Gwamnan Jihar Jigawa, Mal. Umar A. Namadi da takwaransa na Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, haɗa da tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido da tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso na daga cikin tarin jama’ar da suka halarci jana’izar marigayi Sardaunan Dutse, Sheikh Dr. Bello Maitama Yusuf.
A ranar Juma’ar da ta gabata Allah Ya yi wa Bello Maitama rasuwa a gidansa da ke Tarauni, Kano, yana da shekara 76.
A halin rayuwarsa, Bello Maitama ya taɓa riƙe muƙamin Ministan Cinikayya da wasannin motsa jiki a Jamhuriyya ta ɗaya ƙarƙashin Gwamnatin marigayi Ahaji Shehu Shagari.
Haka nan, ya yi sanatan Jigawa ta tsakiya ya kuma bada gudummawa a ɓangarori da dama.
Sauran da suka halarci jana’izar har da mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam da na Jigawa, Aminu Usman da Alhaji Bashir Ɗalhatu, (Wazirin Dutse) da Alh. Basiru Nuhu Sanusi (Galadiman Dutse) da Mai Shari’a Tijjani Abubakar da sauransu masu yawan gaske.
An gabatar da sallar jana’izar ne a ƙofar fadar Sarkin Kano ban kammala sallar Juma’a.


