Home Labarai Tubabben Dan Daba mai suna “Chile Mai Doki” ya zama “Constabulary” a kano.

Tubabben Dan Daba mai suna “Chile Mai Doki” ya zama “Constabulary” a kano.

by Muhsin Tasiu Yau

Tubabben ɗan daba mai suna Chile Mai Doki ya kammala daukar horo na zama dan sandan sarauniya, wato Constabulary a kano

Wato daga aikata laifuka ya koma mai kama masu aikata laifuka. Muna Godiya da Addu’o’inku.

Alfijir Labarai ta rawaito cewar idan zaku iya tunawa Chile Mai Doki na ɗaya daga cikin ‘yan daban da runudnar ‘yan sanda a Kano ta ce ta na nema, har ma ta sanya tukuicin 100k ga wanda ya kawo daya daga cikin su, ya tuba, ya kai kan sa ga rundunar.

Matashi Chile Mai Doki, na daga cikin wadanda Rununar ‘Yan Sanda ke nema idanu rufe, bayan gano yadda suke hana zaman lapiya da tayar da tarzoma a Kano.

Sai dai bayan billar wani bayani, wanda ke nuni da neman mutanen idanu rufe, ya sa Chille ya kai kan sa, kuma ya ce ya tuba, har ma da alqawalin zai ba da gudunmawa wajen zaman lapia a Kano.

Chille ya bayyana cewa, ya koma rayuwa a maqabarta musamman bangaren kwana, saboda gujewa kamun ‘Yan Sanda, kafin daga bisani ya yanke shawarar mika kan shi.

Zuwa yanzu dai, Chille ya shiga kundin Tubabbun ‘Yan Daba a Jihar Kano.

 

Related Posts

Leave a Comment