322
Tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar Tudun Wada/Doguwa na Jihar Kano, Alhassan Ado Doguwa, ya yi ikirarin cewa jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar ta lashe zaben 2023 ta hanyar magudi.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa jam’iyyar NNPP ta samu rinjayen kuri’u a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 da kuma kujeru masu rinjaye a zabukan ‘yan majalisar dokokin jihar da aka gudanar a rana guda.
Daga nan ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana jam’iyyar a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

