Home Labarai Shugaba Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar EFCC

Shugaba Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar EFCC

by Muhsin Tasiu Yau

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta Nijeriya ta bayyana cewa, ta ƙwato jimillar Naira 27,184,357,524.52 da dala 19,084,419.33 a wasu shari’o’i uku na karkatar da kuɗaɗe. Daga cikin wannan adadin da aka ƙwato, an gano Naira biliyan 12.7 ne daga hannun mutum ɗaya.

Hukumar ta EFCC na binciken tsaffin gwamnoni da tsofaffin Ministoci da wasu jami’an gwamnati a faɗin ƙasar nan a ƙoƙarin da ta ke yi na yaƙi da cin hanci da rashawa.

Muƙaddashin shugaban hukumar ta EFCC Abdukarim Chukkol ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai da wasu ’yan jarida a Legas.

Chukkol, wanda kakakin hukumar, Dele Oyewale, ya wakilta, ya bayyana cewa, hukumar ta himmatu wajen kwato wasu haramtattun kuɗaɗe, kuma nan ba da daɗewa ba za ta bayyana cikakken bayanan binciken da ta gudanar kan ayyukan wasu shugabannin da suka gabata.

Hukumar ta EFCC ta kuma ɗauki matakin shawo kan badaƙalar sayen manyan kadarori da ake alaƙantawa da jami’an ma’aikatar wutar lantarki ta tarayya da na ma’aikatar gona.

An karkatar da kuɗaɗen da aka tanada don ayyuka irin su Mambilla da Zungeru Power ta hannun wasu ma’aikatan ofishin canji. Sakamakon haka, an kwace wasu kadarori da dama a babban birnin tarayya, Legas, da jihohin Kuros Ribas.

Chukkol ya jaddada cewa binciken da ake yi ya haɗa da zargin da ake yi wa wasu tsaffin gwamnoni, waɗanda a halin yanzu ke riƙe da muƙaman ministoci ko kuma ’yan majalisar dokokin ƙasar.

Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa da zarar an kammala waɗannan bincike, mutanen da ke da hannu za su fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada, ba tare da la’akari da matsayinsu na hukuma ba.

Bugu da ƙari, Chukkol ya bayyana yadda hukumar ta ƙara mayar da hankali kan hana aikata laifukan da suka shafi kuɗi da tattalin arziki, domin hanya ce mai tsadar gaske idan aka kwatanta da bincike da kuma gurfanar da su a gaban kotu.

EFCC na da niyyar inganta aikinta ta hanyar yaƙin wayar da kan jama’a da sauran tsare-tsare.

Related Posts

Leave a Comment