Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, ya ce, ba zai binciki gwamnatin tsohon gwamnan jihar da ya gada, Alhaji Aminu Masari, ba, saboda shi ma yana cikin gwamnati tasa.
Malam Raɗɗa ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC ranar Alhamis.
Ya ce: “Babu wani shiri na bincikar wanda ya gabace ni. Kuma ina da dalilai guda biyu na faɗar haka.
“Na farko ina cikin waɗanda suka kafa gwamnatin Aminu Bello Masari. Don haka ba ku tsammanin zan binciki gwamnati, wacce nake cikinta.
“Kuma ko da ma wanda ya gada na baya daga jam’iyyar adawa, ba zan yi bincike a kansa ba saboda yana cikin ƙa’idata.
“Na kuma gane cewa yawancin binciken da aka gudanar a baya bai haifar da wani abu mai ma’ana ba.
“Har yanzu ban ga kyakkyawan sakamako na duk wani binciken da aka yi a baya ba. Yana ƙara zafi ne kawai a siyasance kuma yana lalata dangantaka mai kyau,” in ji shi.
A cewarsa, gwamnatinsa ta ƙuduri aniyar farfaɗo da makarantun gwamnati, da inganta harkokin tsaro ta hanyar hukumar kula da al’umma ta jihar Katsina, da kuma inganta ayyukan gwamnati.
Gwamnan ya kuma ce sauran gwamnonin yankin Arewa maso Yamma na ƙoƙarin ganin sun yi amfani da tsarin mulkin sa don kafa nasu kayan tsaro.
Da yake magana kan naɗin ministocin da Shugaba Bola Tinubu ya yi, Raɗɗa ya ce an buqaci gwamnonin su miqa sunayen uku daga jihohinsu.
“Ka sani, gwamnoni ba sa naɗa ministoci. Amma Shugaban Ƙasa ya buƙaci mu (gwamnoni) mu miƙa sunayen uku da zai zaɓa daga cikinsu.
“Kuma na miƙa sunayen Mai Girma Tsohon Gwamnan Jihar, Aminu Bello Masari, Hajiya Hannatu Musawa, da Arc. Ahmad Ɗangiwa,” Raɗɗa ya ƙara.

