuka faru a Tribunal saitace, hukuncin da Tribunal ta yanke yayi daidai sannan kuma Tribunal ma tayi kuskure da batace Alh Abba Kabir Yusuf ba ‘dan Jam’iyya bane. To anan mene hukuncin Tribunal? Hukuncin Tribunal kuma shine maganar kuri’u na bogi da akanshi tace Dr Nasiru Yusuf Gawuna yaci zabe.
Yanzu mudawo SUPREME COURT da zatayi hukuncin gobe:
Supreme Court fa itama review ne bawani abuba ta duba taga abubuwan da Tribunal da Appeal sukayi shin sunyi daidai ko kuskure.
Wasu suna ganin SUPREME COURT zata iya cewa INCONCLUSIVE ne Election din gabadaya, ni kuma sai nake gani tun a Tribunal Court muka wuce wannan maganar.
Wasu suna ganin ai SUPREME COURT tayi hukunci akan shari’ar membership a baya wanda tace ba huruminta bane ba. To zan iya yarda APC zata iya faduwa maganar Membership na Alh Abba Kabir Yusuf wanda ba lallai hakan tafaru ba duba da case din ba iri daya bane dana sauran shari’un da akayi a baya.
Babbar Tambaya: Ya za’ayi da kuri’un bogi a Supreme Court.
Itafa Supreme Court bawasu shaidu da Zata sake karba, anwuce wannan gun tuntuni.
Amsa: Kuri’un bogi su zasu kayar da NNPP gobe a SUPREME COURT, anan ta ayyana Dr Nasiru Yusuf Gawuna na APC a matsayin Gwamnan Kano.
UsmanIshaq Shehu, GMICCON
PhD Candidate. 🖊

