Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu a ƙwarya-ƙwaryar kasafin kuɗin shekarar 2023 wanda ya kai Naira biliyan hamsin da takwas, da miliyan ɗari da casa’in da daya, da dubu dari biyar da talatin da biyar, da naira goma sha takwas da kobo goma sha biyu (N58, 191, 535, 018.12), inda ya zama doka.
Yayin da yake sanya hannu a kasafin kuɗin, Engr. Abba Kabir Yusuf ya tabbatar wa al’ummar jihar Kano cewa gwamnatinsa za ta bi ƙa’idojin amfani da kasafin kuɗi domin kuɗaɗen da aka ware za a yi amfani da su bisa hanyar da ta dace.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yaɗa labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya aiko wa Blueprint Manhaja,
“Wannan ƙarin kasafin kuɗin an yi shi ne domin samar da ababen more rayuwa da kasafin kuɗin shekarar 2023 bai kula da su ba, don biyan buƙatun al’ummar jihar Kano.” a cewar Gwamnan,
Engr. Abba Kabir Yusuf ya yaba da ƙoƙarin kwamishina, tsare-tsare da kasafin kuɗi bisa yadda suka gaggauta aiwatar da aikin haɗa daftarin kasafin kuɗin har aka miƙa shi ga majalisar jiha.
Tun da farko a jawabinsa, kakakin Majalisar dokokin jihar Kano, dama Hon. Jibrin Ismail Falgore wanda ya jagoranci shugabannin majalisar da kuma yan kwamitin kasafi na majalisar ya gabatar da kundin kasafin da majalisar ta amince da shi ga gwamnan domin Sanya masa hannu don ya zama doka a gidan gwamnatin jihar Kano
Sannan gwamnan ya buƙaci cigaba da samun goyon baya da kyakkyawar alaƙa tsakanin ɓangaren zartarwa da na majalisar dokoki a jihar Kano.

