Home Labarai LAMUNIN ILMI BA ZAI TAKAITA GA MASU ZUWA JAMI’A BA. IN JI SHUGABAN KASAR NIJERIYA TINUBU

LAMUNIN ILMI BA ZAI TAKAITA GA MASU ZUWA JAMI’A BA. IN JI SHUGABAN KASAR NIJERIYA TINUBU

by masta

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umurci hukumar kula da asusun ba da lamunin ilimi ta Najeriya (NELFUND) da ta fadada shirinta na bayar da lamuni marar ruwa har ya kai ga daliban Najeriya masu sha’awar kirkire-kirkiren bunkasa fasaha.

Shugaban ya bayar da wannan umarni ne a yau 22/ 01/24 a fadar gwamnatin yayin wata tattaunawa da ta hada da sakataren zartaswa na NELFUND Mista Akintunde Sawyerr, kan yadda za a fara kaddamar da shirin bayar da lamunin nan da kwanaki kadan masu zuwa.

Shugaban ya kara da cewa samin damar koyon sana’o’i tamkar samun digiri na farko da na biyu ne idan aka yi la’akari da irin tarin baiwar da Allah Ya hore wa matasan Najeriya a fannonin kirkira daban daban.
"Don haka bai kamata wannan lamuni ya takaita ga masu son zama likitoci ko lauyoyi, ko ma’aikatan bankuna kadai ba, dole ne ya karade sauran masu dauke da kwarewa, da buri da fasahar da za ta gina al’ummarmu a bangarori bila adadin, bisa ga wannan, na umurci NELFUND da ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta kafa shirin inganta fasaha ga wadanda ba dole ne sai sun je jami’a ba”
inji Shugaba Tinubu

Da yake nasa jawabin Mista Sawyerr ya sha alwashin samar da shiri na dindindin ga kudaden da aka ware wa jajurtattun ɗaliban Najeriya ta inda za su rika samin lamunin kai tsaye ta hanyoyin da suka dace.

Related Posts

Leave a Comment