*SHUGABA TINUBU YA NUNA BACIN RANSA KAN HARIN BAM A KADUNA*
A yayinda yake mika ta’aziyyarsa ga Gwamnatin jahar Kaduna da iyalan mamatan da ma daukacin Najeriya. Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna kaduwarsa kan mummunan lamarin da ya faru na tashin bam a wani kauye da ke Tundun Biri a karamar hukumar Igabi a jihar.
Shugaba Tinubu ya bayyana lamarin a matsayin wani abu mai tayar da hankali da sanya takaici mai radadi, inda ya bayyana bacin ransa matuka kan abinda ya kira mummunan asarar rayukan da ta auka wa Najeriya.
Shugaban kasar ya bayar da umarni na gaggawa kan a gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da yin kira da a kwantar da hankula yayin da hukumomi suka sanya ido sosai kan lamarin.
Shugaban ya kuma umarci jami’ai masu ruwa da tsaki da su bayar da kulawar gaggawa ga wadanda abin ya shafa tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.
Chief Ajuri Ngelale
Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman
(Kan yada labarai da Jama’a)
Disamba 5, 2023


