
GWAMNATIN SHUGABA TINUBU TA JANYE DOKAR SHEKARAR TA 2015 DA TA HANA SHIGO DA WASU KAYAYYAKI GUDA 43 MUSAMMAN KAYAN ABINCI ZUWA CIKIN NIGERIA
Sanarwar tazo ta hannun babban Bankin ƙasar CBN cewa daga yanzu Gwamnati ta amince a shigo da kayayyaki 43 da Gwamnatin baya ta hana shigo dasu, kuma an amince CBN ta bayar da Canji Dala ga waɗanda zasu shigo da irin kayayyakin Nigeria.
Kuma wannan zai taimaka ƙwarai da gaske wajen sauƙo da kayayyakin da sukayi tsada a faɗin ƙasar idan anbi yadda aka tsara
Lallai haƙiƙa wannan janye Dokar cigaba ne sosai a wannan ƙasar musamman mallam talaka, domin wannan Dokar tana daga cikin abubuwan da suka bayar da matsala sosai wa ƙasar da Gwamnatin shugaba Buhari data kawo Dokar, da ace anyi nasarar bin tsarin da Gwamnatin Buharin tazo dashi koda da kaso 60 cikin 100 ne da wahalar Bata tsananta a kasar ba.
Kuma shugaba Tinubu yayi haka ne domin talakawa su sarara, domin shugaba Tinubu bashi sa wani mafarki wanda ya wuce talaka ya samu sauƙi a ƙasar nan.
Waɗannan Sune Abubuwa 43 da aka janye dokar shigo da su ƙasarmu.
1. Shinkafa
2. Siminti
3. Magarin – (Botar Biredi)
4. Man Kwantirola
5. Man gyaɗa
6. Man alayyahu da kayan lambu
7. Nama da naman da aka sarrafa
8. Kayan lambu da kayan lambun da aka sarrafa
9. Kaji da kayan kiwon kaji da aka sarrafa
10. Kifin gwangwani wata Geisha ko sardine
11. Shimfiɗaɗɗen ƙarfe watau faleti
12. Dogon kwanon rufi
13. Gajeren kwanon rufi
14. Wilbaro
15. Kwanon sarki
16. Akwatunan ƙarfe da kwantenoni
17. Fadi ka mutu
18. Badujala
19. Fayif na ƙarfe
20. Wayar rodi – lalatacce da wanda bai lalace ba
21. Rodi sitil
22. Rodi Bagobiri
23. Wayar raga
24. Ƙusa
25. Wayar tsaro da turakuna
26. Fatikus bodi
27. Faibod da faleti
28. Filawud
29. Ƙofofin katako
30. Tsinken sakace
31. Gilashi da kayan da aka yi da gilashi
32. Kayan kicin
33. Kayan hada tebur
34. Tayil
35. Silindar gas
36. Sakakkun yadudduka
37. Tufafi
38. Kayayyakin da aka yi da roba
39. Kwayoyin roba watau Polypropylene
40. Ledar rufe alewa da jaka
41. Sabulu da kayan kwalliya
42. Tumatur/tumaturin gwangwani
43. Hannun jarin Yurobond/Bond na kuɗin ƙasashen waje/ko kuma hannun jarin ƙasar waje
Tinubu ya ƙara fito da martabar talakawa a idanuwan duniya.
Renewed Hope is on track!
Endure…
♾️🇳🇬

