Home Labarai Mu biyar aka ce za a tsige a majalisar Dattawa saboda ba mu yi Akpabio ba – Sanata Agbo.

Mu biyar aka ce za a tsige a majalisar Dattawa saboda ba mu yi Akpabio ba – Sanata Agbo.

by Muhsin Tasiu Yau

Tsigaggen sanatan Adamawa Elisha Abbo ya bayyana wa manema labarai ranar Litinin cewa kotun ɗaukaka ƙara ta tsige shi ne saboda bai goyi bayan zaman sanata Godwill Akpabio shugaban majalisa ba.

Abbo ya ce ba shi kaɗai bane kotu za ta tsige, akwai wasu mutum huɗu baya ga shi da suma za a tsige su a Kotu saboda ba su goyi bayan Akpabio ba lokacin da yake neman kujerar shugaban majalisar dattawa.

Abbo ya ce ciki har da Sanata Orji Kalu.

Kotun ɗaukaka kara ranar Litinin ta tsige sanata Abbo da ke wakiltar Adamawa ta Arewa a majalisar Dattawa.

Kotun ta ce bisa ga ƙarar da abokin takarar Abbo na PDP Amos Yohanna ya shigar a kotun ɗaukaka ƙarar, shine ya yi nasara a zaɓen.

Kotun daukaka kara, bayan sauraron duka ɓangarorin, ta amince cewa bisa ga sashi na 137 na dokar zabe ta 2022, sakamakon da aka gabatar ya nuna karara cewa ba a bi dokar zabe.

Daga nan ne kotun ta cire kuri’un da aka yi wa Abbo aringizon su sai aka gano cewa Yohanna da PDP ne suka lashe zaben da mafi rinjayen halastattun kuri’un da aka kaɗa.

Sannan kuma kotu ta umarci hukunar zaɓe ta janye satifiket ɗin nasarar zaɓe da ta ba Abbo ta mika wa Yonana na PDP.

A karshe Abbo ya ce ” Zan yi hakuri, tunda ba bu inda zan je gaba. Shekara biyu ce kacal, zan dawo kuma zan yi nasara.

Idan ba a manta ba tun ya na ɗanyen ɗan majalisa, aka fara kai ruwa rana da Sanata Abbo, inda aka same shi da laifin gaggaura wa wata yarinya mai saida kayan batsa a Abuja mari.

 

Related Posts

Leave a Comment