Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta cafke wasu mutane shida da ake zargin su da garkuwa da mutane.
Ana tuhumar mutanen shida ne da laifin yin garkuwa da wani yaro mai shekaru 9, Mustapha Ibrahim, da kuma neman kudin fansa naira miliyan biyar.
Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Mubi-South.
Wadanda ake zargin sune Abubakar Mohammed, Auwal Usman, Mohammed Abubakar, Umar Mohammed, Abdulhameed Musa da Muhammad Nasir, mazauna unguwar Maiha Road da Kaba Ward ne a karamar hukumar Mubi-South da Mubi ta Arewa.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje ya fitar a ranar Litinin, ya ce an kama wadanda ake zargin ne biyo bayan korafin da aka samu daga mahaifin wanda abin ya shafa a ranar Alhamis da ta gabata, 19 ga watan Oktoba.

