Home Labarai Gombe a shekara 27: Tarihi ba zai manta da shugabannin jihar ba – Zannan Gombe

Gombe a shekara 27: Tarihi ba zai manta da shugabannin jihar ba – Zannan Gombe

by Muhsin Tasiu Yau

Daga MOHAMMED ALI a Gombe

Maigirma Zannan Gombe, Alhaji Baba Gana Goni, ya yi imani da cewa, duk shugabannin da suka mulki Jihar Gombe tun da ta samu ‘yancin kanta daga Jihar Bauchi ranar ɗaya ga watan Oktoba, 1996, wato shekara 27 kenan, mutane ne masu kishi da kuma hangen nesa.

Zannan ya yi wannan iƙirarin ne yayin tattaunawa da manema labarai a ofishinsa a garin Gombe cikin makon jiya, a kan cikan shekara 27 da jihar ta yi, inda ya yi nuni da cewa, ci gaban da jihar ta samu cikin wannan tafiya (shekara 27), abin alfahari ne ga waɗanda suka mulki jihar tun daga kafuwanta har zuwa yau.

A cewar shi: “Alhamdulillahi, mu da dubban al’ummar wannan jiha tamu, babu abin da za mu ce illa son-barka ga waɗanda suka mulki Gombe tun kafuwarta a 1996 domin sun shimfiɗa ayyukan ci gaban ta, ta fannonin rayuwa iri-iri, saboda kishin su da hangen nesa wanda tarihi ba zai taɓa mantawa da su ba.”

A nan, Zannan Gombe sai ya auna sikeli a matsayin gwajin irin salon mulkin shugabannin, wato gwamnonin da suka jagoranci jihar tun fara mulkin dimukraɗiyya a Nijeriya a 1999, sai ya yi hukunci da cewa, “a gaskiya, gwamnan dake kan gado a yau, Maigirma Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ɗara sauran takwarorinsa na baya nesa ba kusa ba wajen ci gaban jihar ta shimfiɗa ababen more rayuwa ga al’ummarta a ko’ina a faɗin jihar ba a cikin Birnin Gombe kawai ba,” inji shi.

Sai ya jinjina wa gwamnan yadda ya ɗora ayyukan ci gaba a kan na waɗanda ya gada, har ma a ganin sa, ya yi musu fintikau musamman ganin yadda jihar a cewar shi, “ta zama wata karamar Dubai tun kafin ma ya shekara biyar da zama gwamna duba da irin tallafi ga ‘yan kasuwa da masu ƙananan masana’antu da kuma muhimmin wurin kafa masana’antu na Muhammadu Buhari Industrial Park da hanyoyi da lantarki ta ko’ina da sauransu da ya kawo wa kihar.

“Don haka, Inuwa Yahaya ya cancanci yabo, kuma a yi ta yi mishi addu’a sabooda maganar gaskiya, Gombe ta samu ƙarin ci gaba matuƙa a ƙarƙashin shi.”

Da yake martani game da gunagunin da mutane suke yi na cewa yawancin ayyukan duk an fi yin su ne a ƙwaryar birnin, amma ba su kai wa ga unguwanni, sai ya ce, “ka san al’umma na da yawa, amma duk an yi kasafi da su wanda kwanan nan za a fara kaiwa ga lunguna da anguwannin garin Gombe tunda aiki ya kai ga duk ƙananan hukumomin jihar.”

Daga ƙarshe Zanna Goni sai ya jinjina wa Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar (III) a kan haxɗin kan da ya kawo tsakanin al’ummar jihar, baya ga irin ɗimbin taimakawa jama’a da yake yi musamman ga marasa galihu, yana fatan Allah Ya ƙara mishi martaba.da daraja da kuma lafiya.

Related Posts

Leave a Comment