Home Labarai Yadda Jami’ar FUDMA Ta Bunƙasa A Ƙarƙashin Jagorancina, Cewar Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi

Yadda Jami’ar FUDMA Ta Bunƙasa A Ƙarƙashin Jagorancina, Cewar Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi

by Muhsin Tasiu Yau

Yadda Jami’ar FUDMA Ta Bunƙasa A Ƙarƙashin Jagorancina, Cewar Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi

Shugaban Jami’ar Gwamnatin Tarayya Dake Dutsinma a jihar Katsina, Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi ya bayyana cewa Jami’ar a ƙarƙashin jagorancinsa ta samu gagarumar bunƙasa a ƙarƙashin jagorancinsa da dama a fannoni daban-daban.

Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi ya bayyana haka a lokacin da ya ke tattauna wa da manema labarai a shirye-shiryen yaye daliban Jami’ar da ake shirin yi ranar Asabar mai zuwa, yau Alhamis a mazaunin Jami’ar da ke Dutsinma, jihar Katsina.

Shugaban Jami’ar, Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi ya kara da cewa lokacin da na karɓi ragamar tafiyar da Jami’ar, tana da tsangoyoyi guda ukku kacal, amma a halin yanzu muna da tsangoyoyi guda goma sha ukku. Haka zalika, na iske ana kwasa-kwasai ashirin zuwa yanzu sun fi guda ɗari kuma a lokacin guda ukku kaɗai Hukumar kula da Jami’o’i ta amince da su dari bisa dari. Waɗannan sama da dari da mu ke da su an aminta Jami’ar ta gudanar da su dari bisa dari.

Haka zalika, mun gina tsangayar Nazarin Aikin Likita da ta Injiniyarin da ta Albarkatun Ƙasa kuma muna kan hanyar gina ta muhalli da kuma ta nazarin aikin malanta. Cikin Kuɗin shigar da muke samu a Jami’ar, mun gina dakin kwanan dalibai mata.

Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi ya cigaba da cewa wannan biki yaye daliban da za mu yi wanda muka haɗa karo na bakwai da na Takwas, za mu yi yaye masu digirin farko su 4365, wanda cikin su akwai masu digiri mai daraja ta daya guda 112. Wannan Shi ne karo na farko da za mu yaye dalibai masu digiri na biyu da na ukku a wannan Jami’a, su 401 a cikin su akwai masu digirin Digir-gir su 11 da digirin na biyu 168, akwai masu digiri na biyu fannin Ƙwarewa su 75 da kuma masu babbar diploma 179.

Akwai manyan kasa da za mu karrama da digirin Girmamawa, Waɗanda suka haɗa da Tsohan Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Shehu Shema da mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar da kuma mai martaba Sarkin Bichi a jihar Kano, Alhaji Nasiru Ado Bayero a ranar Asabar mai zuwa.

Related Posts

Leave a Comment