354
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta ce ta kama wasu mutane shida da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, wadanda suka bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 5 kan wani yaro dan shekara tara da aka sace a karamar hukumar Mubi ta Kudu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan SP Suleiman Nguroje, wanda ya bayyana hakan a Yola ranar Litinin, ya ce wadanda ake zargin sun yi garkuwa da Mustapha Ibrahim, a ranar 18 ga watan Oktoba da misalin karfe 6:30 na yamma.
An kama wadanda ake zargin ne bayan mahaifin mamacin ya kai kara a ofishin ‘yan sanda a ranar 19 ga watan Oktoba.


