Home Labarai Liverpool za ta ɗauki Jamal Musiala, Al-Ettifaq na son Lingard.

Liverpool za ta ɗauki Jamal Musiala, Al-Ettifaq na son Lingard.

by Muhsin Tasiu Yau

Ɗan wasan Everton da Ingila Dominic Calvert-Lewin mai shekara 26, ya shirya duba tayin da aka yi masa zuwa ƙungiyar Al-Ettifaq ta Saudiyya da Steven Gerrard ke jagoranta. (Sun)

Atletico Madrid na son ɗan wasan Argentina mai shekara 25 Nahuel Molina ya sanya hannu a sabuwar kwantaragi a ƙungiyar, yayin da manyan ƙungiyoyi ke nuna sha’awarsu kan ɗan wasan.(Fichajes – in Spanish)

Manchester City za ta bar ɗan wasan tsakiya na Ingila Kelvin Phillips mai shekara 27 ya bar ƙungiyar a watan Janairu mai zuwa. (Star)

Ƙungiyar Etihad ta Saudiyya ta ƙagu wajen ganin ta ɗauko ɗan wasan West Ham Lucas Paqueta. (Teamtalk)

Napoli na son tattaunawa da tsohon kocin Brighton da Chelsea Graham Potter domin zama sabon kocin ƙungiyar, sai dai Potter na ciki ƙila wa ƙala game da Manchester United idan Erik ten Hag zai bar ƙungiyar. (Sun)

Bayern Munich na bibiyar dan bayan Chelsea Trevoh Chalobah mai shekara 24, duk da cewa ɗan wasan yana cikin shirin kocin ƙungiyar Mauricio Pochettino.(Mirror)

Newcastle United na shirin ƙaddamar da buƙatar ɗaukar ɗan wasan Real Betis Juan Miranda mai shekara 23 domin ya dawo gasar Premeir a watan Janairu. (Fichajes – in Spanish)

Crystal Palace za ta karɓi tayin fan miliyan 60 daga Manchester United kan ɗan wasan bayan Ingila Marc Guehi. (Teamtalk)

Ana hasashen Liverpool za ta ɗauki ɗan wasan Bayern Munich dan Jamus Jamal Musiala mai shekara 20. (Football Insider)

Aston Villa na nuna muradinsu kan ɗan wasan PSG Carlos Soler mai shekara 26 a lokacin musayar ‘yan wasa a watan Janairu. (Le Parisien, via Birmingham Mail)

Al-Ettifaq ta Saudiyya ta nuna ƙaunarta da tsohon ɗan wasan Manchester United da Ingila Jesse Lingard a watan Janairu.(Goal)

Related Posts

Leave a Comment