320
Shahararren jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Sadiq Sani Sadiq ya karyata rade-radin cewa shi dan daba ne a baya.
Da yake amsa tambayoyi a shirin “Gabon’s Room Talk Show‘ wanda jaruma Hadiza Aliyu Gabon ke gabatarwa a Youtube, jarumin ya ce shi mafaruci ne a lokacin da yake tasowa.
Ya ce shakka babu ya dan taba rashin ji da yake tasowa domin har ya yi sana’ar siyar da mai na bunburutu.

