Mataimakin shugaban kasa sanata Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a wajen taron Babban Maulidin Manzon Allah na kasa ( SALLALLAHU ALAIHI Wasallam)
Wanda ya gudana a Dandalin Tafawabalewa da ke Jahar Lagos a ranar 13 ga watan jinairun 2013.
Mataimakin ya kara da cewa domin biyayya ga wannan koyarwar gwamnatin shugaba Tinubu zata yi duk mai yiwuwa don ganin ta kare hakkokin ‘Yan Najeriya, ba tare da la’akari da Addini ko Kabilanci ba
Sanata Shettima ya yaba da kokarin da Jam’iyyatu Ansariddeen Attijaniyya da ma daukacin ‘yan Tijjaniyya da sauran darikun sufaye ke yi don shirya taruka masu kira ga zaman lafiya a tsakanin addinai daban-daban
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Jam’iyyar Jam’iyyatu Ansariddeen (Attijjaniyya) da Sarkin Kano na 14, Khalifa Muhammadu Sanusi Lamido Sanusi II, suka roki ‘yan Nijeriya da su ba gwamnatin Tinubu goyon baya domin ciyar da kasar gaba.
A wani mataki na inganta hadin kai da hakuri da juna a tsakanin al’ummar kasar, mataimakin shugaban kasar ya jaddada muhimmancin hada kai da kuma mutunta ‘yancin addini a kasar da ke da al’umma sama da miliyan 200 da suka rabu ta hanyar addini da kabilanci.
Mataimakin shugaban kasar ya tabbatar wa da mahalarta taron cewa shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai yi aiki da sakonnin zaman lafiya da taron ya kunsa kuma tuni ya himmatu wajen kare haƙƙin ‘yan Nijeriya da ‘yancinsu, ba tare da la’akari da imaninsu ba.
“Koyarwar Annabi Muhammad (SALLALLAHU ALAIHI Wasallam) ta kasance wani ma’aunin koyar da adalci da kyautata mu’amala a tsakanin Al’ummomin duniya mabambanta matsayi da al’adu. Manzon Allah SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM Ya koya mana hanyoyin samar da zaman lafiya da magance rikice-rikice ta hanyar kyakkyawar tattaunawa, da kuma juriya,” inji shi.
Mataimakin Shugaban ya nuna godiya ga Babban Sakataren kungiyar Tijjaniyya ta kasa da kasa kuma Shugaban Jam’iyyatu Ansariddeen Attijaniyya bisa kyakkyawan jagoranci da jajircewa wajen bayyana kyawawan dabi’u.
Da yake magana kan kalubalen da al’ummar kasar ke fuskanta, Shettima ya amince da nauyin amanar da al’ummar Najeriya suka dora wa Shugaba Tinubu.
Ya yi kira da a taya shugaban kasa da sauran shugabanni addu’a don samin nasara a kan gyaran Najeriya.
Sanata Shettima ya wakilci shugaban kasa da al’ummar Najeriya sama da miliyan 200 wajen nuna farinciki da godiya kan addua da saukar Alqur’ani mai girma sau 4,444 da Jam’iyyatu Ansariddeen Attijaniyya tayi ga Najeriya da shugabanta.
“Muna fatan kulla zumunci da kungiyar Jam’iyyatu Ansariddeen Attijaniyya, muna yaba wa kokarinku na samar da zaman lafiya a tsakanin al’ummomin addinai daban-daban. "in ji shi.
VP Shettima ya tabo maganar gyaran halaye a matsayin abin da ake bukata don sauye-sauyen al’umma, yana mai cewa "kamar yadda Allah ya yi umarni a cikin Alkur’ani, cewa Allah Ba Ya sauya al’umma har sai ta yi yunkurin sauya kanta da kanta"
Ya bukaci daukacin ‘yan Najeriya da su yi koyi da wannan koyarwar, da kwarewar sufaye wajen tsarkake ruhi da kuma dabi’u
Kalamansa: "Dukkanmu muna neman hanyoyinmu don samun fansa, a nan, muna ba da gudummawar gina al’umma mai kare mutuncin kowane mutum, da sanin hakkin kowace kungiya, da kuma jaddada ma’anar hakuri."
Mataimakin shugaban kasar ya yi kira da a dauki matakin bai daya, yana mai jaddada bukatar gina kasa mai tubalin tausayi da adalci da adalci.
Ya kuma roki ‘yan Nijeriya da su hada kai da ‘yan uwantaka da ‘yan’uwantaka wajen sauke nauyin da ke wuyan kasa a kan al’ummarta da kuma rungumar karantarwar Manzo maras lokaci.
Tun da farko, Shugaban Jam’iyyatu Ansariddeen (Attijjaniyya), Khalifa Muhammadu Sanusi Lamido Sanusi II, ya roki ‘yan Nijeriya da su ba da goyon baya ga gwamnatin Tinubu domin ciyar da kasa gaba.
Sarkin Kanon na 14 ya kuma yi kira ga ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da malaman addini da sarakunan gargajiya da su mai da hankali kan aikin gina kasa,
Shi ma Babban Jagorab Ansariddeen Attijaniyya na duniya Sheikh Baba Lamin Inyass yayi kira ga Al’ummar Musulmi da su mutunta ‘yancin Dan Adam da yin riko da zaman lafiyar. Sheikh Inyass ya kara da cewa yin hakan wani babban matsayi ne a sashin biyayya ga halaye da koyarwar Halayen Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad SALLALLAHU ALAIHI Wasallam
*Stanley Nkwocha Babban mai taimaka wa Mataimakin Shugaban kasa kan harkar yada labarai*
Fassarar: Rahma Abdulmajid


