278
Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari a rukunin gidajen Hukumar Kwastam da ke garin Geidam cikin Ƙaramar Hukumar Geidam, Jihar Yobe, inda suka kashe wani jami’in hukumar, Usman Gombe.
Majiyarmu ta kalato cewar maharan sun yi dirar mikiya a kusa da hanyar Maine Soroa da motocinsu da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Asabar sannan suka shiga harbi da bindiga.
A cewar majiyar, “Sun kai harin ne bayan da suka tabbatar da jami’an sun dawo gida daga wurin aiki. Jin yadda maharan ke ta ruwan alburusai ya sa jami’an neman mafaka, yayin da wasunsu suka tsallaka katanga.

