Najeriya ta gaji samin sabanin fahimta a duk lokacin da wata ma’aikata ko birni zai bar wani yanki zuwa wani, Misalin hakan shine lokacin tashin babban birnin tarayya daga Legas zuwa Abuja karkashin Shugaba Babangida. Mutanen yankin kudun sun rika korafin cewa an yi haka ne da wata boyayyar manufa ta kashe yankin na Kudu.
Wannan ne ya sanya ba za a ga laifi ko beken masu korafi kan tashin FAAN daga Abuja zuwa Lagos ba, sai dai dole a yi musu bayanin abinda hakan ke nufi kamar dai yadda aka yi ta bayani ga ‘yan kudun dalilan dawowa Abuja.
Bari mu fara da wannan tambayar, Shin ko kun san cewa Dawowar FAAN Abuja dama ta jeka-na-yi-ka ce?
Kwarai babu Wata FAAN a Abuja domin tun da fari babu wani ginin Shalkwatar a Abuja, kuma gaggan ma’aikatan hukumar tun da fari can suna Legas din kasancewar kashi sittin na aiyukan hukumar da ma kudin shigarta yana Legas din ne duba da yadda harkar sifiri ta nace a tsohon birnin.
Ba wannan ne damuwar ba, Babbar damuwar ita ce Almubazzaranci. A duk shekara Hukumar na kashe makudan kudaden talakawa da suka zarce Bilyoyin Nairori don biyan hayan ginin da ake kira Shalkwatar ta Hukumar FAAN a Abuja, baya da wannan Gwamnati na biyan karin makudan kudin guziri ga ma’aikatan da ke Legas kari akan salary da alawus dinsu da sunan cewa sun zo ne daga Shalkwatar hukumar da ke Abuja, duk kuwa da a Legas din suke, wannan fa na faruwa ne a yayinda tsohuwar Shalkwatar dake Legas kuma mallakar hukumar ba gidan haya ba tana nan daram
Domin magance wannan Almubazzaranci da yin tattalin kudin kasa, Hukumar ta yanke shawarar mai da Shalkwatar ta wucin gadi zuwa Legas don cin ribar abubuwa kamar haka:
1 Daina biyan kudin haya da ake na ginin hukumar a Abuja don zuba kudin a aikin gina sabuwar hukumar a Abuja
2 Daina buyan kudin Guziri na DTA ga ma’aikatan hukumar ta hanyar tabbatar musu da cewa su fa ba baki bane a Legas a can suke aiki, Shi ma wannan kudin za a zuba shi a aikin ginin hukumar.
3 Daina asarar kudin da ak


