Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta ce, hukumar na da tsawon makonni uku domin tattaunawa da masu yi wa alhazai hidima a ƙasar Saudiyya, inda ta buƙaci maniyyatan Nijeriya da su fara ajiye Naira miliyan 4.5 kafin lokacin aikin hajjin a matsayin adashin gata.
Mataimakiyar Daraktar Hulɗa da Jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda Usara a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, ta ce Masarautar ta sanya ranar 4 ga watan Nuwamba, 2023 don kammala taron share fage da masu ba da hidima, inda ta ce, kafin nan ya kamata hukumar ta yi kiyasin aniyar maniyyata aikin Hajji.
anda ta ce, tun farko shirye-shiryen aikin hajjin 2024 ne ya jagoranci hukumar da kuma ƙungiyar zartaswar sakatarorin jin daɗin alhazai ta jiha suka sanar da Naira miliyan 4.5 a matsayin ajiya na kuɗin aikin hajji.
“Hikimar da ke tattare da wannan mafi ƙarancin ajiya ta ta’allaƙa ne akan dalilai uku. Na farko, shi ne jihohi da hukumar su yi kiyasin adadin maniyyata nawa ne za su cancanci a ƙidaya su a matsayin mahajjata aƙalla nan da 4 ga Nuwamba, 2023, lokacin da Saudiyya ta sanya hukumar ta kammala taron share fage da masu ba da hidima.
Ta ƙara da cewa, an amince da wannan adadin ne domin baiwa mahajjata damar biyan sauran kuɗaɗen cikin sauki idan aka bayyana kuɗin tafiya na ƙarshe.


