Kungiyar Hamas ta Falasdinu ta fitar da sanarwa a yau Talata cewa ta harba rokoki a Tel Aviv da Beersheba dake tsakiya da kudancin Isra’ila a matsayin martani ga “kisan gilla” da sojoji ke yiwa fararen hula a zirin Gaza.
A cikin jawabai daban-daban, reshen kungiyar Qassam Brigades masu kula da makamai sun ce sun harba makaman roka ne “a matsayin martani ga kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa” a Gaza.
Sojojin Isra’ila, a nasu bangaren, sun ce an yi ta harba makaman roka a fadin garuruwan da ke tsakiyar kasar da kuma kudancin Isra’ila, amma ba su bayar da karin bayanin ɓarnar da rokokin ya yi masu ba.
Rikicin Gaza da Isra’ila ya faro ne tun 7 ga watan Octoba bayan da Hamas ta kaddamar da wani harin ba-zata kan Isra’ila wacce ta daɗe tana zaluntarsu, a inda Isra’ila ta ƙaddamar da martanin hare-hare kan zirin Gaza ta hanyar harba makaman roka da kuma kutsawa da sojoji ta kasa da ruwa da sararin samaniya,
Isra’ila ta dade tana cin zarafi da matsugunawa Falasdinawa shekara da shekaru,
Kusan mutane 7,200 ne aka kashe a rikicin da ya barke tsakanin Isra’ila da Hamas da suka hada da Falasdinawa akalla 5,791 da kuma Isra’ilawa 1,400.
Daga Wakiliya


