Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ministan Harkokin Cikin Gida na Nijeriya, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce ana ci gaba da sauye-sauye domin sauƙaƙa aikin fasfo tare da yiyuwar ‘yan Nijeriya su fara gabatar da aikace-aikacen samum fasfo ɗin ta yanar gizo tun daga watan Disamba.
Da yake magana a gidan talabijin na Channels Television a shirin ‘Siyasa A Yau’ a Laraba, Tunji-Ojo ya bayyana cewa, ɗaya daga cikin sauye-sauyen da ma’aikatar ke aiwatarwa a fannin sarrafa fasfo shi ne kawo ƙarshen tsarin neman fasfo cikin wahala.
“Ni da kaina na faɗi haka ga masu samar da ayyukan; Na faɗa yau, na fadi haka jiya, kuma a koyaushe ina gaya musu, ‘Kuna buƙatar ku sauƙaƙa wa mutane. A matsayinmu na gwamnati masu son hidimta wa al’umma, ya kamata mu nemi hanyar da za mu samar musu da sauƙi,” inji shi.
“Daga cikin gyare-gyaren da muke yi a yanzu, daga watan Disamba, shi ne, ko da za ku yi rajistar fasfo ɗin ku, sai ku cika fom ɗin ku ta yanar gizo, ku biya ta yanar gizo, da komai.”
Ministan yana mayar da martani ne ga wata tambaya kan mafi kyawun tsarin ƙasa da ƙasa na neman fasfo da karɓan fasfo, idan aka kwatanta da abin da ake samu a Nijeriya, da kuma hanyoyin da za a rage wa ‘yan Nijeriya wahalhalu a harkar neman takardun.
Idan aka kwatanta da tsarin neman fasfo a ƙasashen waje, ministan ta bayyana cewa, na’urar ɗaukar hoto ne kawai ake buƙatar a yi a ofishi, inda ta bayyana cewa za a iya miƙa dukkan bayanan da suka dace ta manhajar Hukumar Shige da Fice (NIS).
“Ba kwa buƙatar zuwa ofishin fasfo don a ɗauki hotonku. Mutane suna neman bizar Amurka, mutane suna neman bizar Birtaniya, kuma mutane suna neman biza a duk faɗin duniya. Za a loda fasfo ɗin ku tare da ƙayyadaddun da ake buƙata kamar yadda NIS ta umarta a kan dandamalin ta.
“Kuna loda fasfo ɗin ku a kan layi, kuna loda takaddun ku akan layi, don haka lokacin da kuka je ofishin shige da fice, zai ɗauki kamar minti biyar kawai don karve ku; shi ke nan,” inji shi.
‘Yan Nijeriya na iya neman fasfo ta yanar gizo daga watan Disamba
344
previous post

